Me ya jawo ƙarancin kishin ƙasa tsakanin matasan Najeriya?

Masu bikin 'yancin kai a Abuja ranar Talata

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wasu masu goyon bayan gwamnatin Bola Tinubu ta jam'iyyar APC sun yi bikin Ranar 'Yanci a Abuja babban birnin ƙasar
    • Marubuci, Mukhtari Adamu Bawa
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Senior Broadcast Journalist
    • Aiko rahoto daga, .
  • Lokacin karatu: Minti 6

"Wa ya gaya ma ana mutuwa a kan Najeriya?" "Ba zan taɓa sadaukar da rayuwata a kan wata aba Najeriya ba - "a kan Najeriyar? Taf!"

Waɗannan ne ire-iren laffuzan da akan ji suna fitowa daga wasu matasan Najeriya da ke nuna tsantsar ƙarancin kishin ƙasa, musamman a shafukan sada zumunta cikin ƴan shekarun nan.

Kai ƙarewa da ƙarau ma, cikin ƴan watannin baya, an ga wasu matasa a Kano na ɗaga tutocin ƙasar Rasha, lokacin zanga-zangar nuna adawa da yunwa. Wasu da dama sun fassara hakan da ƙoƙarin fito da fushin da suke da shi a kan shugabanni, da ita kanta Najeriya.

Shin me yake faruwa, matasa ke fitowa fili suna yanke ƙauna ga ƙasarsu, mahaifarsu kuma tushensu?

Me ya yi zafi, har matasa ke dawowa daga rakiyar Najeriya?

Wani ɗan gwagwarmaya da wayar da kan matasan Afirka a Najeriya, Kwamared Abdulmajid Sa'ad ya ce lamarin abin tsoro ne, kuma idan hakan ta ci gaba, Najeriya ta kama hanyar rasa makomarta kenan.

"Ba kalmar da zan iya amfani da ita domin nuna muhimmancin kishi na matashi a kan ƙasarsa. Domin shi ne abin da ake cewa makomar ƙasa na hannun matashi.

Sai dai Dr. Kole Shettima, darakta a Gidauniyar McArthur ya ce ba shakka, batun raguwar kishin ƙasa a tsakanin matasa, gaskiya ne, amma matsalar ta karaɗe ƙasashe da dama, ba kawai Najeriya ba.

'Matasa ba su ga hujjar yin alfahari da Najeriya ba'

Masu zanga-zanga a Lagos

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wasu mazauna birnin Legas sun gudanar da zanga-zangar yin tir da salon mulkin Bola Tinubu a Ranar 'Yanci
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kwamared Abdulmajid, babban jami'i a wata ƙungiyar wayar da kan matasa mai suna Youth Global Vision for Peace in Africa (YGVPA), ya ce matsalar ta ƙara ta'azzara ne tun bayan komawar Najeriya mulkin dimokraɗiyya a 1999.

Ya ce gwamnatoci ba su mayar da hankali wajen samar da ilmi da walwala da jin daɗin matasa ba.

Dr Kole Shettima a nasa ɓangare, ya ce matasan da suka taso ba su san daɗin Najeriya ba.

"Ba su san yanda aka sha wahala, aka yi yaƙin neman ƴancin ƙasa da gwagwarmayar da aka yi ba. Irin yadda mutane suka mutu. Irin wahalolin da mutane suka sha, wayansu ma an sa su a gidan yari."

Wannan duka, su ba su sani ba, in ji Kole Shettima.

Bugu da ƙari gwamnatoci ba su mayar da hankali wajen yin dokokin da suka dace da za su inganta rayuwar matasa ba, Kwamared Abdulmajid ya ce.

A cewarsa: "Idan ka lura a ƴan shekarun nan da suka wuce, matasa sun fuskanci barazana ta fuskar ilmi, ta fuskar tattalin arziƙi, ta fuskar tsaro".

"Har ma alƙaluma sun nuna, kusan Najeriya ce ta zama cibiyar talauci a duniya."

Kole Shettima ya ce kusan za a ce Najeriyar nan ba ta yi wa matasanta abin da ya kamata a ce ƙasa ta yi wa mutanenta ba.

Ra'ayin jami'an biyu sun zo ɗaya a kan cewa matasa ba su ga hujjar da za ta sanya, su riƙa jin alfaharin kasancewarsu ƴan Najeriya ba.

"Amma kuma in muka duba, dattawa da tsofaffi waƴanda suka sha gwagwarmayar neman ƴanci da faɗi-tashi da yanda aka kulle mutane da sauransu.

"Za a ga ƙasa ta ba su ƴanci. Sun samu ilmin da za a ce mai kyau (ne). Sun samu aikin yi. Haka ma sha'anin sana'o'i da sauransu, Najeriya ta ba su, amma idan aka kwatanta da matasanmu na yau, za a iya cewa su ba su ji daɗin waɗannan abubuwa ba."

Ƙwararren ya ce kusan komai da komai su suke yi wa kansu. Rayuwarsu na cike da wahala, shi ya sa ba su da wannan kishin na jin cewa Najeriyar nan tasu ce, in ji shi.

