Muhammadu Buhari: Sabbin alkawuran da shugaban Najeriya ya dauka

Buhari

Asalin hoton, Buhari Sallau

Shugaba Muhammaud Buhari ya zayyana wasu abubuwa guda tara da ya ce zai mayar da hankali cikin shekaru ukun da suka rage masa domin inganta rayuwar 'yan Najeriya.

A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Femi Adeshina ya wallafa a shafinsa na Facebook, Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a lokacin da yake karbar sabbin jakadun wasu kasashe zuwa Najeriya.

Shugaba Buhari ya shaida wa jakadun cewa "a kokarinmu na ganin mun inganta tsare-tsarenmu na cikin gida da waje da kuma samar da ci gaba a Najeriya mun fahimci dole ne mu aiwatar da wasu abubuwa guda tara da ya kamata mu bai wa fifiko a 'yan shekarun da suka rage mana."

Abubuwa tara da Buhari ya alkawarta

  • Gina tattalin arziki mai dorewa
  • Bai wa jama'a dama da yaye talauci
  • Inganta sha'anin noma domin samar da abinci har ma a rinka fitar da shi
  • Samar da wutar lantarki tsayayya
  • Samar da ingantaccen sufuri
  • Inganta sana'o'i da masana'antu
  • Samar da ilimi mai nagarta
  • Samar da ingantacciyar lafiya ga 'yan kasa a farashi mai rahusa
  • Fito da hanyoyin yaki da rashawa da cin hanci da kuma inganta harkar tsaro

To sai dai shugaba Buhari ya bayyana cewa abubuwan guda tara da ya lissafa suna kunshe a cikin "Kundin habaka tattalin arziki da dawo da martabarsa na Najeriya" da gwamnatinsa ta fito da shi domin inganta rayuwar 'yan kasar.

Dama dai kusan dukkan sabbin alkawuran na kunshe a cikin abubuwa uku da shugaba Buhari ya sha alwashin yi a lokacin yakin neman zabensa na 2015 da 2019.

Buhari ya yi alkawarin ganin ya samar da tsaro da yakar rashawa da cin hanci da kuma kyautata sha'anin noma domin samar da wadataccen abinci.

'Yan Najeriya da dama dai na ta faman yanke kauna kan cika alkawuran da gwamnatin shugaba Buharin ta sha yi musu.

Yanzu dai abin jira a gani shi ne ko wadannan sabbin alkawura da Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa za ta mayar da hankali a kai za su tabbata a shekaru ukun da suka ragewa gwamnatin.

Wannan alwashi dai na zuwa ne kwanaki biyu bayan ta bayyana cewa tattalin arzikin Najeriya ya samu komada da kaso 6.1.

Hukumar kididdigar kasar ce dai ta NBS ta fitar da wannan alkaluma a ranar Litinin inda ta ce wannan ne lokacin da kasar ta samu komada mafi girma a tsawon fiye da shekaru 10.

Shugaba Buhari ya bayyana sabbin jakadun wasu kasashe a Najeriya

Asalin hoton, Bashir Ahmed/twitter