Gwamnatin Tinubu ta yi watsi da yankin arewa - Kwankwaso

Kwankwaso

Asalin hoton, Kwankwaso/X

Lokacin karatu: Minti 3

Tsohon gwamnan jihar Kano, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya caccaki gwamnatin Bola Tinubu kan abin da ya kira watsi da yankin arewacin Najeriya, inda ya ce shugaban ya fi mayar da hankali kan gina kudancin ƙasar ta hanyar amfani da albarkatun ƙasar.

Kwankwaso ya bayyana haka ne a wajen taron shawarwari na masu ruwa da tsaki a jihar Kano na 2025 - wanda aka gudanar da yammacin Alhamis ɗin nan.

"Bayanai da muka samu na nuna cewa kamar rabin kasafin kuɗi na tafiya zuwa wani ɓangare guda a ƙasar nan," in ji Kwankwaso.

Kwankwaso wanda ya yi wa jam'iyyar NNPP takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, ya zargi jam'iyyar APC da karkatar da albarkatun ƙasa tsakanin ɓangarori biyu na Najeriya.

Ya ce: "Bari in bai wa waɗanda ke ƙoƙarin yin duk mai yiwuwa wajen ɗaukar komai, su tuna cewa wasu batutuwan da muke ciki a ƙasar nan a yau suna da alaƙa da rashin isassun kuɗaɗe da kuma almubazzaranci da wasu ke yi," in ji Kwankwaso.

Ya ce wannan ya sa ake fama da rashin tsaro da talauci da sauransu.

Kwankwaso ya ce yawancin hanyoyi da ke arewacin suna cikin mawuyacin hali, wasu ma sun lalace - a daidai lokacin da gwamnatin APC ke ci gaba da ware maƙudan kuɗaɗe wa ɓangaren ayyukan more rayuwa a kudancin ƙasar.

Ya buƙaci gwamnatin Tinubu da ta sauya alkibla domin tafiya da kowa da kuma tabbatar da cewa an raba albarkatun ƙasa yadda ya kamata domin ci gaban dukkan sassan ƙasar.

"Yanzu lokaci ne da ya kamata gwamnati ta kawo sauyi, domin mu san cewa ba gwamnati ce kaɗai ta wani ɓangare guda ba," in ji shi.

Me kalaman Kwankwaso ke nufi?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kalaman tsohon gwamnan dai na zuwa a daidai lokacin da ake ta hasashen yana gab da komawa jam'iyyar APC mai mulki da ake ta raɗe-raɗin tana zawarcinsa.

Hakan ya sa wasu tunanin cewa ko shugaba Tinubu da jam'iyyar APC ba su kammala daidatawa da Kwankwaso ba inda ake tunanin ka iya ci gaba da zama a jam'iyyar tasa ta NNPP.

Sai dai kuma wasu na yi wa kalaman kallon siyasa kasancewar Kwankwaso ya shawarci gwamnati ne inda ya tunatar da ita dangane da abubuwan da ya kamata ta mayar da hankali domin cin ribar siyasa a yankin mai ɗimbin matsaloli.

Bayanai da hotuna sun nuna yadda tsohon gwamnan na Kano ya karɓi wasu mutane da aka ce ƴan jam'iyyar APC da suka sauya sheƙa zuwa jam'iyyar Kwankwaso ta NNPP.

A baya-bayan nan ne Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce babu dalilin da zai sa ya shiga jam'iyyar da ba ta damu da talakawa ba wato jam'iyyar APC, inda ya bayyana yin hakan da "sabo" irin na siyasa.

Sai dai kuma tun bayan saukar Abdullahi Umar Ganduje daga shugabancin jam'iyyar APC, mabiya Kwankwaso suke ta rubuce-rubuce a kafafen sada zumunta cewa "ƙafarka ƙafarmu jagora", wani abu da masu fashin baƙin siyasa ke kallo da dabarun sauya sheƙa.