Rabi'u Kwankwaso: Tsohon gwamnan Kano ya bar PDP ya koma jam'iyyar NNPP

Kwankwaso

Tsohon gwamnan Jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bar jam'iyyar PDP zuwa ta NNPP.

Sai dai dama tun a farkon watan nan na Maris Sanata Kwankwaso ya shaida wa BBC cewa a lokacin dai yana PDP amma ya soma tattauna wa da jam'iyyar NNPP domin sauya sheka zuwa can.

Amma a ranar Talata 29 ga watan Maris tsohon gwamnan kuma tsohon ministan tsaro a kasar ya tabbatar da ficewarsa daga PDP zuwa sabuwar jam'iyya ta NNPP.

A hirarsa da BBC a farkon watan Maris, jagoran kungiyar siyasa ta Kwankwasiyya ya ce a makwannin da suka gabata ne suka kaddamar da wata sabuwar kungiya mai suna 'The National Movement', bayan nan ne aka samar da jam'iyyar NNPP wato New Nigeria People Party ma'ana dai sabuwar Najeriya.

A wata wasiƙa da ya aika wa shugaban mazaɓarsa, Kwankwaso ya rubuta cewa, "Ina so na fara da miƙa godiyata ga shugaba da dukkan ƴan uwa da abokan arziki na mazaɓata, da ma faɗin Najeriya duka, kan irin kyakkyawar dangantakar da muka yi da su da kuma goyon bayan da suka ba ni a lokacin da nake PDP.

"Na rubuta wannan wasiƙa don shaida maka cewa sakamakon rashin haɗin kai da mabambantan ra'ayoyi da muka kasa warwarewa ya sa na yanke shawarar fita daga PDP, daga ranar Talata 29 ga watan Maris din 2022, na janye zamana a matsayin ɗan jam'iyyar PDP."

Me Kwankwaso ya ce tun kafin ya koma jam'iyyar NNPP?

Kwankwaso Facebook

Asalin hoton, Kwankwaso Facebook

Tun da fari Kwankwaso ya ce, wannan sabuwar jam'iyya ce ta mutanen da suka amince cewa akwai bukatar tsarin da aka taho da shi daga shekarar 1999 a sauya shi a kawo abin da jama'a za su amfana.

Ya ce akwai bukatar nazari kan abin da kasa za ta sauya sannan ta samu sabon alkibla, sai dai yana mai jaddada cewa har yanzu ya na nan a cikin jam'iyyar PDP bai fita daga cikinta ba.

''A yanzu maganar da ake yi ina cikin jam'iyyar PDP, tun wancan lokacin mun fara abin hawa-hawa.

"Abu na farko da muka fara yi shi ne ja baya daga tsarinta, tunanin wasu masu hankali za su zo a zauna a fada musu abin da ya dame mu amma jam'iyya ba ta yi ba, muka shiga kungiya nan ma ba a yi komai ba, to gamu a matakin jam'iyya.