Ƴan Boko Haram sun sace gwamman mutane a Ngala na jihar Borno

Rahotanni daga jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya na cewa wasu da ake zargin ƴan ƙungiyar Boko Haram ne sun sace gwamman mata da maza a garin Ngala da ke makwabtaka da Jamhuriyar Kamaru.

Wani mazaunin Gamboru Ngala ya shaida wa BBC cewa lamarin ya faru ne lokacin da mutanen suka je saran itace a cikin daji.

Bayanai sun nuna cewa waɗanda aka sacen na zaune ne a wani sansanin ƴan gudun hijira da ke yankin.

Waɗansu mazaunan garin sun ce lamarin ya faru ne a ƙarshen mako amma saboda rashin kyawun hanyoyin sadarwa sai daga ranar Talata aka soma samun bayanai a kan lamarin.

Kawo yanzu hukumomi ba su tabbatar da adadin waɗanda aka sace ba amma waɗansu mazauna yankin sun ce an sace fiye da mutum 100.

"Ranar Lahadi muka samu labarin cewa 'yan gudun hijira suka tafi daji domin yanke itace sai 'yan Boko Haram suka sace su. Mutane sama da 200 ne suka shiga dajin amma sai suka zabi 113 suka sace sannan suka bar tsofaffi da kananan yara su tafi," in ji mutumin da ya bukaci a sakaya sunansa.

Wasu kafafen yaɗa labarai a Najeriya na cewa mutanen da aka yi garkuwa da su sun kai 319 kuma idan hakan ya tabbatar, to shi ne adadi mafi yawa da aka sace tun bayan kwashe ɗaliban sakandaren Chibok su 276, shekaru 10 da suka wuce.

Wannan lamarin na zuwa ne bayan da gwamnatin jihar Borno tayi iƙirarin cewa kashi 95 cikin 100 na mayaƙan Boko Haram sun miƙa wuya ko kuma an kashe su.

An shafe fiye da shekaru 10 ana rikici da ƴan ƙungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 40,000 a yayin da waɗansu fiye da miliyan biyu suka rasa muhallansu.

A watan Mayun 2023 ne shugaba Bola Tinubu ya sha rantsuwar kama mulki a Najeriya inda ya ɗauki alƙawarin inganta tsaro a ƙasar amma kuma lamarun na kara dagulewa.