Ƙungiyoyin agaji sun buƙaci a gaggauta tsagaita wuta a Gaza

Asalin hoton, Reuters
Ƙungiyoyi agaji fiye da ɗari sun yi gargaɗin yaɗuwar mummunar yunwa a Gaza, inda mutane fiye da miliyan biyu ba su iya samun abinci.
Ƙungiyoyin sun ce a halin da ake ciki yanzu hatta ma'aikatansu su na fama da ƙarancin abinci a Gaza.
Ƙungiyoyin agajin da suka fitar da rahoton mawuyacin halin da mutane ke ciki a Gaza sun haɗa da ƙungiyar likitoci ta ƙasa da ƙasa, da Save the Children da kuma Oxfam.
Sun ce ma'aikatansu ba su da wani zaɓi illa su shiga layin neman agajin abinci tare da al'umma Gaza, wani abu da ke sanya su shiga yanayin da za a iya harbe su, saboda ƙoƙarin nema wa iyalansu abinci.
Sun buƙaci a samar da tsarin rabon kayan agaji a Gaza ta hannun hukumomin Majalisar Dinkin Duniya.
Isra'ila ta amsa cewa an samu raguwa da gagarumin rinjaye kan yawan kayan agaji da Falasɗinawa ke samu, amma ta musanta cewa akwai yunwa a yankin.
Dr Graeme Groom babban likitan ƙashi ne a asibitin London, wanda kuma ya yi aiki a Gaza a watan jiya.
Ya ce: ''A kullum abokan aiki na aiko mani saƙo domin sanar da ni cewa babu abinci. Kwanaki biyu da suka wuce, wani babban jami'in mu ya shaida mani cewa babu abinci, kuma ko kaɗan babu, sai ya ce ai babu komai, asali ma cikin matsananciyar yunwa suke.''
Wani rahoton da ma'aikatar lafiya ta Hamas ta fitar ya ce mutane fiye da 30 suka mutu saboda tsananain yunwa a kanaki uku, lamarin da Isra'ila ta ce farfaganda ce kawai.
Ƙungiyoyin sun buƙaci a gagauta kawo ƙarshen yaƙin domin samun damar shigar da wadataccen abinci ga al'ummar Gaza.














