Abubuwa uku game da sabuwar hukumar yaƙi da rashawa a Najeriya

Asalin hoton, @Malami
Majalisar zartawar Najeriya ta amince da kafa wata sabuwar hukumar yaƙi da rashawa baya ga hukumomin EFCC da kuma ICPC da ke yaƙi da rashawa a ƙasar.
Ministan Shari'a Abubakar Malami wanda ya sanar da matakin bayan kammala taron majalisar ministoci a ranar Laraba, ya ce aikin sabuwar hukumar ta yaki da rashawa ya shafi kula da kuma daidaita dukkanin ƙadarorin da aka kwato a cikin gida da kuma ƙasashen waje bayan gudanar da bincike.
Ministan ya ce kafa sabuwar hukumar ya zama wajibi domin ƙarfafa nasarorin da gwamnati ta samu a yaki da rashawa a Najeriya.
Hukumar EFCC da ke yaƙi da rashawa a Najeriya ita ke da alhakin kula da ƙadarorin da aka gano ko aka kwato, amma ita ma ta fuskanci zargin karkatar da wasu kuɗaɗen wanda har ya kai ga dakatar da shugabanta na riƙo Ibrahim Magu.
Sunan sabuwar hukumar
Ministan shari'a ya ce sunan ƙudirin da majalisar zartarwa ta amince shi ne Hukumar ƙula da Ƙadarorin da aka sace, wato 'Proceeds of Crime Recovery and Management Agency.'
Kuma wannan ƙudirin ne aka gabatar wa majalisar dokoki domin ta amince domin kafuwar hukumar.
Malami ya ce da zarar majalisa ta amince da ƙudirin ya zama doka, hukumar, za ta duba yadda ya kamata a kula da kadarorin da aka kwaro tare da tabbatar da gaskiya da amana.
Aikin Hukumar
Aikin hukumar ya shafi tattara dukkanin ƙadarori a hukumomin gwamnati daban-daban da aka kwato. kuma a cewar ministan shari'a samun kyakkyawan tsari zai ƙarfafa gwuiwar ƙasashen duniya domin bayar da goyon baya ga kwato ƙadarorin da aka sace.
Sannan hukumar za ta dinga yi wa ma'aikatar kuɗi bayani dalla-dalla na kasafin kuɗaden da aka ƙwato.
Ya ce babbar manufar kafa sabuwar hukumar shi ne tabbatar da gaskiya da amana kan kadarorin da aka ƙwato.
Dalilin kafa hukumar
Gwamnatin Najeriya ta ce galibi kuɗaɗen da aka ƙwato suna hannun hukumomin gwamnati daban daban da suka haɗa da ƴan sanda da DSS da EFCC da kuma ICPC.
Kuma wannan tsarin na wuccin gadi ne, domin babu wata hukuma da aka ɗaura wa nauyin tattara bayanai game da ƙadarorin a hannun hukumomin na gwamnati.
"Akwai buƙatar wata hukuma da za ta iya ba da cikakken bayani kan yawan adadin kadarorin da aka kwato, da suka haɗa da tsabar kuɗi da gwamnati ta gano da aka sace." inji Malami.
Ya ce haƙƙin hukumar ne ta bayar da bayanai ga ma'aikatar kuɗi da kasafi da tsare-tsare musamman kan yawan kuɗaɗen da ta tara domin amfani da su a kasafin kuɗi.











