Wane amfani afuwar Tinubu za ta yi wa Herbert Macaulay, Mamman Vatsa da Farouk Lawan?

Asalin hoton, Nigeria Presidency/Noo Saro-Wiwa
Har yanzu ana ci gaba da tsokaci kan afuwar da Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya yi wa wasu fitattun ƴan ƙasar da aka taɓa samu da laifi da kuma wasu fursunoni.
A ranar Alhamis ne shugaban Najeriya Shugaba Tinubu ya amince da yi wa wasu fitattatun ƴanƙasar da suka aikata laifuka afuwa domin yafe musu a hukumance.
Shugaba Tinubu ya gabatar da sunayen waɗanda yake son ya yi wa afuwar ne gaban majalisar magabatan ƙasar a zaman da ta yi domin tatauna batutuwan da suka shafi ƙasar, kamar yadda fadarsa ta bayyana cikin wata sanarwar da ta fitar.
Wani kwamiti da shugaban ƙasar ya kafa ne a farkon wannan shekara ya bayar da shawarar afuwar.
Cikin waɗanda suka samu afuwar Tinubu akwai waɗanda suka mutu da waɗanda ke ci gaba da zaman gidan yari da ma waɗanda suka kammala zaman.
Fadar shugaban ƙasa dai ta ce an yi wa mutanen afuwa ne don su koma rayuwa cikin al'umma bayan sun nuna matuƙar nadama.
A wannan maƙala muhn duba wasu fitattu daga cikin waɗanda aka yi wa afuwar.
Manjo Janar Mammam Vatsa

Asalin hoton, Nigerian Presidency
Mamman Jiya Vatsa babban jami'in soji ne da ya kai matsayin Manjo Janar a rundunar sojin ƙasa ta Najeriya.
Ya kuma riƙe muƙamin ministan Abuja, a tsakanin shekarar 1984 zuwa watan Disamban 1985.
A watan Disamban 1985 ne gwamnatin Najeriya ta zarge shi tare da wasu manyan sojoji tara da haɗa baki wajen cin amanar ƙasar.
Gwamnatin ta gurfanar da su a gaban kotun soji, inda a ƙarshe ta same su da laifukan da aka tuhume su da su, sannan aka yanke musu hukuncin kisa.
A ranar 5 ga watan Maris ɗin 1986 aka zartar masa da hukuncin ta hanyar harbe shi da bindiga.
Baya ga kasancewarsa jami'in soji, Mamman Vatsa mawaƙi ne da ya wallafa rubutattun waƙoƙi na manya da ƙananan yara.
A matsayinsa na ɗaya daga cikin manyan kwamandojin sojin Najeriya a lokacin yaƙin basasar ƙasar, Vatsa ya rubuta maƙaloli masu yawa na abubuwan da suka faru a lokacin yaƙin.
Herbert Macaulay

Asalin hoton, Nigerian Presidency
Cikakken sunansa shi ne Olayinka Herbert Samuel Heelas Badmus Macaulay, an haife shi a watan Nuwamban 1864.
Ɗan gwagwarmaya ne da ya shafe tsawon lokaci yana yaƙin neman ƴancin kan Najeriya daga hannun Turwan mulkin mallka.
Ya yi aiki tare da Dokta Nnamdi Azikiwe, wajen kafa jam'iyyar NCNC, inda har ya zama shugaban jam'iyyar na ƙasa.
Jam'iyyar NCNC ƙarƙashin jagorancin Macaulay ta taka muhimmiyar rawa wajen nema wa Najeriya ƴancin kan daga Turawan Mulkin Mallaka.
A shekarar 1913 Turawan Mulkin Mallaka suka same shi da laifi tare da haramta masa riƙe muƙamin gwamnati.
Duk da cewa Macaulay ya rasu a shekarar 1946, laifin da Turawan mulkin mallakar suka same shi da shi ya ya ci gaba da binsa in ban da yanzu da gwamnatin Najeriya ta yafe masa.
Farouk Lawan

