Za mu koma aikin haƙo ɗanyen mai a arewacin Najeriya - NNPCL

Asalin hoton, NNPC Limited/Facebook
Shekara biyu bayan ƙaddamar da aikin haƙo ɗanyen man fetur a iyakar jihohin Bauchi da Gombe - wanda tun daga wancan lokaci ba a ci gaba da aikin ba - a yanzu sabon shugaban kamfanin man fetur na Najeriya Bayo Ojulari ya fada wa BBC cewa za a koma kan aikin.
Aikin da aka ƙaddamar a gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari da ta gabata, ya sanya al’ummar arewacin ƙasar sun fara kyakkyawar fatan cewa yankin zai bi sahun wasu yankunan ƙasar da ke samar da man fetur wanda tattalin arzikin ƙasar ya dogara a kai.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ƴan Najeriya suke cigaba da kokawa kan tsadar rayuwa, wadda ke da alaƙa tashin farashin man fetur a sanadiyar cire tallafin da gwamnati ke bayarwa a bangaren.
Tun a jawabin Shugaban Najeriya Bola Tinubu na farko bayan shan rantsuwar kama mulki ne ya sanar da cire tallafin man fetur.
Tun daga lokacin ne farashin man fetur ɗin ya fara tashi, wanda kamar yadda aka saba, farashin kayayyaki da kuɗin sufuri da sauran abubuwa suma suka tashi a faɗin ƙasar.
Shi dai tallafin man fetur ɗin nan wasu kuɗaɗe ne da gwamnatin tarayya ke fitarwa domin biyan wani ɓangare na kuɗin da ake kashewa wajen sayowa da shigo da tataccen man fetur daga kasuwannin duniya zuwa Najeriya tare da sufurinsa zuwa jihohi domin ƴan ƙasar su same shi a farashi mai rahusa.
Hakan ya sa ƴan arewacin Najeriya suka shiga murna da farin cikin ganin za a fara haƙo ɗanyen man daga yankinsu, wanda hakan zai sa su same shi ba tare da wahalar sufuri ba.
Haƙo ɗanyen mai a Kolmani

Asalin hoton, Fadar Shugaban Najeriya
A ranar Talata 22 ga watan Nuwamban shekarar 2022 ce shugaban Najeriya na wancan lokacin, Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da aikin haƙo ɗanyen man fetur a yankin Kolmani da ke iyakar jihohin Bauchi da Gombe da ke arewa maso gabashin ƙasar, wanda shi ne karon farko da aka fara aikin haƙar man a arewa.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Haka kuma bayan wannan, kamfanin na NNPCL ya bayyana cewa cikin a watan Maris na 2023 ne za a fara aikin haƙo ɗanyen man fetur a jihar Nassarawa da ke arewa ta tsakiyar ƙasar.
Sai dai tun daga lokacin, sai aka ji shiru, har aka yi zaɓe sabuwar gwamnati ta fara aiki, lamarin da ya wasu ƴan yankin suka fara tambayar ko dai dama an ɗanɗana musu zuma a baki ne kawai.
A game da wannan ne sabon shugaban kamfanin NNPCL, Injiniya Ojulari ya ce ƴan yankin su kwantar da hankalinsu domin za su koma bakin aikin kamar yadda ya bayyana a tattaunawarsa da BBC.
A cewarsa, "Za mu cigaba da aikin haƙo mai a Kolmani da sauran wurare. Bayan aikin haƙo man, za mu kuma tabbatar da cewa mun gama aikin bututun man gas daga Ajaokuta zuwa Kano," in ji shi.
Ya ce waɗannan ayyukan za su sa a sake buɗe kamfanonin da aka kulle a baya domin su cigaba da aiki sannan a buɗe wasu sababbi.
"Wannan zai sa a samu amfani a yankin, wanda zai kai ga kowa ya ci moriyarsa saboda arziki zai bunƙasa. Don haka dole ne za mu koma mu cigaba da wannan aikin," in ji shugaban na NNPCL.
Ojulari ya ƙara da cewa shi ma ɗan arewa ne, inda a cewarsa ya yi mamakin martanin da wasu ƴan yankin suka riƙa yi lokacin da aka sanar da naɗa shi.
Sai ya buƙaci ƴan yankin da ma ƴan ƙasar baki ɗaya da su ba shi goyon baya, kuma su taimaka masa da addu'a domin ya samu nasarar ciyar da yankin da ma ƙasar gaba.
Sulhu da Dangote

