Lai Mohammed: Gwamnatin Buhari ta ƙwato naira biliyan 800

Lai Mohammed

Asalin hoton, Getty Images

Gwamnatin Najeriya ta ce ta kwato fiye da naira biliyan 800 tare da gurfanar da fiye da mutum fiye da 1,400 a gaban kuliya a yakin da take yi da cin hanci da rashawa.

Ministan yada labaran kasar, Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana hakan a taron manema labarai a ranar Talata.

Ministan ya ce gwamnatin Shugaba Buhari ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen gannin ta murkushe ayyukan masu cin hanci da karbar rashawa.

Lai ya ce: "Wannan gwamnatin za ta ci gaba da yaki da rashawa fiye da kowanne lokaci, kuma muna da alkaluman da suka tabbatar da hakan."

"Wannan gwamnatin ta gurfanar da mutum fiye da 1,400 gaban kuliya ciki har da manyan mutane sannan ta kwato fiye da naira biliyan 800, ga kuma wasu attajirai da suka mika dukiyarsu," in ji ministan.

'Ba za a fasa ɗaure duk wanda aka kama da cin hanci ba'

A kwanakin baya Shugaba Buhari ya ce har yanzu yana kan bakansa cewa duk wanda aka kama da laifin cin hanci sai ya sha dauri.

Mai magana da yawun shugaban kasar, Femi Adesina, ya ambato Shugaba Buhari yana bayyana haka a sakon da ya fitar na cikar shekara biyar tun da ya soma mulkin kasar.

Muhammdu Buhari

Asalin hoton, @buharisallau

Bayanan hoto, A maye gurbinsu sannan a yi musu horo mai tsanani nan take, inji Buhari

"A game da yaki da cin hanci, babu wani shafaffe da mai. Idan ya aikata laifi, za ka yi zaman gidan yari. Babu gudu, babu ja da baya," a cewar shugaban kasar.

Sai dai wasu 'yan kasar na nna shakku kan matakan da ake dauka wajen yaki da cin hanci, musamman yadda ake zargin an bar wasu da ake zargi rashin hukunta wasu da suka sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulkin kasar.

Amma gwamnatin kasar ta sha cewa babu wani shafaffe da mai, tana mai bayar da misali da yadda aka daure wasu manyan 'ya'yan jam'iyyar ta APC.

'Dakatar da shugaban EFCC Ibrahim Magu'

A farkon wannan watan ne gwamnatin Najeriya ta ce ta dakatar da shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC, Ibrahim Magu, kan wasu manyan zarge-zarge da kuma saɓanin alƙaluma cikin harkokin hukumar.

Ibrahim Magu

Asalin hoton, EFCC/Twitter

Ta ce daga cikinsu, dakataccen shugaban ya yi iƙirarin ƙwato kuɗi kimanin dalar Amurka biliyan arba'in da shida amma sai aka taras da biliyan talatin da bakwai a banki. "To, ina biliyan takwas".

Mai magana da yawun shugaban Najeriya Malam Garba Shehu ya bayyana "kamar yadda na ce zargi ne, mai yiwuwa ko iya lissafin ne ba a yi ba".