Ko shugaba Tinubu na fifita Yarabawa a rabon muƙamai?

.

Asalin hoton, Tinubu X

Lokacin karatu: Minti 3

A Najeriya ana ci gaba da samun karuwar korafi a tsakanin wasu 'yan kasar da ke zargin shugaba Bola Ahmed Tinubu da nuna fifiko ga 'yan kabilarsa ta Yarabawa a nade-naden muhimman mukaman gwamnati.

Masu sukar wannan salo dai suna zargin 'yan kabilar Yarabawa suna ta kokarin mamaye duk wasu manyan mukamai masu matukar muhimmanci da tasiri a gwamnatance.

Matakin baya-bayan nan da ya sabunta irin wannan tunani, shi ne sauke shugaban kamfanin NNPCL, Malam Mele Kolo Kyari da kuma maye gurbinsa da Injiniya Bashir Bayo Ojulari.

Mutane dai dai ku da kungiyoyi da dama ne dai, musammanwadan da suka futo daga yankin arewacin Najeriyar, na ta bayyana damuwa tare da yin kakkausar suka, game da salon nade-naden mukaman da gwamnatin ta Bola Ahmed Tinubu ke yi, wanda ake zargin tamkar yukunrin cika manufar fifita muradun al'ummar Yarabawa da kokarin yarabantar da al'amuran Najeriya.

Kwamred Jamilu Aliyu Charanci shi ne shugaban kungiyar Gamayyar kungiyoyin arewacin Najeriya, wato CNG, kuma daya daga cikin masu ganin baiken ire-iren wadannan nade-nade, ya ce akwai bukatar shugaban na Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya tuna cewar ba wai iya kabilarsa ta Yarabawa ba ne kadai ba yan Najeriya.

"Kusan dukkan wani banagren da ke da tasiri a gwamnatance gwamantin nan ta baiwa Yarabawa, shugaban hukumar tattara haraji ta FIRS Bayerebe ne, shugaban DSS shi ma Bayerebe ne, ministan Kudin Najeriya Bayerebe ne, in aka ci gaba da tafiya a haka to kuwa za a ci gaba da danka su ga yarabawa, wanda hakan babu abin da zai haifa sai kara raba kansu, sannan kuma ba zata yi musu adalci ba saboda inda suka futo", in ji Kwamard Chiranci.

Haka kuma Ya ce 'babu yadda zaai a ce a Najeriya, babu wanda ke da ilimi illa Yarabawa, su ne kadai za su iya gudanar da wadan anan wurare? idan ma akwai wadan da zai sakawa bai wuce 'yan Arewacin Najeriya ba, don haka abun da ya kamata ya yi, shi ne ya zama shugaba mai hada kan 'yan Najeriya ba wai raba kawunansu ba', a cewar Kwamaret Jamilu Aliyu Chiranci.

Martanin fadar shugaban ƙasa

Sai dai daya daga cikin masu magana da yawun shugaban na Najeriya, Abdulaziz Abdulaziz, ya yi watsi da wadan nan korafe-korafe, yana mai cbayyana shi da mara tushe.

"Idan ka duba akwai mukamai masu mahimmanci sosai da aka baiwa yan arewa, abun da mutanen suke mayar da hankalinsu akai shi a baiwa mutane mukamai su yi bushasa kawai ba wai irin aikin ko mahimmancin da mukamin ke da shi ba", in ji Abduslaziz din.

Har ila yau Abdulaziz Abdulazizi din dai ya ce 'idan ka duba noma da kiwo da bangaren tsaro dukkan su wurare ne masu matukar mahimmanci, wanda kuma dukkansu yan arewacin Najeriya aka baiwa don kula da su, don haka ka ga ai ko ina ana damawa da shi a harkokin da suka shafi ci gaban kasa' in ji shi.

'Yan Najeriya masu yawa ne dai suka zuba idanu don gani a kasa, game da tasirin wadan nan nade-naden mukaman da Shugaba Tinubun ya yi, wajen ingantawa tare da kyutata rayuwar mutanen kasar, tare da ci gabanta a karkashin wannan gwamnati.