Me dokar Najeriya ta ce kan taron siyasa ba da izinin ƴansanda ba?

Wani mutum na jawabi ga dandazon taro

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 5

A Najeriya ƴan ƙasar na ci gaba da dora ayar tambaya game da abin da dokokin ƙasar suka ce kan neman izinin ƴansanda kafin gudanar da taron siyasa.

Lamarin na zuwa ne bayan rundunar ƴansandan kasar a jihar Kaduna ta ce ta ƙaddamar da bincike kan wani taro da tsohon gwamnan jihar, Mallam Nasir El-Rufai ya jagoranta da suke zargin ya tayar da rikici.

A ƙarshen watan da ya gabata ne aka El-Rufai da wasu ƴaƴan jam'iyyar ADC suka gudanar da wani taro a jihar ta Kaduna.

Sai dai taron ya gamu da cikas bayan da wasu ƴandabar siyasa suka far wa taron tare da tarwatsa mutane.

Cikin wata sanarwa da ƴansandan jihar suka fitar, sun ce suna binciken lamarin da ya faru a wurin taron - wanda jam'iyyar ADC ta shirya ba tare da neman izinin ƴansanda da sauran jami'an tsaro ba.

Sanarwar ta ce hukumomi sun yi wa masu shirya taron jerin gargaɗi da shawarar kauce wa yinsa.

A nasa ɓangare tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya ce a ƙarƙashin dokokin ƙasar, ba dole sai an nemi izinin ƴansanda kafin gudanar da taron siyasa ba.

Kan wannan batu ne muka ji ta bakin lauyoyi, da masana kundin tsarin mulkin Najeriya domin jin abin da dokokin ƙasar suka ce game da shirya taron siyasa.

Me dokokin Najeriya suka ce?

wasu littafai uku da abun bugawa na kotu da alamar ma'auni na kotu

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Barista Abba Hikima Fagge wani fitaccen lauya ne a Najeriya kuma masanain kundin tsarin mulkin ƙasar, ya kuma ce sashe na 40 da na 39 da ke magana a kan taron jama'a da ƴancin faɗin albarkacin baki sun yi magana a kan abin da ke faruwa a lokacin taro.

''Su ne sassan da suka yi magana a kan taruwar jama'a domin tattaunawa kan ƴancin faɗin albarkacin bakinsu da motsi ko zirga-zirga wanda shi kuma sashe na 35 ne'', in ji shi.

Lauyan ya ce dole sai an haɗa waɗannan sassa guda uku kafin fitar da abin da wannan maƙala ta ƙunsa.

''Waɗannan sassa sun bai wa ƴan Najeriya dama su yi taronsu, su kuma faɗi abin da suke so, matsawar ba su karya doka ko taɓa haƙƙin wani ba'', a cewar lauyan.

Sai dai lauyan ya ce akwai dokar da ake kira ''Public Order Act'' da ta jima ana amfani da ita.

Ya ƙara da cewa a cikin wasu saɗarorin wannan doka akwai wuraren da suka ce sai an nemi izinin ƴansanda kafin yin taruka.

Sai dai lauyan ya ce da daɗewa wasu kotunan ƙasar sun soke irin wannan tanadi, na neman izinin ƴansanda, suna masu cewa sun ci karo da waɗancan sassa da aka lissafa a sama, don haka aka daina amfani da su.

''Wannan abu ya faru a shari'ar da aka yi tsakanin babban sufeton ƴansanda da Buhari a 2005', a cewar lauyan.

''Kuma ni da kaina na shigar da ƙara a shari'ar da na yi tsakanina da babban sufeton ƴansanda, domin tabbatar da wannan doka, kuma na yi nasara'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.

Wajibi ne a nemi izinin ƴansanda don yin taro?

Babban sifeton ƴansandan Najeriya na zaune a kan kujerarsa yana jawabi

Asalin hoton, Nigeria Police

Barista Abba Hikima Fagge ya ce babu wasu taruka da ke buƙatar izinin ƴansanda kafin gudanar da su a ƙarƙashin dokokin Najeriya.

''Ƴansanda ba su da damar bayar da izinin yin taro, amma sanar da su yana da amfani ko don su bayar da tsaro a wurin taron'', kamar yadda ya bayyana.

Lauyan ya ce a dokance akwai bambanci tsakanin ''neman izini'' da kuma ''sanarwa''.

''Shi neman izini a iya hana ka, amma sanarwa kana gaya wa mutum ne kawai in ya ga dama ya zo, in kuma bai gani ba ya ƙi zuwa'', in ji shi.

Ya ce sau da dama ƴansanda kan ce ba su bayar da izinin taro ba, saboda suna fargabar samun aikata abin da ya saɓa wa doka.

''Suna tsoron kar a samu wasu da za su shiga cikin taron domin tayar da fitina ko yin abubuwa na karya doka'', in ji shi.

Ya ƙara da cewa da haka suke fakewa sai su ce ba su bayar da izinin yin taro ba.

Me ya kamata ƴansanda su yi idan suna fargaba?

Wasu ƴansanda

Asalin hoton, Nigeria Police

Fitaccen lauyan ya ce abin da ya kamata ƴansanda su yi shi ne su yi ƙoƙarin gano masu tayar da hargitsi a wurin taro domin su kama su.

"Don wani mutum guda ko wasu tsiraru za su kawo ruɗani a taron da wasu suka shirya, ba zai zama hujjar hana mai ƴanci haƙƙinsa ba'', in ji shi.

Ya ƙara da cewa idan kundin tsarin mulkin ƙasa ya bai wa mutum ƴanci, bai kamata ka hana mutum yancin domin wani ba.

''Ai dama aikin ƴansanda shi ne hana aikata laifi da kama masu laifi, don haka sai a kama waɗanda ake zargi, su kuma masu ƴanci a bar su, su yi ƴancinsu'', in ji shi.

Shin akwai tarukan da doka ta haramta?

Wasu gangami

Abba Hikima ya ce akwai tarukan da doka ta haramta yinsu a wasu lokuta, saboda wasu dalilai ko ƙa'idoji.

Ya ce ɗaya daga cikin irin waɗannan taruka shi ne taron yaƙin neman zaɓe, kuma dalili kan haka shi ne akwai dokar zaɓe da ta haramta yin hakan.

''Wannan ba za a yi ba dole sai lokacin da doka ta tanadi fara shi, idan lokacin ya wuce to laifi ne mutum ya shirya irin waɗannan taruka a ƙarƙashin dokokin zaɓe,'' in ji Abba Hikima.

To sai dai Lauyan ya ce shi taron yaƙin neman zaɓe daban yake da taron siyasa, ''siyasa tana da faɗi, abin da kawai aka hana shi ne yaƙin neman zaɓe, kamar yadda ya yi ƙarin haske.