Lambar girmamawa da Tinubu ya ba shugabannin majalisa na tayar da ƙura

Asalin hoton, @PBATMediaCentre
Batun lambar girmamawa da Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ba shugabannin majalisa ya tayar da ƙura inda wasu ƴan majalisar suka ce an yi kuskure.
Wasu yan majalisar wakilai a zaman da suka yi ranar Laraba sun yi watsi da lambar girmamawa ta CFR da shugaba Tinubu ya ba kakakin majalisar wakilai Tajudeen Abbas.
Ƴan majalisar sun ce lambar girmamawar ta CFR ga shugaban majalisar wakilai kamar ragewa majalisar daraja ne.
Sun ce dukkanin majalisun tarayya biyu darajarsu ɗaya, kuma ba daidai ba ne ana danganta majalisar wakilai a matsayin ƙaramar majalisa.
Fadar shugaba Tinubu dai ba ta ce komi ba kawo yanzu game da ƙorafin ƴan majalisar wakilan.
A ranar Talata ne shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sanar da karrama shugabannin majalisar tarayya da lambar girmamawa ta ƙasa a cikin jawabinsa na bikin cika shekara 64 da samun ƴancin kan Najeriya.
A cikin jawabinsa Tinubu ya ba shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio da Alƙalin Alƙalai mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun lambar yabo ta girmamawa ta biyu mafi daraja ta GCON, yayin da kuma ya ba kakakin majalisar wakilai lambar yabo ta CFR. Shugaban ya kuma ba mataimakin kakakin majalisar wakilai Benjamin Kalu lambar yabo ta CON.
A wani ƙuduri da kusan ƴan majalisar wakilai 300 suka jagoranta, sun bayyana rashin amincewa matakin wanda suka kira tamkar mayar da majalisar wakilai saniyar ware ne.
Sun buƙaci shugaban ya gyara abin da suka kira “kuskure.”
Ƙorafin ƴan majalisar ya kuma mayar da hankali kan lambar girmamawa ta GCON da shugaba Tinu ya ba Alƙalin Alƙalan ƙasar inda suka ce an nuna ta fi kakakin majalisar wakilai daraja.
Sun ce kakakin majalisar wakilai shi ne na huɗu a tsarin matsayi na shugabanci a Najeriya, yayin da Alƙalin Alƙalai ke matsayi na biyar. Don haka sun nuna cewa "ofishin Kakakin majalisa ya fi na Alƙalin Alƙalai matsayi."
Ƴan majalisar dai sun ce ba wai suna korafin ba ne da yawun Tajudden Abba, amma suna yi ne don darajar ofishin kakakin majalisar wakilai.
Majalisar ta kuma kafa kwamiti ƙarƙashin jagorancin Julius Ihonvbere domin tuntuɓar bangaren zartarwa kan ƙorafinsu.
Me wannan ke nufi ?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Masana siyasa iirinsu Malam Kabiru Sufi malami a kwalejin ilimi da share fagen shiga jami’a da ke Kano na ganin wannan ba batu ba ne da ya kamata a ce ya tayar da ƙura a Najeriya.
Ya ce sun yi mamakin yadda fadar shugaban kasa ta ba batun lambar yabo muhimmanci musamman a jawabin shugaba Tinubu na bikin samun ƴancin kai "a daidai wannan lokaci da ba shi ba ne batun da ya damu ƴan Najeriya."
“Yakamata a ce an takaita jawabin shugaban domin ba batun lambar girmamawa ba ne ya damu ƴan Najeriya da suke son ji daga jawabin shugaban,” in ji Malam Sufi.
Game da koken da majalisar wakilai ke yi na fifita majalisar dattawa da Alkalin Alkalai, masanin ya ce kila fadar shugaban ƙasa ta yi la’akari ne da cewa majalisar dattawa tana kan gaba da majalisar wakilai.
Sannan ya ce idan aka kalli turakan gwamnati guda uku, akwai bukatar tabbatar da daidaito tsakaninsu domin kaucewa ƙorafin ganin fifita wani ɓangare domin kaucewa duk abin da zai kawo zargi.
“Idan ɓangaren shari’a yana samun fifiko daga ɓangaren zartarwa, ana iya ganin zai iya fifita ɓangaren zartarwa idan wani abu ya taso tare da nuna rashin adalci a tsakani idan har aka samu saɓani da majalisa.”
“Tayar da ƙurar ba wani abu ba ne illa kawai majalisar wakilai na ƙoƙarin tabbatar da girmanta domin tana ganin kamar an rage mata daraja, in ji Malam Sufi.
Ya ƙara da cewa wannan wata manuniya ce ga fadar shugaban ƙasa cewa akwai buƙatar nazari a duk lokacin da za a bayar da irin wannan lambar girmamawar domin kaucewa abin da daga baya za a dawo ana tayar da jijiyar wuya duk da cewa ba wani alfanu irin wannan lambobin girmamawar ke tattare da su.
Sai dai wasu za su yi tambayar shin shugabannin majalisar wakilai da suka gabata wace irin lambar girmama aka ba su?











