Cin hanci da rashawa: Mawaƙan waƙoƙin Ingausa sun yi waka kan "Kwarafshan"

Bangon Littafin Kwarafshan da mawakan turanci da hausa suka rubuta

Marubuta wakokin Hausa da na Turanci a Najeriya sun koka dangane da yadda cin hancin da rashawa ya addabi ƙasar.

Marubutan dai na wannan koke ne cikin wasu waƙoki da suka gwama Hausa da turanci da suka rubuta aka kuma tattatara su cikin wani littafi da suka yi wa lakabi da 'Kwarafshan'.

Taron wanda ya sami halartar malaman jami'o'I da banagren yaki da cin hancin da rashawa a Najeriya, da Matasa, ya mayar da hankali kan yadda za a yi amfani wakar Ingausa wajen jan hankalin matasan kasar wajen yaki da cin hanci da rashwa.

Shugaban ƙungiyar marubuta waƙokin Hausa da na turanci a Kano Khalid Imam ne ya jagoranci taron, ya kuma ce shi ne karon farko da aka tattara wakokin wuri guda.

''Mun yi wannan littafi da aka sanya wa suna Kwarafshan, domin mu faɗakar da jama'a illolin da cin hanci da rashawa suke da su, kuma fatanmu a karshen taron shi ne jama'a su san cewa maganar yaki da cin hanci da rashawa ba nauyin gwamnati ne kadai ba, alhakin kawo gyaran ya rataya a wuyan al'umma. Ni da kai, da ke da ku duka mu na da rawar da za mu taka domin ganin mun yaki cin ha nci da rashawar,'' in ji Imam.

Farfesa Uba Abdallah, Farfesa Sadik Isa Radda da mawaki Aminu Ladan Ala na daga cikin wadanda suka halarci taron

Wasu daga cikin jagororin taron irinsu farfesa Sadik Isa Radda, shugaban kwamitin gwamnatin Najeriya wajen yaki da cin hanci da rashawa a kasar, na da ra'ayin cewar amfani da wakokin ingausa wajen yakar cin hanci da rashawa zai yi tasiri wajen cusawa irin wadannan matasa akidar kaucewa munanan dabi'un da ka iya janyo aikata rashawa.

Radda ya kara da cewa gwagwarmayar da gwamnati ke yi don yaki da rashawa ya samu karbuwa ga matasa, shi ya sa sakon da gwamnati ke aika wa ke zuwa kunnensu, kuma a yanzu sun maida lamarin mai muhimmanci ta hanyar sanya shi cikin wake, da rubuce-rubuce domin fadakarwa.

''Abin farin ciki a nan shi ne, wadanda sukai wadannan wakoki matasa na tsakanin shekara 20 zuwa 25, hakan na nufin tun yanzu za su fara kyamatar abin, sannan za su yada kyamar abin ga sauran al'umma ta hanyar amfani da baiwar da Allah ya yi musu,'' in ji Radda.

Suma wasu daga cikin matasan da suka gabatar da wakoki a kan cin hanci da rashawar sun bayyana cewa za su yi duk kokarin domin ganin sakon ya isa ga wadanda aka yi dominsu, wato matasa 'yan uwansu.

Mata mahalarta taron kaddamar da littafin Kwarafshan

Najeriya dai na daga cikin kasashen da ke fama da matsalar cin hanci da rashawa, sai dai duk da matakan da gwamnatocin kasar ke dauka domin ganin an magance wannan matsala, har yanzu al'ummar kasar na kokawa.

Sannan ana zargin matsalar ta yi kamari tsakanin manyan jami'an gwamnati, da ma'aikatu da sauransu.

Mahalarta taron littfain wakokin ingausa mai suna Kwarafshan