Yayin da Kwamared Abdulmajid ya ce ba mamaki, zaizayewar kishin ƙasa a zukatan matasa, na da alaƙa kai tsaye da yadda gwamnati ta tanadi makomar rayuwar matasa.

'Akwai babban hatsari'

Ɗan gwagwarmayar ya ce hakan zai iya sanya matashin da ba shi da zurfin tunani, shiga hanyoyin aikata laifi da bore da kuma nuna bijirewa ga ƙasa.

Ya kuma ce: "In ka lura za ka ga matasa, da su ake amfani wajen kawo barazana ga harkar tsaro. Da su ake amfani, ake bangar siyasa. Da su ake yin amfani wajen aikata abubuwa daban-daban na laifi."

A cewarsa, hakan na sanya matasa su yi ta rige-rigen fita daga ƙasar zuwa ƙetare a matsayin ƴan ci-rani ta kowacce hanya.

Dr Kole Shettima ya ce babban hatsarin rashin kishin ƙasa shi ne, idan wani abu da ya taso da ke buƙatar sadaukarwa da yin tsayuwar daka da sayar da rai domin fansar al'ummar ƙasa, matasan ba za su ga dalilin da zai sa su je su hidimta wa ƙasar ba.

Kwamared Abdulmajid Sa'ad ya ce kusan kullum ƙungiyarsu na samun rahotanni na yadda matasa ke ci gaba da tsallakewa suna barin Najeriya.

"Matasa a kodayaushe, da waƴanda suka yi karatu da waƴanda ba su yi ba, kullum neman hanyar ficewa daga ƙasar suke, saboda dusashewar kyakkyawar makoma," Kwamared ya ce.

Ya ce idan hakan ta ci gaba, za a wayi gari, an rasa kyakkyawan shugabancin da zai zo ya gina ƙasa.

"Ka ga an samu shuwagabanni suna kwashe dukiyar ƙasa ta haramtacciyar hanya. Kuma suna haɗa baki da wasu marasa kishi, ana cutar da ƙasa."

Dr Kole Shettima kuma ya ce, idan abin Allah ya kiyaye wani yaƙi ko wata masifa ta taso wa ƙasar, su ba za su ga cewar wannan yaƙin da ya tunkaro Najeriya, nasu ba ne, balle har su shiga, su yi tsayin dakan da zai tabbatar ƙasarsu ta yi galaba.

"Kai ko aiki suke yi ma, za ka ga aikin kawai rabi-da-rabi suke yi, saboda babu wannan kishin a jikinsu."

Ta yaya za a sauya zukatan matasa?

  • Koyar da tarihin Najeriya

Dr. Kole Shettima na ganin ta hanyar dawo da darasin tarihi ko kuma inganta shi a makarantun ƙasar, ana iya cusa wa matasa hujjar da za su tsaya, su dage su yi kishin ƙasarsu.

Ya nunar da cewa hatta matasan da suka yi ilmi mai zurfi, za a ga suna da ƙarancin sanin tarihin gwagwarmaya da wahalar da aka yi wajen kafa Najeriya.

Kuma in ji shi, tarihi ne zai koya wa matashi cewa kowa da haɓarsa yake tagumi, a ko'ina a duniya, ƴan ƙasa ne suke yin tsayin daka, jini da tsokarsu, su gina ƙasarsu.

Haka zalika ta hanyar tarihi, matasa za su fahimci kowacce ƙasa ta wuce zamunna marasa daɗi a tsawon rayuwarta, wasu ma taɓarɓarewar rayuwar da aka shiga ta wuce ta ƴan Najeriya.

Shi ma Kwamared Abdulmajid Sa'ad ya ce ba shakka ilmi, ginshiƙi ne wajen dawowa da matasan Najeriya kishin ƙasar da suka rasa a yanzu.

  • Sanar da su nauyi da haƙƙoƙinsu a kan ƙasa

Dr Kole Shettima ya ce kamata ya yi hukumomi su ƙarfafa darasin sanin nauyin da ya rataya a wuyan ɗan ƙasa, da haƙƙoƙin da ɗan ƙasa yake da su a kan ƙasa, a cikin makarantu da ke faɗin Najeriya.

"Abu ne mai muhimmanci kowane ɗan Najeriya ya san cewa yana da haƙƙi a kan ƙasarsa, ciki har da haƙƙin ta kare shi daga cutarwa, ta kare mutuncinsa. Kuma akwai haƙƙin a sama masa ababen more rayuwa kamar tituna da lantarki da ruwan sha da sauransu," a cewar masanin.

"Shi kuma ɗaya ɓangaren, akwai nauyin da ke kansa na ya biya haraji, domin gina ƙasa. Akwai nauyin ya yi biyayya ga hukumomin da doka ta kafa. Kuma ya bi dokokin ƙasa, da sauransu."

Dr Kole ya ce rashin sanin nauyin da ya rataya a wuyan ɗan ƙasa ne kan sa ko a lokacin zaɓe ma, sai mutum ya riƙa ganin tamkar wani ɓata lokaci ne kawai.

"Suna ganin to mene ne ma amfaninsa, a kan me za su fita, su sha rana kawai?"