Ko gwamnati za ta iya ƙayyade farashin kaya a Najeriya?

Asalin hoton, getty
Hukumar da ke sanya ido kan farashi da kare haƙƙin masu sayen kaya ta Najeriya (FCCPC) ta bai wa ƴan kasuwa da ke da hannu a tsawwalar farashin kayan masarufi wa’adin wata ɗaya da su karya farashi ko kuma ta ɗauki mataki a kansu.
A wani bayani da ya yi a ranar Alhamis, mataimakin shugaban hukumar FCCPC, Tunji Bello, a lokacin wani taro, ya ce hukumar ta shirya taron ne domin tattauna yadda za ta shawo kan matsalar hauhawar farashin kaya da ayyuka da ta ce, ''ba gaira ba dalili'' da ƴan kasuwa ke haifarwa.
Mataimakin shugaban ya ce bayan wa’adin wata ɗaya da ta bai wa ƴan kasuwar, idan ba su karyar da farashi ba za ta tilasta musu yin hakan.
Me ya sa gwamnati ta bayar da umarnin rage farashin kaya?

Asalin hoton, STATE HOUSE
Kamar yadda shugaban Hukumar FCCPC ya bayyana, sun ɗauki wannan mataki ne bayan binciken da suka gudanar, inda suka gano abubuwa masu ban-tsoro game da tsawwala farashi a Najeriya.
Ya ce "mun gano cewa farashin kayan da ake shigowa da su zuwa ƙasar nan sun bambanta sosai a wurare daban-daban.
Duk da cewa mun yarda akwai matsala a ɓangaren canjin kuɗi wanda hakan ya shafi farashin kaya, amma mun fahinci cewa ana tsawwala farashi fiye da kima a wasu lokutan.
Najeriya dai na fuskantar matsanancin tashin farashi. Duk da cewa a watan Yuli Hukumar ƙididdiga ta ƙasar ta bayyana cewa tashin farashi ya sauka a karon farko cikin sama da shekara ɗaya, amma babu wani bambancin a zo a gani a kasuwanni.
A rahoton da ta fitar, hukumar ta ce tashin farashin ya sauka daga kashi 34.19 cikin ɗari a watan Yuni zuwa kashi 33.4 cikin ɗari a watan Yuli.
Tsawon shekaru ke nan al'ummar Najeriya na fuskantar tashin farashin kaya, tun zamanin mulkin tsohon shugaban ƙasar Muhammadu Buhari.
Sai dai zuwan shugaba mai ci, Bola Tinubu abubuwa sun ƙara ƙamari.
Matakan da shugaban ƙasar ya ɗauka jim kaɗan bayan hawa kan mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023 sun sanya farashin kaya sun yi tashin gwauron zabo.
Cire tallafin man fetur da barin naira ta tantance farashinta a kasuwa na daga cikin manyan abubuwan da suka sanya farashin kaya suka nunnunka.
Lamarin ya kai ga cewa a farkon watan Agusta al'ummar ƙasar sun gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa kusan dukkanin manyan biranen ƙasar.
Mene ne aikin hukumar FCCPC?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Federal Competition and Consumer Protection Commission (FCCPC), hukuma ce wadda dokar Najeriya ta samar a shekarar 2018, tare da ɗora mata alhakin kare masu sayen kaya daga cutarwa da kuma lura da gasa tsakanin kamfanoni.
Aikinta shi ne ta tabbatar kamfanoni masu samar da kaya na samar da su bisa ƙa'ida da cika sharuɗɗa, haka nan za ta sanya ido wajen ganin cewa ba a cutar da al'umma ba.
To amma ko FCCPC na da ikon ƙayyade farashi?
A duk lokacin da abubuwa suka cude game da tashin farashin kaya, kamar halin da ake ciki a Najeriya yanzu, inda al'umma ke fuskantar tashin farashin kaya a kullum, abin da hukumar za ta iya yi shi bayar da 'umarni' ko 'shawara' ga kamfanonin ko ƴan kasuwa su rage farashi.
Amma "hukumar ba ta da ikon ƙayyade farashin kayan" in ji wani masanin dokokin Najeriya kuma malamin jami'a, Dakta Sulaiman Santuraki.
Sai dai a cewarsa, hukumar na da ƴancin ta hukunta duk wanda ya ƙi umarninta ta hanyoyi da dama.
