Lokuta huɗu da aka yi wa matafiya kisan gilla a Filato

Janar Alƙali

Asalin hoton, Twitter/@HQNigerianArmy

Lokacin karatu: Minti 5

Har yanzu ƴan Najeriya na cigaba da alhinin kisan da aka yi wa wasu matafiya da suka tashi daga Kaduna zuwa jihar Filato domin halartar ɗaurin aure.

Hukumomi sun ce kimanin mutum 13 ne aka kashe bayan an tare motarsu ƙirar bas mallakin Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria.

Tuni shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya fitar da wata sanarwa yana nuna takaici kan faruwar lamarin tare da umurtar jami'an tsaro su zaƙulo tare da hukunta waɗanda suka aikata hakan.

Shi ma gwaman jihar Kaduna Uba Sani, a wata tattaunawa da BBC ya ce "wajibi ne sai an hukunta waɗanda suka kashe matafiyan".

Sai dai wannan ba shi ne lokaci na farko ko na biyu da aka taɓa samun irin wannan kashe-kashe ba na matafiya a jihar ta Filato mai fama da rashin tsaro.

Faɗa tsakanin al'ummar yankin ta sanya akai-akai wasu ƙalibun jihar Filato na sauke fushinsu kan masu tafiya kan titin da ya ratsa ta jihar ya haɗa da jihohi masu maƙwaftaka.

Ita dai Filato jiha ce da ta dade tana fama da rikice-rikice mai alaka da ƙabilanci da addini da kuma fafutika game da filayen noma da na kiwo.

Har ta kai cewa a shekara ta 2004 tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar a lokacin da lamurra suka rincaɓe, abin da ya kai ga dakatar da zaɓaɓɓen gwamnan jihar na wancan lokaci, Joshua Dariye.

BBC ta yi waiwaiye, domin kawo muku wasu daga cikin kashe-kashen gilla da aka taɓa yi wa matafiya a jihar ta Filato waɗanda suka tayar da hankalin al'ummar ƙasar.

Kashe almajiran Sheikh Dahiru Bauchi su 30

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A watan Agusta na shekarar 2021 an tare wasu matafiya da suka tashi daga jihar Bauchi zuwa jihar Ondo bayan halartar taron bikin sabuwar shekarar Musulunci a gidan Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi, a garin Bauchi.

Bayanai sun nuna cewa a lokacin an kashe aƙalla mutum 30 daga cikinsu, tare da jikkata wasu da dama.

Lamarin ya auku ne a lokacin da wasu mahara suka tare motocin matafiyan a yankin Rukuba da ke Jos, inda suka hau su da duka da sara, har suka kashe su, sannan wasu suka tsira da raunuka.

A lokacin da lamarin ya faru, rundunar ƴansandan jihar ta tabbatar da mutuwar aƙalla mutum 22.

Sai dai wani ɗanjarida da ya ziyarci asibitin yankin bayan faruwar lamarin ya faɗa wa BBC cewa ya ga gawar mutum 30, sannan wasu sun jikkata, kuma akasarin mutanen na ɗauke da sara na adduna da sauran makamai a jikinsu.

Gwamnan jihar Filato na wancan lokacin, Simon Bako Lalong ya yi Allah-wadai da harin sannan ya yi gargaɗin cewa "masu tayar da fitina su guji yin hakan" saboda "gwamnati ba za ta lamunci tayar da hankali ba".

Janar Idris Alƙali

A ranar 30 ga Satumban shekarar 2018 ne rundunar sojin Najeriya ta sanar da ɓacewar Janar Idris Alƙali mai ritaya a hanyarsa ta zuwa Bauchi daga Abuja, sannan daga bisani rundunar sojin ta sanar da cewa ta gano gawarsa a garin Dura-Du da ke ƙaramar hukumar Jos ta Kudu.

An fara gano motarsa ne tare da wasu motoci ciki har da wata ƙirar bas a wani kududdufi da ke Lafendeg a yankin Du na ƙaramar hukumar Jos Ta Kudu, inda ake zargin ana kashe matafiya ana jefa motocinsu a ciki, domin su ɓace ba tare da samun labari ba.