Asalin hoton, Farouk Lawan
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Tsohon ɗanmajalisar Wakilan Najeriya ne mai wakilatar ƙananan hukumomin Bagwai da Shanono daga jihar Kano.
Ya shafe wa'adi huɗu a majalisar wakilan Najeriya, daga shekarar 1999 zuwa 2015.
Lawan ya kasance shugaban kwamitin kuɗi na majalisar wakilan Najeriya, lokacin Aminu Tambuwal na matsalyin kakakin majalisar.
To sai dai an zargi ɗanmajalisar da laifukan da suka shafi cin hanci da rashawa, inda kotu ta same shi da laifin karɓar dubban daloli a wani binciken almundahanar tallafin man fetur a 2012.
Lamarin da ya sa kotun ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekara bakwai kodayake daga baya an mayar da da hukuncin shekara biyar.
Kotun ta ce ta same shi da laifin karɓar dala 500,000 a amtsayin cin hanci daga Femi Otedola domin sanya kamfanin mansa cikin waanda za su ci gajiyar tallafin man fetur.
Wani bidiyo da aka fitar a lokacin ya nuna yadda Otedola ke bai wa Lawan kuɗi, inda har yake sanya wasunsu cikin hularsa.
Bayan kotun tarayya ta same shi da laifi, Lawan ya ɗaukaka ƙara zuwa Kotun ƙoli wadda ita ma ta tabbatar da hukuncin
A watan Oktoban 2024 ne aka sake shi daga gidan yari bayan kamamla shekarun da aka ƙayyade masa.
Barrista Hussaini Umar
Ya kasance fitaccen lauya wanda ya tsaya wa wani tsohon shugaban hukumar kwastam ta Najeriya.
Kotu a Najeriya ta same shi da laifin halasta kuɗin haram sama da naira biliyan ɗaya tare da yi masa ɗaurin shekara bakwai da zaɓin tara.
Ayinla Saadu Alanamu
Tsohon shugaban hukumar gudanarwar kwalejin fasaha ta jihar Kwara ne da ke arewa ta tsakiyar Najeriya.
Kotu ta ɗaure shekara 12 bisa laifin karɓar cin hancin naira miliyan biyar a hannun ɗan kwangila.
Wasu ƴan gwagwarmayar Ogoni tara

Asalin hoton, Noo Saro-Wiwa
Wannan masu rajin kare muhallai ne na yankin Ogoni a jihar Rivers mai arzikin man fetur, waɗanda suka riƙa nuna adawa da ayyukan wasu kamfanonin mai na ƙasashen waje da suka ce yana janyo malalar mai a yankunansu
Sun haɗa da :
- Ken Saro-Wiwa - Wanda shi ne shugabansu
- Saturday Dobee
- Nordu Eawo
- Daniel Gbooko
- Paul Levera
- Felix Nuate
- Baribor Bera
- Barinem Kiobel
- John Kpuine
Gwamnatin Najeriya ta zarge su da kashe wasu shugabannin Ogoni huɗu, inda a ranar 10 ga watan Nuwamban 1995, gwamnatin Najeriya da zartar da hukuncin kisa ta hanyar rataya a kansu a gidan yarin Fatakwal.
Amfani da afuwar za ta yi musu
Sashe na 175 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya bai wa shugaba ƙasa damar yafewa duk wanda ya aikata wani laifi, matsawar majalisar magabata ta amince masa.
To ko me hakan ke nufi ga waɗanda suka samu yafiyar shugaban ƙasar?
Barista Audu Bulama Bukarti Fitaccen lauya a Birtaniya kuma masanin dokokin Najeriya ya ce abin da hakan ke nufi shi ne daga yanzu mutanen da aka yafewar sun fita daga jerin waɗanda suka yi laifi.
''Daga yanzu babu wanda zai ƙara kallonsu da wannan tabon na cewa an taɓa kama su da laifi har ma aka yanke musu hukunci'', in ji lauyan.
Shi ma Barista Sani Bala Wada'u wani lauya mai zaman kansa a Kano ya ce daga yanzu babu wanda zai taɓa kallonsu a matsayin waɗanda suka taba aikata laifi.
Dangane da waɗanda suka mutun kuwa Barista Bukarti ya ce a doka ba wanda zai ƙara kallon iyalansu da cewa sun aikata laifi ba.
''Kuma idan a lokacin shari'ar an taɓa kwace kadarorinsu ko sun biya tara, to da wannan yafiya za a maido musu da kadorori ko tarar da aka sanya musu'', in ji shi.
Barista Sani Wada'u ya ƙara da cewa ''daga yanzu babu wanda zai kalli iyalansu da laifin da aka kama su da shi a baya, an goge duka laifukan, idan ma suna jin kunyar hakan, yanzu wannan ta kau'', in ji shi.
Ga waɗanda ke raye kuwa akwai sashen dokar da ya yi tanadin cewa wanda aka kama da laifi da ya shafi zamba ko sata ba zai ƙara riƙe muƙamin siyasa ba har na tsawon shekara 10.
Dokta Bukarti ya ce ''akwai sassan dokokin da suka yi tanadin cewa wannan mutumin ko daraktan kamfani ba zai riƙe ba, sanna ba zai iya kafa ƙungiyar NGO ba, ko kuma ba za a ɗauke shi aikin gwmanati ba''.
Ƙwararren lauyan ya ce amma da wannan yafiya a yanzu duka waɗannan shingaye sun kau.
''A yanzu idan suna so za su iya tsayawa takara, ko a naɗa su domin riƙe wani muƙami, ko kuma su kafa ƙungiyar NGO, duk za su iya babu laifi'', in Dokta Bukarti.
Barista Wada'u ya ƙara da cewa, "A yanzu kamar Farouk Lawan ko gobe zai iya tsayawa takara idan ya ga dama''.











