Nan ba da jimawa ba za mu tuntuɓi Kwankwaso - PDP

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso

Asalin hoton, OTHERS

Lokacin karatu: Minti 3

Babbar jam'iyyar hamayya a Najeriya, PDP ta ce nan ba da jimawa ba za ta tuntubi tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, domin ya sake komawa jam'iyyar a yi tafiya tare domin ganin bayan jam'iyyar APC mai mulki a kasar.

Mai riƙon muƙamin shugaban jam'iyyar na kasa, Ambasada Umar Iliya Damagun ne ya bayyana haka a hirarsa da BBC, yayin da yake mayar da martani kan kalaman da Kwankwason ya yi na cewa jam'iyyar, PDP ta mutu, kuma ba za ta iya wata nasara ba a nan gaba.

Ya jaddada cewa a yanzu haka a shirye suke su karbi duk wasu 'ya'yansu da suka yi fushi suka tafi wasu jam'iyyu, ciki har da Sanata Kwankwanson.

''Mutum zai iya faden ra'ayinsa, amma ina so in tuna masa baya, a lokacin da suka bar jam'iyyar PDP a 2015, in ba ta mutu ba a wancan lokacin, a 2015, a lokacin da suke ganin sun yi mata illa to ba n ga dalilin da za a ce ta mutu ba yanzu,'' in ji shugaban.

Ya kara da cewa, ''kuma kar ka manta jam'iyyar PDP ita kadai ce ke iya cin zabe idan aka cire masu mulki.''

Damagun ya ce shi kansa Kwankwason da ya ce PDP ta mutu, ai bai yi wa kansa adalci ba, domin ai ya dauki jam'iyya amma jiha nawa ya ci ?

Shugaban na riko ya kuma bugi kirji da cewa jam'iyyarsu ta PDP ita ce har yanzu bayan shekara 26 take amsa sunanta na PDP ba ta sauya ba, kuma take da gwamnoni dasanatoci zababbu a kowane sashe dabangare na Najeriya.

Ya ce yau a Najeriya idan aka cire PDP, aka hada jam'iyyu hudu ba za su iya cin zabe ba.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Dangane da magar na Kwankwason ya yi cewa an ci musu fuska a jam'iyyar ta PDP a baya saboda haka ya kawar da duk wata magana ta hada kai da su domin zaben 2027, Ambasada Damagun ya ce lalle haka ne wasu maganganun na Kwankwaso ya yi gaskiya ne domin shi kansa a lokacin da tsohon gwamnan na Kano yake yunkurin barin jam'iyyar lokacin shi yana matsayin mataimakin shugabanta na kasa shiyyar arewa ya yi iya kokarinsa na sasantawa amma abin ya ci tura.

''Amma dai duk da haka ba shi da jam'iyyar da ta fi PDP domin idan ka duba ita ta rene shi, ita ta kawo masa siyarsa ta kai inda yau ta kai, har gobe ba ma cire tsammani zai iya zuwa a yi tafiya da shi mu karkade jam'iyyarmu mu fuskanci wannan azzalumar gwamnati,'' in ji shugaban.

Shugaban na PDP, ya ce idan Allah Ya yarda nan ba da jimawa ba za su tuntubi, Kwankwason duk cewa ya san a fusace yake, kuma ya san abin da yake so zai yi wuya ya samu a waccan jam'iyyar da yake.

Ya ce jam'iyyarsu ta PDP jam'iyya ce da kodayaushe take karbar duk wani danta da aduk lokacin da ya yi fushi ya tafi idan ya dawo tana karbarsa kuma ta ba shi dama kamar kowa.