Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mayakan Boko Haram sun yi awon gaba da mutum 160 a garin Kuchi da ke jihar Neja
Al’ummar garin Kuchi da ke karamar hukumar Munya ta jihar Neja sun tsinci kansu cikin wani mawuyacin hali sakamakon hare haren da ‘yan bindiga da ake zargin mayakan Boko Haram ne suka kai a baya baya nan.
Al'amarin ya sa mazauna garin tserewa kamar yadda shugaban ƙaramar hukumar ta Munya, Honarabul Aminu Na-jume ya shaida wa BBC:
‘’ Jama’a da dama sun watse, mun samu IDP camps daban-daban a yanzu, tun da aka fara wannan tashin hankali, ba a taba samu iftila’i irin wannan ba, kuma sun kwashe awa 8 suna aika-aikar’’ in ji shi.
Maharan sun kashe mutum takwas kuma sun yi awon gaba da mutum dari da sittin, bayan da suka fasa shaguna suka ɗebe kayan abinci da na masarufi a cewar shugaban karamar hukumar ta Munya:
‘’ Da suka zo wurin sun fi awa biyu suna dafa Indomie a shagunan masu shayi, su na shan shayi, su na hura wuta, su na jin dumi saboda ana ruwan sama’’
‘’Bayan nan kuma sun fasa shagunan mutane, sun kwashe abubuwan sanyi irinsu lemun kwalba da abinci da biskit da shinkafa,’’ in ji shi.
Honarabul Aminu Na-Jume ya ce a cikin mutum dari da sittin da aka sace akwai mata da yara da maza da tsofaffi da ma sarkin Hausawan garin da ke fama da rashin lafiya.
Ya kuma ce yanayin yawan maharan da karfinsu da makaman da suke rike da su ya nuna cewa su ba kananan ‘yan bindiga bane.
Ya ce suna rike da tutarsu ta Boko Haram kuma ya yi ikirarin cewa yanayin maganarsu ya yi kama da na 'yan Boko haram
Al'ummar garin na Kuchi sun yi kira ga gwamnatin tarraya da ta taimaka mu su da jami’an tsaro domin dakile ayuikan ‘yan bindigar da ke addabarsu.