Ƙarin 'yan Najeriya sun shiga tashin hankali saboda ƙazancewar rashin tsaro

    • Marubuci, Mukhtari Adamu Bawa
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Senior Broadcast Journalist

Ana samun ɗumbin 'yan Najeriya da ke ƙara shiga zulumi da kwanan zaune saboda daɗuwar ayyukan rashin tsaro a sassan ƙasar, musamman na hare-haren 'yan fashin daji da satar mutane don kuɗin fansa.

Da yawa na da ra'ayin, ƙoƙarin da hukumomi ke cewa suna yi na tsare rayuka da dukiya da kuma mutuncin 'yan ƙasar, daga maharan da suka addabi al'umma, bai isa ba.

Hankula sun daɗa tashi ne cikin 'yan kwanakin nan har a Abuja, babban birnin Najeriya, saboda sake yunƙurowar 'yan fashin daji da masu satar mutane don neman kuɗin fansa.

Wani ɗan Najeriya mai gwagwarmayar siyasa Sanata Shehu Sani, ya wallafa a shafinsa na X cewa, kamata ya yi a ce Abuja ta kasance wani gida na kwanciyar hankali, kuma alƙaryar hutawa ga manyan mutane. Sai dai fitintinun da ke faruwa a sauran sassan Najeriya, a yanzu sun lallaɓa sun shiga har cikin babban birnin.

A baya-bayan nan dai an ba da rahoton yadda 'yan bindiga suka kashe wata matashiya, bayan sun sace ta tare da 'yan'uwanta shida da kuma mahaifinta a gidansu da ke Bwari, wanda ke wajen Abuja.

Haka zalika, rashin tsaro na daɗa ta'azzara a jihohin da suka zagaye Abuja, ciki har da Neja da Kaduna da Nasarawa, musamman hare-haren 'yan fashin daji. Don haka ba abin mamaki ba ne da cikin mazaunan Abuja ya sake ɗurar ruwa.

A ƙarshen watan jiya, wasu 'yan bindiga waɗanda har yanzu hukumomi ba su kai ga kamowa ba, sun auka wa ƙauyuka a cikin jihar Filato mai nisan ƙasa da kilomita 250 daga Abuja, tare da kashe kimanin mutum 200.

Rundunar 'yan sandan Najeriya a ranar Talata 9 ga watan Janairu ta yi baje-kolin makaman da ta ce jamia'nat sun kama baya-bayan nan a sassan ƙasar daga 'yan fashi da masu fasarar makamaki, a ciki har da harsashi 5,454 da bindigogi guda 68.

An dai yi ta alla-wadai da matakin sacewa da kashe matashiya Nabeeha, wadda har zuwa lokacin wannan rahoto, masu garkuwa ke ci gaba da garkuwa da 'yan'uwanta mai yiwuwa a cikin daji.

'Yan bindigar dai sun ƙara kuɗin fansar da suka nema, bayan sun sako mahaifin Nabeeha, don ya je ya haɗo kuɗin da suka nema. Iyalin Mansoor Al-Ƙadriyah dai na fuskantar barazanar kisa a hannun masu garkuwa, matuƙar aka gaza kai kuɗin fansar su.

Da yammacin jiya, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wata ganawar gaggawa da manyan hafsoshin tsaron ƙasar a fadarsa ta Aso Rock.

Rahotanni sun ce taron wanda mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu ya halarta, ya maida hankali ne a kan ƙoƙarin shawo kan ƙaruwar ta'addanci da satar mutane don neman fansa da kashe-kashe a faɗin Najeriya.

Kafin sannan babban sufeton 'yan sandan ƙasar, Kayode Egbetokun shi ma ya yi taro da manyan jami'an rundunarsa kan ƙarin damuwar da ake nunawa game da taɓarɓarewar tsaro a babban birnin na Najeriya.

Haka zalika, an ambato ministan Abuja Nyesom Wike na gudanar da taro da masu ruwa tsaki a birnin kan sha'anin tsaro, bayan sukurkucewar al'amura.

Masu fafutuka kamar ƙungiyar Amnesty International sun yi kira ga Shugaba ya ɗauki dukkan matakan da ke kan doka wajen kawo ƙarshen tashe-tashen hankula da fargabar da ake ciki a Najeriya.

Amnesty ta kuma ba da shawarar gudanar da bincike kan yawan sace-sacen mutane da kashe-kashe kuma a tabbatar da hukunta duk masu hannu cikin lamarin.

Ta ce 'yan fashin daji suna fasa gidaje tare da kwasar mutane zuwa maɓoya da nufin yin garkuwa da su har sai an kai kuɗin fansa.

A cewarta, iyalai da yawa sukan gwammace kada su kai rahoton irin wannan sata idan lamarin ya ritsa da makusantansu kuma suka biya kuɗin fansa saboda fargabar za a iya cutar da su daga bisani, don haka ana samun irin waɗannan sace-sace da ba a sanin aukuwarsu.

Ta yi iƙirarin cewa annobar satar mutane a baya-bayan nan wata manuniya ce ta tsagwaron kasawar hukumomin Najeriya wajen kare rayuka yadda ya kamata.

Amnesty ta ce satar mutane don neman kuɗin fansa ya zama wani ɓangare na rayuwar yau da kullum ga 'yan Najeriya. Kuma a cewarta waɗanda ake sacewa kan fuskanci azabtarwa da duka da horon yunwa da barazanar kashewa da fyaɗe da rufe idanun mutum tsawon kwanaki da kuma zagi da duka.

Ilmantar da ɗumbin matasa

Shugaba Bola Tinubu dai ya yi Alla-wadai da sake ɓarkewar sace-sacen mutane don neman kuɗin fansa da hare-haren 'yan fashin daji, lamarin da ya bayyana da mai cusa damuwa, baƙin hali ne kuma babu Allah a ciki.

Da yake wannan jawabi ranar Talata lokacin da ya karɓi wani ayarin malaman addinin Musulunci daga wata ƙungiya da ake martabawa a ƙasar, Jam'iyyatu Ansaridden, Shugaba Tinubu ya kuma ce yayin da jami'an tsaro ke aiki cikin sauri domin shawo kan wannan ƙalubale nan take, gwamnatinsa za ta ɓullo da tsarin ilmantar da ɗumbin matasa.

Ya ce nan gaba kaɗan zai ɓullo da duk tsare-tsare da manufofi da dukiyar da ake buƙata don wani gagarumin shirin ilmantar da ɗumbin matasan Najeriya.

Bola Tinubu ya ce ilmi shi ne maganin fitintinun da suka hana ƙasar sakat, don haka: "Babu makamin yaƙi talauci da ke da tasiri kamar koyarwa".

Ya yi wa malaman alƙawarin cewa gwamnatinsa za ta kawo canjin rayuwa ga al'ummar Najeriya, don inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali da ƙaruwar arziƙi.

Shugaban ya nanata cewa abu ne mai muhimmanci a bunƙasa ƙoƙarin sabunta ilmi ta hanyar makarantun Islamiyya da ake da su don matasa a arewacin Najeriya ta yadda za a hanzarta ci gaban yankin da Najeriya har ma da ɗaukacin Afirka.

A ƙarshe Tinubu, ya yi roƙo ga malaman su duƙufa addu'o'i.

Yayin da za a zuba ido domin ganin ƙarin matakan da shugaban ya alƙawarta, na yaƙi da wannan matsala da ta hayayyaƙo, tashin hankali da fargaba mai yiwuwa za su ci gaba da hana 'yan Najeriya barci, har zuwa lokacin da aka fara ganin tasirin matakan a ƙasa.