Bayern Munich ta sanya farashin fam miliyan 100 kan Olise, Chelsea na zawarcin Guehi

Lokacin karatu: Minti 2

Bayern Munich na son a biyata fam miliyan 100 a kan dan wasan tsakiya na Faransa Micheal Olise mai shekara 23 wanda ya ja hankalin Liverpool da wasu manyan kungiyoyin turai (Football Insider), external

Chelsea na son daukar dan wasan Crystal Palace da kuma Ingila Marc Guehi, mai shekara 25, da golan AC Milan dan Faransa Mike Maignan,mai shekara 30, a bazarar bana. (TBR Football), external

Da wuya Manchester City ta sabunta kwantiragin dan wasan tsakiyar Portugal Bernardo Silva , wanda zai share fagen barin dan wasan mai shekara 31 daga kungiyar a bazarar badi , inda Juventus da Benfica suka nuna sha'awarsu (AS - in Spanish), external

Liverpool da Arsenal da Manchester United na daga cikin kungiyoyin da ke zawarcin dan wasan tsakiyar Lille, dan kasar Faransa Ayyoub Bouaddi mai shekaru 17. (Teamtalk), external

Bayern Munich na son daukar dan wasan Athletic Bilbao dan kasar Sfaniya, Nico Williams mai shekara 23 a bazara mai zuwa. (Fichajes - in Spanish), external

Chelsea za ta fuskanci hamayya daga Bayern Munich a zawarcin dan wasan gaban Lyon dan kasar Belgium Malick Fofana mai shekaru 20. . (Caught Offside, via Christian Falk), external

Dan wasan bayan Liverpool dan kasar Faransa Ibrahima Konate, mai shekara 26, ya yanke shawarar kin sabunta kwantiraginsa a Anfield, kuma zai rattaba hannu a Real Madrid a bazara mai zuwa. (Fichajes - in Spanish), external

Manchester United ta ci gaba da zawarcin dan wasan Brighton dan kasar Kamaru Carlos Baleba bayan ta rasa dan wasan mai shekara 21 a bazarar bana.(Football Insider), external

Dan wasan Manchester United Sam Mather, mai shekara 21, zai nemi barin Old Trafford a watan Janairu, bayan wa'adin komawar sa Kayserispor ya zo karshe.(Manchester Evening News), external

Chelsea ta aike da 'wakilanta don kallon dan wasan Juventus dan kasar Turkiyya Kenan Yildiz mai shekaru 20.(Caught Offside), external