Ko gwamnatin Tinubu na yin raba-daidai a ayyukanta tsakanin yankunan Najeriya?

Tinubu

Asalin hoton, Twittter/@officialABAT

Lokacin karatu: Minti 4

A daidai lokacin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke murnar samar da ayyukan ci gaba da ta ce ta aiwatar a sassa daban-daban na faɗin Najeriya, muhawara ce ke ƙara zafi a tsakanin al'umomin yankunan ƙasar kan wane ɓangare ne ya fi sharɓar romon dikomuraɗiyya a mulkin.

An daɗe ana zargin gwamnatin na Tinubu da fifita yankinsa na kudancin Najeriya, musamman yankin kudu maso yamma, inda jiharsa ta Legas take da hanyar gudanar da manyan ayyuka da suka laƙume maƙudan kuɗaɗe.

Sai dai gwamnatin ta sha fitowa tana nanata cewa ita ta kowa ce, kuma kowane ɓangare yana samun ayyuka, kuma zai ci gaba da samun ayyuka daga gwamnatin ta tarayya.

Baya ga zargin Tinubu da fifita wani ɓangare a ayyuka, ana kuma caccakar gwamnatin da fifita yankinsa wajen naɗe-naɗen muƙaman gwamnatin ƙasar da ake gani suna da muhimmanci, lamarin da gwamnatin ta musanta tare da cewa kowane ɓangaren ƙasar ya samu rabonsa na muƙamai.

Najeriya dai na da tarihin amfani da ɓangaranci, musamman ƙabilanci a siyasa, musamman a lokutan zaɓe, lamarin da ke dawowa a lokacin da ake mulki, inda ƴan yankin da shugaban ya fito suke fitowa suna buƙatar samun fifiko a ayyuka da muƙamai.

Fifita kudancin Najeriya?

A wani nazari da jaridar Daily Trust ta yi kan ayyukan da gwamnatin tarayya a ƙarƙashin Bola Tinubu ta aiwatar a shekara biyu, ta ce majalisar zartarwa ta amince da muhimman ayyuka da suka laƙume biliyoyin kuɗaɗe a yankin kudu maso yamma sama da na sauran yankunan ƙasar.

A rahoton, an ce gwamnatin Tinubu ta amince da ayyuka a yankunan ƙasar a shekara biyu kamar haka:

  • Kudu maso Yamma: Naira tiriliyan 5.97
  • Kudu maso Kudu: Naira tiriliyan 2.41
  • Kudu maso Gabas: Naira biliyan 407.49
  • Arewa ta Tsakiya da Abuja: Naira tiriliyan 1.15
  • Arewa maso Yamma: Naira tiriliyan 2.7
  • Arewa maso Gabas: Naira biliyan 403.98

Haka kuma akwai wani ƙarin naira tiriliyan 2.70 da aka amince domin aiwatar a wasu muhimman hanyoyi a ƙasar, inda jimillar kuɗin da majalisar ta amince da shi ya kama naira tiriliyan 15.79.

Daga cikin muhimman ayyukan da ake kwatance da shi na kwana-kwanan nan akwai gyara tare da zamanantar da sashen jigilar fasinjojin ƙasashen waje a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas, wanda aka kasafta masa laƙume naira biliyan 712.

Arewa ta fi mora - Gwamnati

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sai dai a wani martani da gwamnatin ta mayar kan zarge-zargen na fifita kudancin Najeriya, musamman jihar Legas, ta ce ita gwamnati ce ta kowa da kowane ɓangare na ƙasar ba tare da fifiko ba.

A sanarwa da ministan watsa labaran Najeriya Mohammed Idris ya fitar, ya ce zargin yana cike da labaran bogi da ɓoye gaskiya.

"Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu tana aiki ne da tsarin gaskiya da amana da adalci ga kowane ɓangare wajen raba muƙamai da aiwatar da ayyukan gwamnati a yankuna shida na ƙasar daidai-wa-daida ba tare da nuna fifiko ba."

