Muhimman abubuwa biyar da Tinubu ya faɗa a jawabinsa na Ranar 'Yanci

Asalin hoton, State House
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce ya duƙufa wajen lalubo hanyoyin kyautata rayuwar 'yanƙasa domin rage musu raɗaɗin da suke ciki.
Cikin jawabinsa na Ranar 'Yanci a ranar Talata, shugaban ya zayyana wasu daga cikin nasarorin da gwamnatinsa ta jam'iyyar APC ta samu cikin wata 16.
Cikin irin abubuwan da ya taɓo har da batun tsadar rayuwa, inda ya ce gwamnatinsa na sane da wahalar da 'yan Najeriya ke sha.
Kazalika, ya bayyana nasarorin da ya ce suna samu kan yaƙi da ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi, da 'yanfashin daji.
Tun hawarsa mulki a shekarar da ta wuce, shugaba Bola Tinubu ya janye tallafin man fetur da kuma karyar darajar naira, abin da ya janyo tsadar rayuwa kuma tashin gauron zabi a farashin abubuwan yau da kullum. Hakan ya sa ‘yan kasar da dama ke wayyo Allah.
A yayin da jami'an gwamnati ke bikin ranar 'yanci su kuwa masu zanga-zanga sun taru ne a Abuja babban birnin Najeriya da kuma Lagos cibiyar kasuwancin kasar domin nuna adawa da tsadar rayuwa da kuma abin da suka ce rashin iya gudanar da tattalin arziki karkashin gwamnatin Tinubu.
Mun duba wasu muhimman abubuwa biyar da ya faɗa yayin jawabin nasa da aka yaɗa kai-tsaye a kafofin yaɗa labaran ƙasar.
Tsadar Rayuwa
Ɗaya daga cikin abubuwan da suka ja hankali a yau bayan bikin har da zanga-zangar tsadar rayuwa da wasu matasa suka yi a wasu biranen ƙasar.
Yayin jawabin nasa, Tinubu ya ce "ina sane da ƙalubalen da akasarinku suke sha fama da su a irin wannan lokaci".
A cewarsa: "Gwamnatinmu na sane cewa da yawanku na fama da hauhawar farashi da kuma neman aikin yi. Ina tabbatar muku an ji koke-kokenku."
Taron Ƙasa na Matasa
A wani gefen kuma, Tinubu ya bayyana aniyarsa ta shirya taron matasa na ƙasa kuma na kwana 30 "da zimmar inganta makomar ƙasa".
"Jagorancinmu a yanzu yana ɗamfare da tunanin makomar da muke son gadar wa jikokinmu, kuma muna sane cewa ba zai yiwu a gina rayuwarsu ta gaba ba ba tare da su a cikin aikin ba. A saboda haka ne nake farin cikin sanar da ku wani Taron Ƙasa Na Matasa."
"Taron zai taɓo muhimman batutuwa kuma ya bai wa matasanmu damar saka hannu wajen gina ƙasa. Taron na kwana 30 zai haɗa kan matasa na ƙasa baki ɗaya domin lalubo mafita game da batutuwa kamar ilimi, da aikin yi, da ƙirƙira, da tsaro, da kuma adalci a zamantakewa."
Yaƙi da 'Yanbindiga
Game da matsalar tsaro kuma, shugaban ya ce sun yi nasarar kashe mayaƙan Boko Haram da 'yanfashin daji kusan 300 cikin shekara ɗaya.
"A ɓangaren tasro, ina farin cikin sanar da ku cewa gwamnatinmu na samun nasara...Aniyarmu ita ce kawo ƙarshen barazanar Boko Haram, da 'yanfashin daji, da garkuwa da mutane, da dukkan wani nau'i na tayar da fitina," in ji shi.
"Karo na ƙarshe da na bincika, 'yan Boko Haram da kwamandojin 'yanfashi sama da 300 dakarunmu suka kashe a arewa maso gabas, da arewa maso yamma, da wasu sassan ƙasar nan."
Ambaliyar Ruwa
Aukuwar bala'o'i na cikin batutuwan da ya taɓo, musamman ambaliyar ruwa.
Ya ce: "Bayan Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya ki ziyara Maiduguri, ni ma na je domin na tabbatar wa mutane cewa wannan gwamnatin tana tare da mutane a cikin halin matsi.
"Yayin zaman majalisar zartarwa da ya gabata, mun amince da kafa asusun rage raɗaɗin bala'o'i domin jawo 'yankasuwa don su tallafa wajen kai agaji cikin sauri.
"Gwamnatinmu ta kuma ba da umarnin yin gwaji kan dukkan madatsun ruwa a ƙasa baki ɗaya domin guje wa bala'o'i a gaba."
Asusun Najeriya na Ƙasashen waje
Da yake magana kan tattalin arziki, Tinubu ya ce matakan da babban banki CBN ke ɗauka sun kawo daidaito a harkokin canjin kuɗi, yana mai cewa ya sa suka biya basuka da kuma ƙara yawan kuɗin da ke cikin asusun Najeriya na ƙasashen waje.
"Mun gaji sama da dala biliyan 33 wata 16 da suka wuce. Tun daga lokacin, mun biya bashin musayar kuɗi na dala biliyan bakwai da muka gada. Mun biya bashin CBN [Ways and Means] na sama da naira tiriliyan 30.
"...Duk da haka, mun yi ƙoƙari wajen ƙara yawan kuɗin da ke cikin asusun Najeriya na ƙasar waje zuwa dala biliyan 37. Za mu ci gaba da ƙoƙarin ganin mun sauke nauyin da ke kanmu."











