Wace dama ta rage wa Najeriya kafin ta samu gurbi a Kofin Duniya?

    • Marubuci, Daga Umar Mikail
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 3

Har yanzu tawagar ƙwallon ƙafar Najeriya ta Super Eagles na da damar samun gurbi a gasar Kofin Duniya ta 2026, kodayake dai ba mai yawa ba ce kuma za ta dogara ne da sakamakon wasu wasanni.

Najeriya ta shiga cikin rashin tabbas ne bayan canjaras 1-1 da ta je ta buga da tawagar Bafana Bafana ta Afirka ta Kudu a yammacin Talata.

Sakamakon ya sa Afirka ta Kudu ta ci gaba da zama a mataki na 1 da maki 17 cikin wasa takwas a Rukunin C, yayin da Benin ke biye mata da maki 14.

Najeriya na mataki na 3 da maki 11, iri ɗaya da na Rwanda da ke mataki na 4. Lesotho na da maki 6 a mataki na 5, sai kuma Zimbabwe ta ƙarshe da maki 4.

Tawaga tara ko 10 ne za su wakilci nahiyar Afirka a gasar da ƙasashe 48 za su fafata, wadda ƙasashen Amurka da Mexico da Canada za su karɓi baƙunci.

Duk tawagar da ta ƙare a mataki na ɗaya daga kowane rukuni guda tara na nahiyar Afirka, ita ce za ta samu gurbi kai-tsaye. Daga baya sai a zaɓo huɗu mafiya ƙoƙari da suka ƙare a mataki na 2, inda za fitar da ɗaya daga cikinsu sannan ta kara da takwararta ta wata nahiyar.

Rabon da Najeriya ta samu gurbin Kofin Duniya tun a 2018 da aka yi a Rasha, inda ta gaza zuwa na 2022 a Qatar.

Me Najeriya ke buƙata kafin samun gurbin?

Jimilla Najeriya ta je gasar Kofin Duniya sau shida a tarihi - 1994, 1998, 2002, 2010, 2014, 2018.

A wasannin neman gurbin na gasar 2026, biyu kacal Najeriya ta ci cikin wasa takwas, ta yi canjaras biyar da rashin nasara ɗaya.

A lissafi, Najeriya za ta iya samun gurbi saboda wasa biyu-biyu suka rage wa tawagogin, inda take da damar samun ƙarin maki shida daga cikinsu idan ta doke Lesotho da Benin a watan Oktoba mai zuwa.

Ko Najeriya za ta iya doke Lesotho da Benin?

Yanzu abin tambayar shi ne ko za ta iya doke su ƙasashen Banin da Lesotho? Idan ta doke su, shin hakan zai sa ta samu gurbin?

Duk da cewa Najeriya ta fi ƙarfin Benin da Lesotho a fagen ƙwallom ƙafa, babu tabbas game da nasararta a kansu, saboda wasan farko da Najeriya ta buga da tawagogin biyu 1-1 suka tashi da kowaccensu.

Wajibi ne Najeriya ta ci wasannin biyu, abin da zai sa ta haɗa maki 17 kamar na Afirka ta Kudu, sannan kuma ta yi fatan a doke Afirka ta Kudun a wasa biyun da za ta buga da Zimbabwe da kuma Rwanda.

Ko da Najeriya ta yi nasara a wasa biyun kuma an cinye Afirka ta Kudu, dole ne sai Super Eagles ɗin ta ci ƙwallaye fiye da shida domin ta wuce Bafana Bafana a yawan ƙwallaye.

Yanzu haka Afirka ta Kudu na da yawan ƙwallaye +8, yayin da Najeriya ke da +2.

A gefe guda kuma, Rwanda ma na iya kawo wa ƙasashen biyu cikas idan har ta samu irin nasarar da Najeriya ke buƙata - amma ita tana buƙatar ƙwallaye aƙalla 9 domin ta kamo yawan na Afirka ta Kudu.