Ministan ya ce yanzu haka akwai muhimman ayyuka da gwamnati ke aiwatarwa a tare a sassa daban-daban na ƙasar.

"Gwamnatin ta samu kuɗi domin gina layin dogo na zamani a Kano da zai ci kuɗi naira biliyan 150, da na Kaduna da zai ci kuɗi naira biliyan 100 kamar yadda aka yi a Legas da Ogun. Haka kuma gwamnatin ta gyara ƙananan asibitoci a matakin farko guda 1,000 a faɗin ƙasar baki ɗaya."

A game da kuɗaɗen da aka amince wa kowane ɓangare na ƙasar, gwamnatin tarayya ta fitar da nasa alƙaluman kamar haka:

  • Arewa maso Yamma: Naira tiriliyan 5.97 (sama da kashi 40)
  • Kudu maso Kudu: Naira tiriliyan 2.41
  • Arewa ta Tsakiya: Naira tiriliyan 1.13
  • Kudu maso Gabas: Naira biliyan 407
  • Arewa ta Gabas: Naira biliyan 400
  • Kudu maso Yamma (banda Legas) - Naira biliyan 604

Sai dai martanin na gwamnatin Najeriya ya bar baya ba ƙura, inda mutane suke tambayar me ya sa gwamnatin ta cire jihar Legas daga cikin kuɗaɗe da aka amince wa yankin Kudu maso Yamma?

Jihar Legas ce jihar shugaban, inda ya yi gwamna sau biyu, sannan ya yi sanata kafin zama shugaban ƙasa.

Ministan ya ce bayan hanyoyi, gwamnatin Tinubu na cigaba da aikin bututun gas na AKK a arewacin Najeriya da kuma cigaba da haƙo man fatur a yankin, ciki har da Kolmai da ke tsakanin jihohin Bauchi da Gombe, wanda a kwanakin baya shugaban NNPCL ya ce za su koma bakin aiki.

Ya ce gwamnatin Tinubu ta tarar da kashi 5 ne kacal a aikin layin dogo na Kano zuwa Maradi, amma yanzu ya ce sun kai kashi 67.

Ya ce Tinibu yana samun karɓuwa da aminta daga ƴan Najeriya domin a cewar ministan, "shugaban ya nuna cewa shi shugaba ne na kowa kuma mai adalci, wanda yake da burin tafiya da kowane ɓangare tare da tabbatar da haɗin kan ƙasar. Ƴan Najeriya su kwantar da hankali, domin babu wani ɓangaren ƙasar da za a bari a baya a wannan gwamnatin."

Ɓangaranci a mulki

Daga cikin fitattun ƴansiyasan arewacin Najeriya da suka zargi gwamnati da caccarta akwai tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da takwaransa na Kano, Rabiu Musa Kwankwaso.

Haka kuma ƙungiyar tuntuɓa ta arewacin Najeriya ACF ta soki shugaban ƙasar, wanda ta zarga da fifita yankinsa na kudancin Najeriya sama da arewacin ƙasar da ta ce ta fi tarin ƙuri'a.

Amma ko a bara a lokacin da aka fara zarge-zargen, mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima wanda shi ne babban mai riƙe da muƙamin siyasa daga arewacin Najeriya ya yi watsi da zargin, inda ya ce hakan siyasa ce kawai."

A lokacin ya ce daga cikin ministoci 46 na lokacin, guda 24 ƴan arewa ne, "kuma akwai manyan shugabannin ma'aikatun gwamnati waɗanda suke da amfani ga arewa, kamar fannin tsaro, da fannin ilimi da noma dukkansu daga ɓangaren arewacin ƙasar suke."

Sai dai ba yau aka fara zargin shugaban ƙasa da zargin fifita yankinsa ba idan yana gudanar da mulki, domin kuma a zamanin tsohon shugaban ƙasa marigayi Muhammadu Buhari, zan zarge shi da fifita yankin arewacin ƙasar, lamarin da shi ma jami'ansa suka riƙa musantawa.