Me shugaban Najeriya ke la'akari da shi wajen yi wa masu laifi afuwa?

Asalin hoton, Nigeria Presidency/Noo Saro-Wiwa
A daidai lokacin da ake ci gaba tafka muhawara kan afuwar da Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi wa wasu ƴan kasar da kotunan ƙasar suka ɗaure bisa aikata laifuka daban-daban, hankali ya fara komawa kan waɗanne matakai ake bi domin zaƙulo waɗanda suka cancanci yafiyar.
A ranar Alhamis na makon jiya ne Tinubu ya amince da yin afuwar ga wasu ƴanƙasar, wanda yake nunawa a hukumance cewa an wanke su daga laifin da suka aikata, wasu kuma an musu sassauci daga hukuncin kisa zuwa ɗaurin rai da rai ko kuma rage musu tsawon ɗaurin.
Tun da farko, shugaban ƙasar ya gabatar da sunayen waɗanda yake son ya yi wa afuwar ne a gaban majalisar magabatan ƙasar, kamar yadda fadarsa ta bayyana cikin wata sanarwar da ta fitar.
Wani kwamiti da shugaban ƙasar ya kafa ne a farkon wannan shekara ya bayar da shawarar afuwar.
Cikin waɗanda suka samu afuwar Tinubu akwai waɗanda suka mutu da waɗanda ke ci gaba da zaman gidan yari da ma waɗanda suka kammala zaman.
Fadar shugaban ƙasa dai ta ce an yi wa mutanen afuwa ne don su koma rayuwa cikin al'umma bayan sun nuna matuƙar nadama.
Wannan ya sa BBC ta yi nazarin hanyoyin da ake bi wajen zabo mutanen da suka aikata laifi domin yi musu afuwa.
Yaya ake yi?

Asalin hoton, Bayo Onanuga/Facebook
Ganin yadda lamarin ya ja hankali musamman bayan fitar da cikakken sunayen waɗanda suka samu afuwar da ma waɗanda suka samu sassauci, Dr Sulaman Usman Santuraki, malami a makarantar zama ƙwararren lauya ta Najeriya da ke Yola a jihar Adamawa, ya ce afuwar wani iko ne da kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba shugaban ƙasa a matakin ƙasa, da kuma gwamnoni a matakin jihohi.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Sashi na 175 na kundin tsarin mulkin Najeriya ne ya ba shugaban ƙasa ikon afuwa ko sassauci ga waɗanda aka ɗaure," in ji malamin shari'ar a Najeriya.
A game da matakan da ake bi wajen zaƙulo waɗanda suka cancanta, ƙwararren lauyan ya ce, "a kundin tsarin mulki, cewa aka yi shugaban ƙasa zai tattara waɗanda yake so ya yi wa afuwar sai ya miƙa su ga majalisar magabata ta ƙasar da dalilansa domin su duba, su ba shi shawara.
“A majalisar akwai tsofaffin shugabannin ƙasa da tsofaffin alƙalan alƙalai da gwamnoni da wasu manyan mutane."
Lauyan ya ce yawanci ana kafa kwamiti ne, sai kwamitin su yi aikin tattara masu laifin da dalilansu, sai su ba shugaban ƙasa shawara.
Sai dai ya ce kamar yadda shugaban ƙasa yake da ikon afuwar, gwamnoni ma suna da ikon aiwatar da yafiyar a jihohinsu.
"A jihohi ne kundin tsarin mulki ya ce majalisa za ta yi doka, inda za ta kafa kwamitin bayar da shawara wato ‘advisory council’. Kwamitin ne gwamna zai miƙa buƙatarsa ta yin afuwar da waɗanda yake so ya yi wa afuwar, sai su duba, su ba shi shawara."
Kowa zai iya neman afuwar?
A game da waɗanda za su iya neman afuwar ta shugaban ƙasa, Dr Santuraki ya ce kowa zai iya nema.
A cewarsa, "ai akwai wasu lokutan da alƙali zai yanke hukunci kamar yadda doka ta buƙata, ya dai yanke hukuncin saboda ya zama dole ya yanke, amma a zahiri sai yake ganin wataƙila akwai wasu abubuwan da suka sa mai laifin bai cancancin hukunci mai tsauri ba, sai ya tura ga kwamitin yana buƙatar su duba yiwuwar afuwar shugaban ƙasa ko sassauci ga mai laifin."
Ya ce kwamitin zai duba, idan ya gamsu sai ya haɗa a cikin waɗanda zai miƙa wa shugaban ƙasa, "shi kuma sai ya miƙa wa majalisar magabatar, idan sun gamsu da dalilan sai shugaban ya yi afuwar ko sasanci."
Ya ƙara da cewa kowa zai iya neman afuwar, "kuma ko a ranar da aka yanke wa mutum hukunci ne zai iya miƙa bukatarsa, kuma shugaban ƙasa zai iya cewa ya masa afuwa bayan ya gabatar a gaban majalisar," in ji shi.
Ko ƴanƙasa na iya neman a soke afuwar?

Asalin hoton, Nigeria Presidency/Noo Saro-Wiwa
A game da irin yadda mutane suke rubuce-rubucen nuna rashin jin daɗi kan afuwar da aka yi wa wasu daga cikin mutane, Barista Santuraki ya ce mutane na da damar ƙorafi, amma a doka, kundin tsarin mulki shugaban ƙasa ne yake da ikon yin afuwar.
"Da yake abu ne na siyasa, idan mutane sun ga abin da suke ganin bai dace ba, za su iya fitowa su bayyan rashin jin daɗinsu. Da yake shugaban ƙasa aiki ya masa yawa, ba dole ba ne ya san komai game da waɗanda aka kawo masa suna neman afuwar. Kwamitin yake ba aikin, kuma su ne suka ba shi shawara."
Sai dai masanin shari'ar ya ce akwai aiki a gaban majalisar magabatan na duba bayanan mutanen sosai domin su ba shugaban ƙasa shawara da ta dace kafin ya ɗauki mataki.
"Ya kamata mambobin majalisar ta magabata su ɗauki lokaci suna duba bayanan mutanen. Kundin tsarin mulki ya ce a miƙa wa majalisar magabata ne saboda an ga irin manyan da ke ciki, kuma ana tunanin ba za su ji tsoron faɗa wa shugaban ƙasa gaskiya ba, ba za su ji tsoron ba shi shawara ba idan sun ga abin da bai dace ba."
Lauyan ya ce su ne ya kamata su duba da kyau su ga dacewar afuwar, "misali a yi afuwar ga wanda aka ɗaure bisa laifin safarar miyagun ƙwayoyi ko masu yi wa tattalin arziki zagon ƙasa, ka ga irin wannan afuwar za ta nuna kamar gwamnati ba ta ɗauki abubuwa da muhimmanci ba. To mutane za su iya magana, idan shugaban ƙasa ya ji, zai iya gyara, amma dai a doka babu abin da za a iya yi, domin shi ɗin ne kaɗai yake da ikon yin afuwar."











