Man fetur: 'Yan Najeriya na da shakku kan binciken shigo da gurbataccen mai a ƙasar

h

Asalin hoton, Getty Images

Masu ruwa da tsaki a Najeriya sun fara tsokaci ga iƙirarin gwamnatin Najeriya na cewa za ta gudanar da gagarumin bincike kan batun shigar da gurɓataccen man fetur daga ƙetare zuwa cikin ƙasar.

A jiya Laraba rahotanni suka ambato ƙaramin ministan mai, Timipre Sylva na cewa za a yi bincike don bankaɗo dalilin shigar da gurbataccen man a Najeriya.

Masu motoci da yawa ne suka koka a kan lalacewar ababen hawansu, bayan sun sha man feturin mai yawan sinadarin methanol fiye da kima.

Kafofin yaɗa labaran Najeriya sun ambato ƙaramin ministan fetur jim kaɗan bayan taron majalisar zartarwar ƙasar na cewa gwamnati ta tashi haiƙan wajen tunkarar batun gurɓataccen man feturin da ya cika gidajen mai.

Ministan ya kuma nemi 'yan ƙasar su ƙara haƙuri har gwamnati ta kammala bincike kafin a fara batun bayyana sunayen masu hannu.

Rahotanni sun kuma ambato shi yana cewa kafin yanzu babu wanda ke duba adadin methanol a cikin man fetur ɗin da ake shiga da shi ƙasar.

Lamarin da ya sa wasu ke tambayar da ma ƙasar ba ta da sashen tantance ingancin man da ake shigarwa daga waje.

Wannan layi ne

Sakaci

Masu harkar man fetur a ƙasar, kamar Shehu Usman Tanko, ya ce kamata ya yi hukumomi a wannan mataki su janye gurɓataccen man daga kasuwa.

''Idan gwamnati ta so, za ta iya yi wa dukkan man kiranye, ta yadda za a daina saida shi, saboda idan aka ci gaba da saidawa mutane wannan man zai kassara musu ababen hawa.

Alal misali mutum ya sha man nan mara kyau ya dauki hanyar Abuja zuwa Kaduna a tsakiyar daji mota ta tsaya maka, ai duk wani tashin hankali na rayuwa ka gan shi. "

Sannan ya ƙara da cewa gwamnati da ta yi sakacin barin man ya shiga kasuwa, ita ce ya dace a matsayin ta na uwa ta yi wa man kiranye a kuma tsaftace shi.

Daga ina aka shigo da man?

A ranar Talata ne sabuwar Hukumar kula da harkokin Sarrafa man fetur da tacewa da sufuri ta Nijeriya wato "Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory Authority" ta tabbatar da samun gurɓataccen man ɗauke da wani adadin sinadarin methanol da ya zarce abin da ƙasar ta iyakance a kasuwa.

Sai dai, sanarwar hukumar da ta kuma ministan man fetur duka ba wadda ta ambacin sunan kamfani ko masu kamfanin da ya shigo da gurɓataccen man.

Sai dai masu fafutuka a Najeriya, irin su Auwal Musa Rafsanjani sun ce ba su da kwarin gwiwa akan ikirarin na gwamnati kan wannan bincike.

Rafsanjani ya ce babu tabbacin za a hukunta wadanda aka samu da laifin shigo da gurbataccen man, idan da gaske gwamnatin ta ke a kafa kwamitin da ya kunshi kwararru ba wai jami'an gwamnati kadai ba, domin a yi bincike mai inganci.

Sharhi

Abin jira a gani dai shi ne ko wannan bincike zai gudana kuma ya yi wani tasiri, ko kuma zai kasance irin bincike-binciken babarodo da aka saba yi a Najeriya.

A baya-bayan nan an ambato ministar kuɗi Zainab Shamsuna na cewa ƙasar za ta kashe kimanin naira tirliyan talatin a matsayin tallafin man fetur a bana.

A wani mataki na tsaftace harkar man fetur dai, tun farkon mulkinsa, Shugaba Muhammadu Buhari ne da kansa, ke jagorantar sashen a matsayin babban ministan man fetur.

Gwamnoni da 'yan majalisa a bainar jama'a sun fito suna nuna shakku kan maƙudan kuɗaɗen da ake kashewa a matsayin tallafin man fetur.

Wannan na nuna cewa mai yiwuwa ko a hukumance baki bai zo ɗaya ba, saboda yawan rufa-rufa da rashin fayyace komai a faifai da ake zargin sun cika harkar.

Wannan layi ne