Daga baya an gano gawarsa a wani rami a yankin, inda aka binne shi bayan kashe, lamarin da ya ɗaga hankali.

Babban hafsan sojin ƙasan Najeriya na wancan lokacin Laftanal Janar Tukur Buratai ya ɗauki alwashin ganin an kama tare da hukunta waɗanda suka aikata kisan.

Sai dai duk da an kama wasu mutane da dama da suke da hannu a kisan, har yanzu dai batun kashe janar ɗin yana kotu.

Kashe Kanawa huɗu

Haka kuma a ranar 6 ga watan Fabrailun shekarar 2022, an tare wasu matafiya da suka taso daga jihar Kano a hanyarsu ta tafiya jihar Nasarawa, inda aka kashe huɗu daga cikinsu.

Lamarin ya auku ne a yankin Bida Bidi da ke ƙaramar hukumar Jos ta Arewa bayan wasu mahara sun tare babbar hanyar Zaria, inda suka musu kisan gilla, sannan suka ƙona motar.

Bayan waɗanda aka kashe, wasu da dama sun jikkata, inda suka yi jinya a asibitin Bingham da ke Jos.

Kakakin rundunar ƴansandan jihar Filato na lokacin, ASP Uba Gabriel ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce za su nemo tare da kama waɗanda suka aikata laifin.

Ƴan ɗaurin daga Zaria

A ranar Asabar 21 ga watan Yunin 2025 ne aka samu labarin kashe aƙalla ƴan ɗaurin aure 12 - daga baya suka koma 13 - a ƙaramar hukumar Mangu ta jihar Filato a hanyarsu ta zuwa ɗaurin auren ɗan'uwansu, sannan kuma an jikkata wasu mutum 11 a lamarin wanda aka yi a ranar Juma'a.

Bayanai sun nuna cewa mutum 31 a cikin motar wadda ta taso daga Zaria a jihar Kaduna, ciki har da mata da ƙananan yara kuma suna tafiya ne a motar bas mallakin Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria.

Ɗaya daga cikin waɗanda suka tsira, Ibrahim Umar ya ce, "mun je auren ɗan'uwanmu ne, sai muka ɓace hanya. Da muka tsaya domin mu yi tambaya, kawai sai suka mana ƙawanya suka fara cewa a kashe mu. Nan suka fara kashe direban, sannan suka kashe wasu, sannan suka ƙona motar. Allah ne ya tseratar da mu," kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Daga cikin waɗanda aka kashe har da mahaifin ango da sauran ƴan'uwansa da abokan arziki.

Ina aka kwana game da hukunci?

Da zarar an samu irin waɗannan kisan gilan da wasu ƙalibun jihar Filato ke yi a kan matafiya, hukumomi kan ɗauki alƙawarin ɗaukar mataki na hukunta masu laifi.

Amma a tsawon shekaru, babu wani abu a zahiri da ake ganin gwamnatin jihar Filato ko na tarraya na yi domin magance matsalar ko kuma ladabtar da masu laifi a kauyukan jihar ta Filato.

A cewar gwamnan, babu wani dalili da mutanen da ba su ji ba su gani ba, suna kan hanya a tare su a kashe.

"Na faɗa wa gwamnan Filato cewa dole ne a ɗauki mataki domin ba za a mayar da jiha ta koma ta kashe mutane kawai ba."

"Na faɗa wa gwamnan cewa abin da ake yi a Filato dole a bari, idan kuma ba a bari ba to laifin gwamna ne," in ji shi.

Ita ma Gamayyar Ƙungiyoyin Arewacin Najeriya ta CNG, ta nemi gwamnatin jihar Filato da ta biya iyalan matafiyan ƴan jihar Kaduna da aka yi wa kisan gilla a ƙaramar hukumar Mangu, diyya tare da tattaki zuwa Kaduna don yin ta'aziyya.

Shugaban gamayyar ƙungiyoyin, Jamilu Aliyu Chiranci ya bayyana cewa lokaci ya yi da hukumomi a jihar Filato za su ɗauki matakai na kawo ƙarshen irin wadannan kashe-kashen.