NNPC zai soma hako danyen mai a jihar Nassarawa

.

Asalin hoton, NNPC/TWITTER

Kamfanin hakowa da sarrafa albarkatun man fetur na Najeriya NNPCL, ya bayyana cewa cikin watan Maris din 2023 ne za a fara aikin hako danyen man fetur a Nassarawa.

Shugaban Kamfanin Mele Kyari ne ya bayyana hakan a wani sako ta shafin Tuwita, inda ya ce hakan ci gaba ne da aikin hakon mai da nufin samar da rijiyar mai ta farko a jihar ta arewacin Najeriya.

Ya shaida hakan a lokacin da yake karbar bakuncin tawagar fitattun yan asalin jihar ta Nassarawa, karkashin jagorancin Gwamnan jihar, Injiniya Abdullahi Sule a ofishin kamfanin da ke Abuja, babban birnin kasar.

Gano arzikin man a Nassarawa ya zo ne kusan wata biyar bayan da NNPC ya soma aikin hako mai a yankin Kolmani, da ke tsakanin jihohin Bauchi da Gombe.

Tun a shekarar 2019 ne kamfanin na NNPC ya bayyana gano albarkatun man fetur a yankin na Kolmani.

.

Asalin hoton, OTHERS

Kyari ya ce binciken da aka gudanar ya nuna cewa akwai tabbacin kasancewar albarkatun ruwa mai yawa a jihar.

Cikin wata sanarwa ta baya-bayan nan da NNPC ya fitar, Mele Kyari ya bayyana bukatar a hanzarta gudanar da aikin, ganin cewa karkatar da kasashen duniya suka yi zuwa ga makamashi ya janyo raguwar zuba jari a bangaren mai.

"Ya kamata a gaggauta yin aikin saboda kasashen duniya na janyewa daga dogaro da man fetur, idan ba haka ba, shekaru 10 daga yanzu, babu wanda zai amince ya zuba kudi a kasuwancin man fetur." kamar yadda sanarwar ta ambato shugaban NNPC na fadi.

A cewarsa, samun hadin kai daga al'umma da yanayi mai kyau na da matukar muhimmanci wajen samun nasarar aikin, domin kaucewa irin barnar da yan bindiga ke yi wa bututan mai a yankin Neja Delta.

A martaninsa, Gwamna Sule ya taya mahukuntan kamfanin NNPC da gwamnatin tarayya murna, saboda kokarin da suka yi na ganin an soma aikin samar da mai a Kolmani da Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar a Nuwambar 2022.