Matakan da muke ɗauka kan kisan matafiya a Plateau - Mutfwang

Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Filato a Nijeriya ya ce gwamnatinsa ta na aiki tare da mahukunta a jihar Kaduna domin sanin abin da za su yi wa dangin matafiyan da aka kashe kwanan baya a jiharsa, waɗanda ƴan asalin Zaria ne.
Gwamnan ya kuma ce rikice-rikice masu nasaba da rashin yardar da ke tsananin mabiya addinai da ƙabilu daban-daban, wanda kuma a wasu lokuta kan ritsa da matafiyan da ba su ji ba, ba su gani ba, ba lallai ne a iya kawo ƙarshensu cikin ɗan lokaci ba.
A hirarsa da BBC, gwamna Mutfwang ya ce sun ɗauki matakan da suka dace a game da kisan mutanen, musamman domin ganin an yi wa iyalan waɗanda aka kashen adalci.
Daga cikin matakan ''Mun haɗa tawaga ta musamman ranar Lahadin da ta wuce a ƙarƙashin shugabancin mai martaba sarkin Wase, zuwa jaje wa shi sarkin Zaria, sun je kuma sun dawo lafiya.''
Ya ƙara da cewa sun yi jinkirin zuwa jajen ne saboda gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya nemi a bayar da lokaci domin a tabatar da cewa babu wani rikici da ya biyo baya.
''Abin da ake ciki yanzu shi ne mutane wajen 22 suna tsare, kuma waɗanda suka ji rauni mun tabbatar da cewa sun koma gida lafiya.
''Kuma muna nan dai muna hulɗa da su shugabannin Zaria domin su bamu shawara yadda za a yi a taimaka wa iyalan da suka yi rashi da wanda kuma ba su da lafiya.'' in ji gwamna Mutfwang.
A ranar Asabar 21 ga watan Yunin 2025 ne aka samu labarin kashe aƙalla ƴan ɗaurin aure 12 , daga baya suka koma 13 a ƙaramar hukumar Mangu ta jihar Filato a hanyarsu ta zuwa ɗaurin auren ɗan'uwansu, sannan kuma an jikkata wasu mutum 11 a lamarin wanda aka yi a ranar Juma'a.
Bayanai sun nuna cewa mutum 31 ne a cikin motar wadda ta taso daga Zaria a jihar Kaduna, ciki har da mata da ƙananan yara kuma suna tafiya ne a motar bas mallakin Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria.
Gwamna Muftwang ya kuma yi bayani a kan rikice-rikicen da jihar Filato ke yawan fama da su, inda ya ce tashe-tashen hankulan jihar na da alaƙa da gazawar hukumomi wajen hukunta masu haddasa rikicin da ya-ƙi-ci-ya-ƙi-cinyewa.
Muftwang ya ce dole shugabanni su faɗa wa junansu gaskiya dangane da matsalolin da ke tsakanin al'umma.
Ya bayyana takaici a kan yadda gwamnatocin baya suka sha kafa kwamitoci masu gudanar da bincike da nufin magance matsalar tsaron jihar, ammm har yanzu haƙa ba ta cimma ruwa ba.
''Rashin hukunta waɗanda aka samu da laifi ne ke ƙara assasa rikicin da ake yawan samu a jihar Filato'', in ji shi.
Mista Muftwang ya ce gwamnatinsa ta kafa nata kwamitin wanda zai yi bincike na musamman a kan rikicin jihar Filato, kuma ya sha alwashin cewa a wannan karon, gwamnatin za ta tabbata an hukunta duk masu hannu a rikicin.