Asalin hoton, Dangote Refinery
Wani al'amari da ya matuƙar jan hankalin ƴan Najeriya daga tsakiyar bara zuwa bana shi ne batun matatar man fetur ta Dangote da saɓanin da ya shiga tsakaninta da kamfanin NNPCL.
A watan Oktoban 2024 ne aka fara aiki da yarjejeniyar da aka ƙulla cewa NNPCL za ta riƙa sayar wa matatar Dangote ɗanyen man fetur da naira.
Hakan ya sa matatar ta Dangote ta fara sayar da man fetur ɗin a Najeriya a farashi mafi sauƙi, ƙasa da farashin kamfanin NNPCL, wanda daga baya kamfanin NNPCL ɗin ya rage nasa farashin.
Sai dai a farkon watan Maris kamfanin na NNPCL ya ce yarjejeniyar ta tsawon wata shida ta ƙare, wanda ya jefa fargaba a zukatan ƴan ƙasar na tunanin za a koma gidan jiya a farashin man fetur ɗin, har masana suka yi hasashen idan ba a samu maslaha ba, farashin man fetur ɗin zai saka tashi bayan sauƙin da aka fara samu.
A game da wannan takun-saƙar, sabon shugaban kamfanin man na NNPCL ya ce tuni ya fara ɗaukar matakan kawo ƙarshen rashin jituwar da ke tsakaninsu da kamfanin mai na Dangote.
Injiniya Ojulari ya ce Dangote ya yi ƙoƙari, wanda a cewarsa hakan abin yabawa ne.
Ya ce, "maganar rikici mun zauna mun yi magana. Daga yanzu za mu haɗa kai ne domin samun ci gaba yadda ya kamata, domin mutanen da suke neman mai a gidajen mai su riƙa samu a lokacin da suke so," in ji shi.
Ya ƙara da cewa idan akwai wata matsala ko kuskure zama za su su fahimci juna a gyara, "amma za a daina jin rigima a tsakanin kamfanin NNPCL da matatar Dangote. Za mu haɗa hannu domin domin amfanar da Najeriya."
Farashin mai a duniya
Shugaban kamfanin man na ƙasa ya kuma bayyana cewa yanzu farashin ɗanyen mai ya faɗi a kasuwannin duniya, wanda hakan ya sa ƙasar ba ta samun kuɗin shiga da ta yi hasashen samu.
Ya ce, "kuma wannan kuɗin da shi aka yi kasafin kuɗin Najeriya, inda ake hasashen cewa idan an sayar da mai ne za a samu kuɗin da za a yi amfani da wajen ayyukan gina ƙasa."
Sai dai ya ce duk da haka suna ƙoƙarin rage kashe kuɗaɗen gudanarwa a harkokin man, "idan mun samu rage kashe kuɗin, yana yiwuwa kuɗin da za mu samu daga sayar da man da gas ya ishe mu."
Sai dai a game da ƙorafin da ƴan ƙasar sukan yi na rashin ganin a ƙasa idan farashin ya sauka a kasuwannin duniya, Ojulari ya ce haka ya kamata a riƙa yi idan farashi ya sauka.
"Amma idan dillalan sun saya man ne a farashin baya, sai yanzu farashin ya sauka dole su sayar a yadda suka sara. Idan suka sake saya a sabon farashin ne za su rage. Amma muna fata nan ba da jimawa ba za mu yi ƙoƙari mutane su riƙa gani a ƙasa idan an samu irin haka."











