Yadda manufofin Tinubu ke yi wa masana'antu 'lahani' a Najeriya

Masana'anta

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

Ƙungiyar masana'antu masu zaman kansu ta ce manufofin da gwamnatin Najeriya ke fitowa da su, da karyewar darajar naira da tsadar kuɗin wutar lantarki sun gurgunta ayyukansu, inda a rana aikin da suke yi baya zarta kashi 30 cikin 100.

Ƙungiyar ta ce duk da ƙorafinsu da neman sauƙi daga gwamnati kan illolin wasu daga cikin manufofinta shiru ake ji.

Ali Sufyanu Madugu, ɗaya ne daga cikin majalisar zartarwa ta ƙungiyar kamfanonin masu zaman kansu wato MAN, ya shaida wa BBC cewa a yanzu masana'antun Najeriya na aiki ne kashi 30 ciki 100 saboda wasu dalilai.

Ya ce, "Dalilan su ne na farko karyewar darajar naira da rashin wadatattun kuɗaɗen waje kamar dala wanda mu masu masana'antu kan yi amfani da su wajen sayo kayan aiki da ma kayan gyare-gyaren injina".

"A bara kamar yanzu dala a hukumance bata wuce naira 400 zuwa da wani abu ba, a yanzu kuma ana maganar dala ta haura naira 1,600, a don haka duk wani mai kamfani idan yana buƙatar ya yi aiki yadda ya kamata sai ya ninka jarinsa sau huɗu."

Ali Sufyanu Madugu, ya ce ƙarin kuɗin wutar lantarki ma da aka yi ya janyo wasu masana'antu basa aiki yadda ya kamata.

Ɗan majalisar zartarwa na kungiyar ta MAN, ya ce ba sau ɗaya ba sau biyu ba, sun sha tuntuɓar gwamnati a kan waɗannan matsaloli amma shiru kake ji, an gaza yin komai.

Ya ce, "Saboda waɗannan matsaloli a yanzu kamfanonin ƙasashen waje da dama sun sayar da jarinsu sun fice sun bar Najeriya, sannan kuma su kansu waɗanda suka rage ɗin ma idan har gwamnati ba tayi wani abu ba su ma za su fice ne su bar ƙasar".

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ali Madugu, ya ce, "Mu dalar da ake sayar mana ta banki ce daga banki banki muke siya, kuma a yanzu idan kana buƙatar dala don kaje ka siyo kayayyakin aiki sai ka yi sati shida zuwa sati takwas baka samu ba".

Ya ce, "Mu babban abin da ke damunmu ma shi ne duk duniya ba inda ake tsawwalawa mai siyan kaya da yawa irin Najeriya, a ƙa'ida idan ka sayi kaya da yawa sawwaƙa maka ake, amma ban da Najeriya.

"Sannan kuma gwamnatin Najeriya bata iya yin wani kan kamfanonin samar da wutar lantarki sai an yi amfani da masu masana'antu saboda mu muna amfani da wutar lantarki to idan an kara kuɗin wutar ai dole muma mu kara kuɗin kaya kuma talaka daga ƙarshe shi ne zai sayi wannan kayan".

"Mu abin da muke so a cire mu daga cikin wannan tsari, ya koma idan gwamnati na son yi wa talakanta wani abu ta ta yi ita da su, ba sai an sanya mu ciki ba."

Ali Sufyanu Madugu, ya ce ya kamata gaskiya gwamnatin Najeriya ta duba halin da masu kamfanoni da masana'antu a ƙasar ke ciki a sauwaƙa musu abubuwa don ciyar da harkokinsu gaba.

Tattalin arzikin Najeriya dai ya shiga mawuyacin yanayi musamman tun cire tallafin man fetur da shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya yi a ranar da ya karɓi mulki cikin watan Mayu na shekara ta 2023.

Cire tallafin man ya sanya farashin kayayyaki sun tashi sannan al'amura sun kara dagulewa, lamarin da ya jefa al'ummar ƙasar cikin mummunan hali.

Masana tattalin arziki na ganin inganta fannin masana'antu wani babban jigo ne wajen samar da ayyukan yi ga miliyoyin matasan Najeriya da ke fama da matsalar zaman kashe wando.

Hakan kuma zai taimaka wajen tsamo miliyoyin iyalai daga kangin talaucin da suke ciki a kasar.