Buhari zai kaddamar da ayyukan hakar man fetur a iyakar Bauchi da Gombe

A ranar Talata ne ake sa ran shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, zai kaddamar da ayyukan bunkasa hakar man fetur a yankin Kolmani da ke iyakar jihohin Bauchi da Gombe.
Kamfanin samar da man fetur na Najeriyar, NNPCL, ya ce shekara biyu da suka wuce ne aka tabbatar da gano tarin arzikin man fetur mai yawan da za a iya sayarwa a yankin.
Wannan ne karon farko da ake haƙo man fetur a Arewacin Najeriya.
Wakilin BBC da yake can yankin na Kolmani, ya ce bayanai sun nuna cewa akwai karin wasu rijiyoyin da aka kammala aikinsu kamar wannan a yankin na Bauchi da Gombe, waɗanda za a ci gaba da aikin samar musu da wuraren da za a sarrafa man fetur da dangoginsa, irin sa na farko a arewacin Najeriya, kana akwai wasu da dama da ake aikin haƙo man.
Bugu-da-kari kuma, bayan Shugaba Buhari ya kaddamar da aikin bunkasa ayyukan hakar man fetur din, za a ci gaba da aikin hako sauran wuraren da aka gano don tantance yawan man fetur da iskar gas din da ke karkashin kasa wanda a za a iya fitar wa tare da sarrafa danyen man fetur din da iskar gas.
Ana sa ran za a gina matatar mai da sauran ayyukan albarkatun man.
Tuni dai al'ummar jihohin Bauchi da Gomben, musamman mazauna yankunan da ake aikin hako man fetur din suka bayyana farin cikin su da wannan aiki.
Wasu daga cikinsu sun shaida wa BBC cewa, sun ji dadi da aka kawo wannan aiki yankinsu tare da fatan samun alkhairi mai yawa dama samun ayyukanyi ga mazauna wajen.
Sun ce suna fatan kuma aikin bunkas ahakar man fetur din zai kawo wa yankinsu ci gaba da zaman lafiya mai dorewa.
A shekarar 2016 ne kamfanin mai na Najeriya NNPC, ya kaddamar da aikin binciko man fetur a arewacin kasar, abin da ya kai ga gano dimbim albarkatun man fetur din a jihohin Bauchi da Gombe da Borno da kuma jihar Neja.
Najeriya dai ita ce kasar da tafi kowacce fitar da danyen mai a kasuwannin duniya a nahiyar Afrika, sai dai kuma takan kashe makudan kudaden wajen shigo da tataccen man da ake amfani da shi a cikin kasar saboda lalacewar matatun man kasar.
A lokuta da dama gwamnatoci daban-daban sun sha lasar takobin gyara matatun man kasar domin wadatar da ita da man take bukata, amma daga baya sai maganar ta bi shanun sarki.
Amma a yanzu rahotanni an ambato gwamnati na cewa gano dimbin man da aka gano a arewacin kasar zai kara yawan man da kasar ke hakowa a kullum tare da samar da wurin da za a rika tace shi.











