Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Saka zai ci gaba da zama daram a Arsenal, United da Liverpool na son Bouwman
Manchester United na neman dan wasan Nottingham Forest Elliot Anderson, Arsenal ta samu ci gaba wajen tsawaita kwantiragin Bukayo Saka da William Saliba, kuma matashin dan wasan baya na Ajax yana jan hankalin mutane sosai.
Manchester United na zawarcin dan wasan Nottingham Forest da Ingila Elliot Anderson, mai shekara 22 a watan Janairu. (Teamtalk)
Arsenal na shirin tsawaita kwantiragin dan wasan Ingila Bukayo Saka da dan wasan bayan Faransa William Saliba, yayin da kwantaragin 'yan wasan biyu, masu shekaru 24, zai kare a karshen kakar wasa ta 2026-27. (Teamtalk)
Mai tsaron ragar Kamaru Andre Onana, wanda ke daf da komawa Trabzonspor a matsayin aro, ya ki amincewa da tayin kungiyoyi da dama, ciki har da Monaco (The I paper)
Dan wasan bayan Manchester United da Netherlands Tyrell Malacia, mai shekara 26, zai iya zaman aro na tsawon kaka daya a kungiyar Eyupspor ta Turkiyya. (Sun)
Liverpool da Manchester United na daga cikin manyan kungiyoyin da ke zawarcin matashin dan wasan baya na Ajax Aaron Bouwman, mai shekara 18. (Teamtalk)
Dan wasan kasar Sipaniya kuma tsohon dan wasan baya na Manchester City Aymeric Laporte, mai shekara 31, yana jiran ya gano ko Fifa za ta amince da komawar shi zuwa Athletic Bilbao daga Al-Nassr bayan rashin yiwuwar hakan a kasuwar saye da sayar da 'yan wasa ta bazara. (AS Spanish)
Dan wasan tsakiya na Ingila Josh Brownhill, mai shekara 29, ya kammala gwajin lafiya a kungiyar Al-Shabab kuma yana shirin komawa kungiyar ta Saudiyya kyauta bayan ya bar Burnley a karshen kakar wasan data gabata. (Fabrizio Romano)
Dan wasan Brazil Casemiro, mai shekara 33, an danganta shi da komawa Saudiyya amma Manchester United za ta iya ci gaba da rike shi har sai kwantiraginsa ya kare a bazara mai zuwa (Cought Offside)
Inter Milan ta nuna sha'awarta a kan dan wasan Canada Jonathan David kafin dan wasan mai shekaru 25 ya koma Juventus a kyauta bayan ya bar Lille a bazara. (Gazzetta dello Sport)