Najeriya: Masu abubuwan hawa sun koka kan gurbataccen man fetur

Gurbatccen mai

Asalin hoton, Getty Images

Masu abubuwan hawa a sassan Najeriya da dama sun koka kan yadda aka ringa sayar musu da gurɓataccen man fetur a wasu gidajen man ƙasar.

Jama'a na kukan cewa sun ringa fuskantar matsalar injinan motocinsu jim kaɗan bayan sun sha mai a gidajen mai.

Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da ake fama da karancin man a sassan kasar inda mutane da dama suka ce motocinsu sun sami matsala bayan da suka sha gurbataccen man.

Tuni ƙungiyar dillalan man fetur a kasar IPMAN ta ce ta shigar da korafi game da matsalar inda tace har hukumomi sun bayar da umarnin dakatar da sayar da gurbataccen man.

Wasu da suka sha man sun ce motocinsu sun ringa tsayawa saboda gurbataccen man da suka ringa sha.

Matsalar dai ta fara ne a makon farko na watan Fabrairu.

Wani direba ya ce "Wannan lamarin bai kamata ba, ga wahalar mai ga gurbacewar mai. Akwai man da za ka sha kamar ka sha iska. Za ka ga mai bai yi maka auki ba. Gaskiya muna fuskantar matsala."

Da take mayar da martani, ƙungiyar dillalan man fetur ta Najeriya IPMAN ta ce tana sane da matsalar, kuma ita ma ta yi wa hukumomi korafi sannan har an dauki mataki.

Shugaban kungiyar ta IPMAN a arewacin Najeriya Alhaji Bashir Ahmad Dan-Mallam ya ce matsalar da aka samu ta gurbataccen man fetur din na da alaƙa da wuraren da suke ɗakko man.

Ya ce "an ɗan samu matsala. Amma hukumar NNPC ta tashi tsaye. kuma an dakatar da dakon wannan man tun makon jiya."

"An samu matsala ne daga yadda aka shigo da wannan kayan. Duk motocin da suka dauka an ce su sauke. Wadanda kuma suka fita an ce su mayar," a cewar Dan-Malam.

Dogwayen layuka a gidajen mai

Matsalar ta gurbataccen mai dai tamkar sara ne a kan gaɓa, domin ta zo ne a dai dai lokacin da ake fuskantar ƙarancin mai da dogayen layuka a gidajen mai a Abuja da ma wasu jihohin ƙasar.

Masu abubuwan hawa kan shafe sa'o'i suna jiran samun damar shiga gidajen mai da abubuwan hawansu.

A Legas ma babban birnin kasuwanci na Najeriya, kaɗan daga gidajen man ne suke bayarwa wanda ake samun cunkoson ababan hawa da na mutane.