Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda matsalar tsaro ta addabi al’ummomin Bwari a Abuja
Al’ummomin wasu ƙauyuka na yankin Bwari, ɗaya daga cikin ƙananan hukumonin babban birnin tarrayar Najeriya, Abuja, na cikin zaman dar-dar game da ƙamarin da suke cewa matsalar tsaro ta yi a yankin.
A makon da ya gabata rahotanni sun ce mutane bakwai ne ‘yan gida ɗaya, wasu ‘yan bindiga su ka yi awon gaba da su, tare da neman kuɗin fansa kafin su sako su.
Wannan fargaba da ake fama da ita a wannan yankin ta shafi garuruwa da dama da ke kewaye da ƙaramar hukumar.
Wata mazauniyar yankin da ta buƙaci a sakaya sunanta, ta bayyana cewa lamarin rashin tsaron da suke fuskanta ya jawo ba sa iya gudanar da harkokin rayuwarsu cikin natsuwa saboda tsoron hare-haren 'yan bindiga da suke yi.
'Bwari, gaskiya babu sauki yanzu fa, cikin kwanakin nan ana cikin tashin hankali domin ana bin gidajen mutane da ke unguwanni daban-daban na yankin ana kwashe su'. In ji ta
Ta ƙara da cewa mazauna yankin ba su da wata masaniya kan waɗanda ke aikata wannan mummunan aiki, sun dai san cewa akasari sukan yi garkuwa da mutane ne domin neman kuɗin fansa.
Ta ce 'sai su kira wani kudin da wataƙila har mutum ya mutu ba zai taɓa ganinsu ba. Sai a kama talakan da ba shi da abincin ci, a ce wai ya kawo miliyan hamsin, a ina zai samo su?'
Ta yi bayanin cewa duk da mutanen yankin na ƙokarin haɗa ƙungiyoyin sa-kai domin kare al'ummarsu suna buƙatar taimakon jami'an tsaro.
A wata sanarwa da jami'ar hulda da jama'a ta rundunar 'yan sandan Abuja, Josephine Adeh ta fitar, ta yi kira ga jama'a da su guji yaɗa jita-jita domin hakan na haifar da ruɗani da kuma fargaba a zukatan al'umma.
Sanarwar ta ƙara yin kira ga mazauna yankin na Bwari da su sanar da jami'an tsaro a duk lokacin da suke fuskantar wani lamarin da suke ganin ya zame masu barazana ga rayukansu.
Rundunar ta bayar da tabbacin cewa ta ɗauki matakan tsaro a yankin da sauran sassan birnin tarayyar domin magance matsalar rashin tsaron da ake fama da ita.