Sakacin gwamnati ne idan ba a daina kashe mutane a Filato ba – Uba Sani

Gwamna Uba Sani na Kaduna

Asalin hoton, @ubasanius

Lokacin karatu: Minti 2

Gwamnatin jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ce za ta tabbatar da bin haƙƙin mutanen jiharta matafiya da aka kashe a jihar Filato a ranar Asabar.

Mutum 12 aka kashe ƴan asalin jihar Kaduna a ƙaramar hukumar Mangu ta jihar Filato yayin da suke kan hanyar zuwa ɗaurin auren ɗan'uwansu cikin motar bas mallakin Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria.

Gwamnatin Kaduna ta ce mutum 16 ke kwance a asibiti da aka jikkata a harin na Mangu daga cikin mutum 31 da ke cikin motar matafiyan.

Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani wanda ya yi allawadai da kisan ya shaida wa BBC cewa ya zanta da takwaransa na jihar Filato gwamna Celeb Mutfwang cewa ba za su bari rayukansu su tafi a banza ba.

"Na kira gwamnan Filato kuma na nuna masa rashin jin daɗinmu kan wannan hali da aka yi na rashin hankali kuma ba za mu bari ya tafi a haka ba," in ji Gwamna Uba Sani.

Gwamnan ya kuma ce ya tattauna da shugaba Bola Ahmed Tinubu game da al'amarin da kuma babban hafsan tsaron Najeriyar Janar Christopher Musa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan sha'anin tsaro Malam Nuhu Ribadu.

Ya ce irin yadda ake kashe mutane a jihar Filato ba za a bari ba idan har gwamnati ba ta ɗauki mataki ba.

A cewar gwamnan, babu wani dalili da mutanen da ba su ji ba su gani ba suna kan hanya a tare su a kashe.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Na faɗa wa gwamnan Filato cewa dole ne a ɗauki mataki domin ba za a mayar da jiha ba ta koma ta kashe mutane kawai."

"Na faɗa wa gwamnan cewa abin da ake yi a Filato dole a bari, idan kuma ba a bari ba to laifin gwamna ne," in ji shi.

Sai dai gwamna Uba Sani ya ce, gwamnan Filato ya tabbatar masa da cewa an kama mutum 22 da ake zargi suna da hannu a kisan matafiyan na jihar Kaduna a Mangu.

Amma gwamnan na Kaduna ya ce duk da an kama su dole a faɗaɗa bincike domin gano sauran mutanen da ke da hannu da aikata kisan a kuma hukunta su.

"Na faɗa wa shugaban ƙasa cewa zan bi diddigi a matsayina na gwamnan jihar Kaduna domin tabbatar da cewa an ɗauki mataki daidai da laifin da suka yi na kisa," in ji Gwamna Uba Sani.

Gwamnan ya ce zai tsaya tsayin daka domin tabbatar da an kawo karshen matsalar kashe-kashe a jihar ta Filato.

Tuni shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi allawadai da harin na Filato, jihar da ta daɗe tana fama da rikicin na ƙabilanci da addini da kuma na makiyaya da manoma.