Me harin ƙunar baƙin wake a Borno ke nunawa a Najeriya?

Asalin hoton, @ZagazOlaMakama
Ƙaruwar hare-haren Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya na ƙara jefa fargaba kan makomar yankin inda masana tsaro suka ce akwai buƙatar sauya salon yaƙi.
Wannan na zuwa bayan wani mummunan harin ƙunar bakin wake da aka kai a garin Konduga a jihar Borno a ranar Juma'a da ya kashe mutane da dama.
Rundunar ƴansandan jihar Borno ta ce mutum 10 aka kashe, yayin da mutanen yankin suka ce sama da mutum 20 aka kashe a harin.
A ranar Juma'ar da ta gabata ne wata mata ta tayar da bama-baman da ke ɗaure a jikinta a wurin ƴansakai da mafarautan da ke taimakawa sojojin Najeriya yaƙi da mayaƙan Boko Haram.
Gwamnatin Najeriya ta yi allawadai da harin da aka shafe lokaci mai tsawo ba a ga irinsa ba.
Mayaƙan Boko Haram da na ISWAP sun tsananta hare-hare a ƴan watannin nan a ƙauyukan Borno da kuma maƙwabtan jihohi.
Sun kuma kai hare-hare a sansanonin soji inda suka kashe sojoji da kwasar makamai.
Masana tsaro a Najeriya na ganin harin ƙunar baƙin wake da aka kai a Konduga yana ƙara tabbatar da dawowar barazanar Boko Haram.
"Yana nuna cewa Boko Haram tana ƙoƙarin dawo wa ne ta hanyar kai hare-hare kan fararen hula da kuma dawo da kai harin ƙunar baƙin wake wanda ƴanmata ke kai wa," in ji masanin tsaro Barista Audu Bulama Bukarti.
Masanin ya ce irin salon da suka saba kai hare-hare a baya ne Boko Haram ke son dawo wa da shi.
Ya ce an ɗauki lokaci mai tsawo ba a kai harin ƙunar baƙin wake ba a Najeriya, wanda hakan a yanzu na nuna wata babbar barazanar tsaro ce ta dawo a Najeriya.
"Ya kamata salon yaƙin da ake yi ya sauya saboda yadda suke amfani da yara mata wajen kai hari, domin idan aka yi wasa zai iya fantsama daga arewa maso gabas zuwa sauran sassan Najeriya," a cewar Barista Audu Bulama Bukarti.
Kusan sama da shekara 16 Najeriya ke fama da matsalar Boko Haram.
Dubban mutane ne suka mutu a yaƙin Boko Haram tun 2009, yayin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce sama da mutum miliyan biyu ne rikicin ya raba da gidajensu.
Rikicin Boko Haram ya bazu zuwa kasashen Nijar da Kamaru da Chadi da ke makwabtaka da Najeriya, lamarin da ya tilasta wa ƙasashen samar da rundunar soji da háɗin guiwa domin yaƙi da mayaƙan ƙungiyar.











