Messi zai ci gaba da zama a Inter Miami, Al-Nassr na son Casemiro

Lokacin karatu: Minti 2

Al-Nassr na zawarcin dan wasan tsakiyar Manchester United Casemiro, yayin da kwantaragin dan wasan mai shekara 33 ke shirin karewa a Old Trafford a bazara. (Mundo Deportivo)

Manchester United na fafatawa da Atletico Madrid da Barcelona wajen siyan dan wasan gaban Serbia Dusan Vlahovic, mai shekara 25, wanda kwantiraginsa a Juventus zai kare a bazara mai zuwa. (La Gazzetta dello Sport)

Real Madrid na zawarcin dan wasan bayan Tottenham Hotspur Micky van de Ven, mai shekara 24, inda kulob din na arewacin Landan ya kimanta dan kasar Holland din a kan fan miliyan 70. (Fichajes)

Inter Miami tana gab da kammala sabuwar yarjejeniya ta shekaru masu yawa da dan wasan gaban Argentina Lionel Messi, mai shekaru 38, wanda ya fara sanya hannu a kulob din na MLS a 2023. (ESPN)

Dan wasan gefe na Liverpool da Italiya Federico Chiesa, mai shekara 27, zai iya barin Anfield a kasuwar musayar 'yan wasa ta Janairu don komawa kasarsa ta haihuwa. (Teamtalk)

Arne Slot yana sha'awar kawo dan wasan baya na Ajax Youri Baas, mai shekara 22, zuwa Anfield, kodayake dan kasar Holland din yana kwantiragi da zai kai har zuwa 2028. (Fichajes)

Tottenham na daga cikin kungiyoyin Premier da dama da ke son dauko dan wasan tsakiya na Atletico Madrid da Ingila Conor Gallagher, mai shekara 25. (TBR Football)

AC Milan na zawarcin dan wasan bayan Udinese dan kasar Denmark Thomas Kristensen, mai shekara 23, wanda Aston Villa ta nema a kasuwar musayar 'yan wasa ta karshe. (La Gazzetta dello Sport)

Manchester United za ta kyale dan wasan gaban Netherlands Joshua Zirkzee, mai shekara 24, inda ta maida hankali kan dan wasan Slovenia Benjamin Sesko, mai shekara 22. (Teamtalk)