'Akwai son zuciya a afuwar da shugaba Buhari ya yi wa fitattun fursunoni 'yan siyasa a Najeriya'

Najeriya

Asalin hoton, BBC Igbo

Bayanan hoto, Daga hagu zuwa dama: Joshua Dariye, da Diepreye Alamieyeseigha, da Jolly Nyame

Afuwar da gwamnatin shuugaba Muhammadu Buhari ta yi wa wasu fursunonin 'yan siyasa na cigaba da jan hankali a Najeriya, yayinda masu fafutika ke ganin akwai son zuciya a ciki.

Tun a ranar Alhamis majalisar koli karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ta sanar da matakin yiwa wasu fitattun 'yan siyasa da ke kurkuku afuwa kan laifin Rashawa.

Duk da cewa gwamnati a hukumance ba ta fitar da sunaye dukkanin mutanen da ta yi wa afuwa ba, akwai bayanan da ke nuna cewa cikin wadanda aka yi wa afuwa akwai tsohon gwamnan jihar Filato Joshua Dariye da tsohon gwamnan Taraba Jolly Nyame.

Tsofaffin gwamnonin sun kasance cikin mutum 159 da majalisar kolin ta yiwa afuwa wanda aka yankewa hukuncin dauri a gidan yari kan cin hanci da rashawa.

Sannan rahotanni na kuma cewa majalisar ta kuma yi wa wani tsohon sojan nan wanda ya rike mukamin ministan a gwamnatin marigayi Sani Abacha wato Tajudeen Olanrewaju afuwa.

A cewar wata majiya a fadar shugaban kasa, an yi wa tsoffin gwamnonin biyu afuwa ne bisa dalilai na rashin lafiyar da suke fama da ita da kuma shekaru.

Mista Nyame, mai shekaru 66, wanda ya rike mukamin gwamnan jihar Taraba daga shekarar 1999 zuwa 2007, yana zaman gidan yari na shekaru 12 a gidan yarin Kuje bisa samunsa da laifin karkatar da kudade a lokacin da yake kan mulki.

Kotun koli ta amince da hukuncin da aka yanke masa a watan Fabarairun 2020.

Mista Dariye mai shekaru 64, wanda ya mulki Filato a tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007, an daure shi ne bisa laifin satar Naira biliyan 2 na dukiyar al'umma a lokacin da yake gwamnan jihar Filato tsakanin 1999 zuwa 2007.

Tuni kungiyoyin Kungiyoyi masu rajin kare hakkin dan adam a Najeriya suka fara tsokaci kan afuwar da gwamantin shugaba Muhammadu Buhari ta yi wa wasu mutane da ake tsare da su a gidajen yarin kasar kan laifin cin hanci da rashawa.

Auwal Musa Rafsanjani wanda shi ne shugaban kungiyar CISLAC, mai fafutukar ganin an kawar da rashawa da cin hanci a Najeriya, ya ce wannan afuwar cike take da son zuciya.

Ya kuma ce matakin da gwamnatin Buhari ta dauka bai ba su mamaki saboda .

"Ganin yadda gwamnatin Buhari ta dauki yaki da cin hancin da rashawa da wasa saboda maimakon a tabbatar da cewa cin hanci da rashawa an fatattake shi amma sai ana ta kawo wasu hanyoyi da za a ba wasu damar yin abin da suke so su yi, wato su rika cin karensu babu babaka a Najeriya."

Masanin ya kuma yi ikirarin cewa matakin da gwamantin Buhari ta dauka nada nasaba da siyasa musaman yanzu da zaben shekarar 2023 ke karo matsowa kusa kuma tsoffafin gwamnonin biyu na da karfin fada a ji a harkar siyasar jihohinsu.

"Kowa ya riga ya gane cewa wadannan hujoji ne kawai da ake son ayi amfani da su domin cimma manufar siyasa a Najeriya dangane da zaben da za a yi nan da shekara guda. Suna bukatar wadannan mutane don su ci zabe a jihohinsu saboda da haka wannan yafiya baa yi ta ba a kan gaskiyar batun cewa shekarunsu ya haura ba ko kuma ba su a isashen lafiya"a cewarsa.

Auwal Rafsanjani ya ce rikon sakainar kashi da ake yi batun cin hancin da rashawa a Najeriya na cikin abubuwan da suka haifar da rashin tsaro da talauci a kasar.

Mai fafutikar ya ce ya kamata gwamnatin ta tashi tsaye don shawo kan matsalolin.