Barca na da kwarin gwiwa kan Haaland, Liverpool da City na hamayya kan Guehi

Lokacin karatu: Minti 2

Shugaban kungiyar Barcelona Joan Laporta ya kara kaimi wajan daukar dan wasa mai kai hari na Manchester City Erling Haaland kuma yana da kwarin gwiwar cewa dan wasan mai shekara 25 dan kasar Norway zai koma taka leda a kungiyar ta La Liga nan gaba.(El Nacional - in Spanish), external

Manchester City na shirin yin hamayya da Liverpool don siyan dan wasan bayan Ingila da Crystal Palace Marc Guehi mai shekara 25 a bazara mai zuwa, lokacin da kwantiraginsa zai kare.(Mirror), external

Brentford ta nuna sha'awar daukar dan wasan bayan Borussia Dortmund Almugera Kabarmai shekara 19 .(Bild - in German, subscription required), external

Everton za ta yi watsi da duk wani tayin da za a yi wa dan wasan Ingila Jarrad Branthwaite a shekarar 2026 inda dan wasan mai shekara 23 zai kasance a cikin kungiyar na tsawon lokaci (Talksport), external

Wakilan Arsenal da Chelsea da Manchester United, da Barcelona da kuma Real Madrid na bibiyar dan wasan tsakiya Ajax dan kasar Belguim Jorthy Mokio mai shekara 17. (Caughtoffside), external

Dan wasan Crystal Palace da Ingila Adam Wharton, mai shekara 21, yana son komawa Liverpool duk da cewa Real Madrid da Chelsea da Manchester United na son daukarsa.(Fichajes - in Spanish), external

Dan takarar shugaban kungiyar Benfica, Cristovao Carvalho ya ce zai kori kocin kungiyar Bruno Lage tare da kokarin shawo kan tsohon kocin Liverpool Jurgen Klopp ya maye gurbinsa idan aka zabe shi a wata mai zuwa. (Sportbild - in German), external

Wani dan takarar shugaban kungiyar ta Benfica, Joao Noronha Lopes, yana son ya dawo da kocin Manchester United Ruben Amorim kungiyar ta Lisbon, inda ya shafe shekaru tara yana taka leda.(Times - subscription required), external