Wasu daga cikin hanyoyin sun haɗa da cin tara ko kuma rufe kasuwancin wanda ya ƙi bin umarninta.
Sai dai baya ga haka akwai kuma kotun sauraron ƙorafe-ƙorafe ta hukumar, wadda ita kuma ke da hurumin sauraron koke-koken kamfanoni ko kuma ƴan kasuwar da ke ganin hukumar ba ta yi musu adalci ba.
'Barazana ce kawai'
Farfesa Muhammad Muttaqa Usman, masani kan harkokin tattalin arziki a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a Najeriya, ya ce umarnin da hukumar FCCPC ta bayar abu ne da ba zai yiwu ba, ''barazana ce kawai'' bisa la'akari da tsarin kasuwanci na Najeriyar - na jari-hujja.
Ya ce abu na farko da za a duba a gani shi ne "ta yaya gwamnati ta san farashin da ƴan kasuwa suka sayo kayansu da irin ɗawainiyar da suka yi har suka kawo kayansu kasuwar suke kuma neman riba?
Haka nan farfesan ya ce wani cikas da hukumar za ta fuskanta shi ne rashin isassun jami'an da za su tabbatar ana bin umarnin da ta bayar.
''Ba su da ma jami'an da za su ƙaddamar da wannan abu da suke cewa za su yi a jihohi 36,'' kamar yadda ya shaida wa BBC.
Shi ma Dakta Nasiru Sa'id Musa, masanin tattalin arziƙi a jami'ar Lead Prenour, da ke Abuja, ya shaida wa BBC cewa a tsarin tattalin arziƙi da ake da shi yanzu a Najeriya bai bai wa gwamnati damar ƙayyade farashi ba.
Ya ce: ''Gwamnati ba ta da iko idan ka sayo kayanka ba ta tallafa maka ba kuma ta zo rana ɗaya wai ta ce za ta sanya maka ƙa'ida kan farashin da za ka sayar da kayanka, wannan babu adalci, kuma ba wannan tsarin a gwamnati, sai dai idan wani abu ne na daban kuma za a yi.''
Masanin ya ce, wannan barazana da gwamnati ke yi cewa za ta tilasta wa ƴan kasuwa karyar da farashi ba abin da za ta haifar, inda ya yi gargaɗin cewa hakan na iya haifar da tsadar kayan.
Mafita game da hauhawar farashin
Dangane da mafita a kan halin da ake ciki na tsawwalar farashin, na kayayyaki a Najeriya, Farfesa Muhamnmad Muttaqa Usman ya bayyana wa BBC cewa, a harkar tattalin arziƙi kasuwa ita ke nema wa kanta farashi.
Idan gwamnati tana son farashin kaya ya ragu sai ta rage haraji ta gyara hanyoyi ta yadda ƴan kasuwa za su iya sufurin kayansu ba tare da wasu matsaloli ba, ta kuma tabbatar jami'ai ba sa takura musu, to da wannan gwamnati za ta iya cewa ga abubuwan da ta yi wa ƴan kasuwar a don haka ta nemi su rage farashi.
Sannan kuma, ''idan gwamnati tana son karya farashi sai ta antayo kayan da take son farashinsu ya ragu, ta cika kasuwa da su, wannan zai sa farashin kayan ya karye,'' in ji shi.
Haka shi ma, Dakta Nasiru Sa'id Musa, ya ce akwai matakai na ƙwarya-ƙwarya da tsaka-tsaki da kuma na dogon zango.
Ya ce, mataki na ƙwarya-ƙwarya shi ne gwamnati ta soke haraji a kan wasu kayan, domin duk inda aka samu tsadar kaya, haraji na daga cikin abubuwan da ke tayar da farashi.
Sannan na biyu gwmanti ta tsayar da farashi a kan dala, sannan kuma ta samar da dalar ga ƴan kasuwa da masana'antu masu shigo da kayayyaki.
''In ba haka aka yi ba, to duk wani abu da za su yi ba zai yi aiki ba, bayar da tallafi ba zai fitar da mutane daga cikin talauci, ko tirelar shinkafa nawa za a raba, hakan ba zai magance matsalar ba,'' in ji shi.
Ya ce, ''Sannan mataki na tsaka-tsaki da na dogon zango, waɗannan abubuwa ne da za su bayyanar da kansu a irin wannan lokacin da aka tanada.











