Hare-haren siyasa biyar da suka faru a mako ɗaya a Najeriya

Hoton yadda aka lalata wata kofa lokacin da wasu da ake zargin 'yan daba ne suka tarwatsa taron siyasa a Kaduna

Asalin hoton, X/Ahmadkargi

Lokacin karatu: Minti 4

Amfani da ƴandaba ko kuma sara-suka da ake yi a baya-bayan nan domin tarwatsa taron abokan hamayyar siyasa ko kuma ƙaddamarwa wani wanda ake ganin barazana ne a siyasance, ya zama wani abu mai kama da sabon salon hamayya a Najeriya.

Wannan ya sana masu nazarin kimiyyar siyasa da lura da al'amuran yau da kullum ke ganin sabon salon hamayyar ka iya barazana ga zaɓuka masu zuwa a kakar zaɓe mai zuwa ta 2027.

BBC ta yi duba kan wasu lokuta da ƴandaba suka kai wa wani ko kuma wasu hare-hare da sunan hamayyar siyasa.

Katsina

Ƴanbanga

Asalin hoton, Getty Images

Wani gungun matasa ɗauke da makamai ne da ake kyautata zaton ƴandaba ne suka afka wa wani taron masu ruwa da tsaki da aka yi ranar Talata a Katsina kan nemo bakin zaren rikicin ƴanbindiga da ke addabar yankunan jihar ta Katsina.

Bayanai sun nuna cewa maharan sun ƙaddamar wa taron ne jim kaɗan bayan da mutumin da ya haɗa taron, Dr Bashir Kurfi ya fara bayar da bahasi kan matsalar tsaron da jihar ke fuskanta.

Yana tsaka da bayanin nasa ne sai wani mutum ya miƙe yana ƙalubalantar sa, inda yake cewa gwamnati na yin iya ƙoƙarinta wajen ganin ta magance matsalar tsaron.

Mutumin ya bayyana kalaman Dr Kurfi da na "ƙyamar gwamnati" wanda ya ce ba za ta saɓu ba saboda da "ba su haɗa irin wannan taron ba a baya lokacin gwamna Aminu Masari."

Rahotanni sun rawaito cewa mutanen sun yi amfani da kujeru da wuƙaƙe a kan mahalarta taron da ƴanjarida.

Kaduna

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A can Kaduna ma an samu irin wannan yanayin inda wani gungun masu ɗauke da makamai suka fasa taron jam'iyyar haɗaka ta ADC a ƙarshen mako duk kuwa da kasancewar jami'an tsaro a wurin.

Al'amarin dai ya faru ne a otal ɗin NUT Endwell Hotel da ke birnin na Kaduna, inda suka fasa taron ta hanyar jifa da dukan mahalarta taron da duwatsu da kujeru da kuma farfasa gilasan tagogin ginin.

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai tare da mataimakin shugaban jam'iyyar APC na arewa maso yammaci, Jafaru Sani da sauran jiga-jigan ƴan jam'iyyar sun kasance a wurin taron domin ƙaddamar da wani kwamitin riƙon ƙwarya.

Malam El-Rufai a wata hira da ya yi da gidan talbijin na Channels ya yi zargin hannun gwamnantin jihar a al'amarin, inda ya ce babu abin da ƴansandan da ke wurin suka yi lokacin da ƴanbangar ke cin karensu babu babbaka.

Tsohon gwamnan jihar ta Kaduna ya ce zai miƙa takardar koke ga babban sifeton ƴansandan ƙasar da hukumar ƴansanda ta Najeriya.

Kebbi

Sakamakon irin wani hari a jihar Kebbi ranar Litinin an samu musayar yawu tsakanin jam'iyyun APC da na ADC, inda kowacce take zargin ɗayar da amfani da ƴanbanga.

Tsohon ministan shari'a na Najeriya, Abubakar Malami ne dai ya yi zargin cewa ƴanbanga daga jam'iyyar APC sun kai wa ayarin moticnsa hari, a kan hanyarsa ta zuwa birnin Kebbi domin yin ta'aziyya.

To sai dai shugaban jam'iyyar APC a jihar, Abubakar Muhammad Kana Zuru ya yi watsi da zargin, inda ya zargi tsohon ministan da cewa shi ne wanda ya ɗauko hayar ƴandabar daga jihar Sokoto domin su tayar da zaune tsaye a jihar ta Kebbi.

Rahotanni sun nuna cewa ƴanbangar sun yi amfani da adduna da wuƙaƙe da sauran muggan makamai a lokacin harin da ke cike da ƙaddama.

Sai Abubakar Malami ya yi wa magoya bayansa jawabi inda ya nemi ka da su tayar da zaune tsaye amma kuma suna da damar kare kansu.

Jigawa

Can ma a jihar Jigawa a ranar Lahadi an fuskanci irin wannan rikicin, inda wasu gungun matasa suka fasa wani taron da aka shirya a garin Kafin-Hausa domin karrama wani ɗan jam'iyyar APC a jihar tare da bayyana goyon baya ga shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027.

Bayanai sun nuna cewa ana tsaka da taron wanda ya samu halartar sakataren kuɗi na ƙasar, Bashir Gumel, ya samu katsewa ne bayan da wani ɓangare na magoya bayan jam'iyyar suka kutsa cikin wurin taron, abin da ya yi sanadiyyar jikkatar mutane da dama tare da lalata abubuwan hawa.

Rahotanni sun nuna cewa ƴansiyasa masu alaƙa da tsohon gwamnan jihar kuma ministan tsaro, Muhammadu Badaru Abubakar ne ke halarartar taron.

Kogi

A jihar Kogi ma an samu wasu mutane da ake tsammanin ƴandabar siyasa ne sun lalata ofishin jam'iyyar haɗaka ta ADC da ke garin Abejukolo da ke ƙaramar hukumar Omala a jihar Kogi ta arewa maso tsakiyar Najeriya.

Rahotanni dai sun nuna al'amarin ya faru ne a ranar Asabar da daddare, sai dai kuma jami'an tsaro ba su samu sun kama kowa ba kamar yadda mazauna yankin suka shaida.

Jam'iyyar ta ADC ta yi kira ga jami'an tsaro da su binciki al'amarin domin hukunta masu hannu a ciki sannan a tabbatar hakan bai sake faruwa ba.

Illar hare-haren

Daba

Asalin hoton, Police

Malam Kabiru Sufi, masanin kimiyyar siyasa a Kano ya shaida wa BBC cewa hare-haren ba zai haifar wa dimokraɗiyya alkairi ba.

"Wannan na nuni da irin yadda ake samun yawaitar dawowar tashe-tashen hankula a siyasar Najeriya. Sannan kuma abu ne da ake ganin zai iya hana ba wai kawai ƴansiyasa ba har ma da kaɗa ƙuri'a wato hakan zai sa su yi ɗari-ɗari da al'amuran siyasa hatta kaɗa ƙuri'a saboda haka ba ƙaramin yi wa dimokraɗiyya zagon ƙasa ba ne." In ji Malam Kabiru