Wane tasiri keɓe takarar shugaban ƙasa ga kudu da PDP ta yi zai yi a 2027?

Lema mai alamar Kore fari da ja

Asalin hoton, PDP

Lokacin karatu: Minti 3

A farkon makon nan ne babbar jam'iyyar hamayya a Najeriya, wato PDP ta sanar da keɓe wa yankin kudancin ƙasar takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

Matakin da jam'iyyar ta ɗauka ya zo wa wasu ƴan ƙasar da dama da mamaki, kasancewa saura kusan shekara biyu a gudanar da zaɓen 2027.

Jam'iyyar PDP ta faɗa rikici tun gabanin zaɓukan 2023 bayan da tsohon mataimakin shugaban ƙasar, Atiku Aubakar ya samu nasara a zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar.

Lamarin na zuwa ne watanni bayan da jam'iyyar APC mai mulki, ta nuna amincewarta da Shugaba Tinubu - wanda ɗan yankin kudanci ne - domin yi mata takara a 2027.

Batun karɓa-karɓa na da matuƙar muhimmanci da tasiri a siyasar Najeriya, tsakanin yankunan ƙasar biyu, kudu da arewa.

A tsarin siyasar Najeriya duka ɓagarorin biyu na da muhimmanci, kuma dole ne ɗan takara ya samu goyon baya daga duka yankunan ƙasar kafin samun nasara.

Hakan zai farfaɗo da kimar jam'iyyar?

Sau biyu PDP na bai wa yankin arewacin Najeriya takara a zaɓukan shugaban ƙasa a baya-bayan nan, 2019 da 2023.

Jam'iyyar - wadda ke cikin rikici tun 2023 - na fatan wannan mataki zai kawo ƙarshen matsalar da take ciki.

To sai dai Dakta Yakubu Haruna Ja'e, Shugaban sashen nazarin kimiyyar siyasa a Jami'ar jihar Kaduna, ya ce ba lallai jam'iyyar ta cimma manufar tata ba.

Masanin siyasar ya ce matakin na PDP zai sa wasu ƴaƴan jam'iyyar daga arewacin ƙasar, su yi mata zagon-ƙasa, saboda ba lallai ne matakin ya yi musu daɗi ba.

''Za su iya haɗa kai su yi jam'iyyar adawa mai ɗan takara daga arewa a sama, ala ba shi idan aka zo sauran zaɓuka su zaɓi ƴan takararsu'', in ji shi.

''Wannan abu ne da zai bai wa jam'iyyar hamayya damar lashe zaɓen 2027''.

Me hakan ke nufi ga zaɓen 2027?

Dakta Ja'e ya ce matakin PDP zai iya bai wa yankin kudancin Najeriya damar samun shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

Ya ci gaba da cewa hakan na nufin takara za ta fi zafi tsakanin ƴan kudancin Najeriya a 2027.

''Kasancewar ita ma APC mai mulki ta amince Tinubu ya yi mata takara a 2027, ƴan yankin za su iya haɗa kansu domin zaɓen mutum guda'', in ji shi.

Masanin siyasar ya ƙara da cewa wannan mataki da manyan jam'iyyun biyu suka yi, zai iya fusata wasu mambobinsu da ke yankin arewacin ƙasar.

''Hakan zai sa su yi ta raka jam'iyyun, sai aski ya zo gaban goshi, sannan su juya musu baya, su koma wa jam'iyyar da ta tsayar da ɗan arewaci'', in ji shi.

'Dama ce ga jam'iyyar ADC'

To sai dai masanin kimiyar siyasar ya ce a gefe guda kuma hakan wata dama ce ga jam'iyyar ADC mai hamayya.

Ya ce idan har jam'iyyar ta samu damar fitar da muhimmin ɗan takara mai farin jini a arewa to lallai zai iya yin nasara.

''Kasancewar duka manyan jam'iyyun sun tsayar da ɗan takara daga kudu, hakan na nufin ƙuri'un kudu za su rabu gida biyu, kuma dama APC ba ta da wani farin jini har a yankin Yarabawa da Tinubu ya fito''.

''To idan ƴan arewa suka haɗe kai, kuma ADC ta fitar da ɗan takara mai ƙarfi da farin jini zai iya yin nasara, saboda dama yankin arewa ƙuri'un suka fi yawa'', in ji shi.

''Wannan dama ce ga ƴan adawar, idan har suka iya fitar da wani gogaggen ɗan takara, to tabbas zai samu goyon bayan arewa, kuma wataƙila zai iya samun wasu ƙuri'un daga yankin kudu'', in ji shi.

Me dokokin Najeriya suka ce kan karɓa-ƙarba?

Dakta Yakubu Haruna Ja'e ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya bai yi tanadin tsarin karɓa-ƙarba ba.

''Babu inda a kundin tsarin mulkin Najeriya aka ce idan ɗan kudu ya yi mulki ya sauka, ɗan arewa ya yi, kuma hatta su kansu jam'iyyun yawancinsu ba su yi wannan tanadi ba'', in ji Dakta Ja'e.

Masanin kimiyyar siyasar ya ce tsarin karɓa-karɓa da jam'iyyun ke yawan bi a siyasar Najeriya ya saɓa wa tsarin dimokraɗiyya.

''Wannan ba dimokraɗiyya ba ce, kuma ba ya cikin kundin tsarin mulkin ƙasar'', in ji shi.

Ya ce akasari ƴansiyasar ne ke tsara karɓa-karɓar da nufin daɗaɗa wa kansu.