Abu hudu da suka jawo zaman fargaba a Abuja

Hankula sun tashi. Fargaba ta ƙaru. An shiga yanayi na zaman ɗar-ɗar.

To amma duk a ina hakan ke faruwa? Ba a ko ina ba ne illa Abuja, babban birnin Najeriya.

Wani da ba mazaunin Abuja ba zai ce ai wannan yanayi ne da tuni wasu sassan ƙasar suka samu kansu a ciki, saboda ta'azzarar rashin tsaro da aka daɗe ana fama da shi.

E, haka ne. Amma abin da zai fi ɗaga hankali a wannan lamari shi ne ganin cewar a Abuja ne manyan madafun ikon ƙasar suke.

A Abuja ne yanki mafi muhimmanci na ƙasar da ya ƙunshi fadar shugaban ƙasa da majalisar dokoki da kuma ɓangaren shari'a suke.

Ofisoshin jakadancin ƙasashen waje da hedikwatar ma'aikatar tsaro da ma'aikatar harkokin cikin gida da hedikwatar rundunonin sojin ƙasar da hedikwatar rundunar ƴan sanda da ma manyan barikokin soji duk suna Abuja.

Kenan dole hankulan mazauna birnin da ma na sauran sassan ƙasar su tashi, idan har aka ga alamu na wani abu da ke kama da rashin tsaro a inda ake sa ran zai fi ko ina samun tsaro.

Duk da cewa dai a baya Abujar ta sha fuskantar barazanar tsaro inda har aka dinga kai mata hare-hare, daga baya tsaro ya samu a birnin, wataƙila shi ya sa a yanzu dawowar duk wata barazana ka iya ɗaga hankalin mazauna cikinta.

To amma mene ne ke faruwa haka da har aka shiga wannan yanayi na zaman ɗar-ɗar a Abuja a ƴan kwanakin nan?

BBC Hausa ta yi duba kan lamarin a cikin wannan maƙala.

Harin gidan yarin Kuje

A ranar 5 ga watan Yuli aka kai hari gidan yari mai matsakaicin tsaro da ke garin Kuje mai nisan kilomita 41 daga cikin birnin Abujar.

Rahotanni sun ce maharan sun yi ta ruwan wuta tare da fin ƙarfin jami'an tsaron wajen, sannan sun kuɓutar da fursunoni da dama.

Wannan lamarin ya kaɗa hantar al'ummar ƙasar da dama ba wai mazauna Abuja ba kawai, musamman da hukumomi suka ce mafi yawan fursunonin da suka tsere ɗin mayaƙan Boko Haram ne da ke tsare.

Sannan kuma ana ganin a shiga har babban birnin tarayya a fasa gidan yari lallai abu ne mai ɗaga hankali.

Hukumar kula da gidajen yari ta Najeriya ta fitar da jerin sunayen mutum 69, kwana uku bayan kai harin, kuma ta ce ƴan Boko Haram ne.

Labarin cewa ƴan boko Haram sun tsere daga gidan yarin ya fi komai ƙara dugunzuma hankalin ƴan Najeriya.

Kwanaki kadan bayan nan hukumomi suka bayar da rahoton gano biyu daga cikin wadnada suka tsere din, ɗaya a wata tahsar mota ma aka gano shi a Abuja.

Mako uku bayan harin ne sai ga wani bidiyo na yadda maharan da suka sace fasinjojin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna suka saki bidiyon da suke zane su, kuma a ciki an ga wani da ya yi ikirarin yana daga cikin waɗanda suka tsere daga Kujen.

Lallai wannan lamari ne da ya sake dugunzuma mutane, musamman da ƙwararru kan harkar tsaro suka yi fashin baƙin cewa ya kamata mutane su sake taka tsantsan.

Umarnin rufe makarantu a Abuja

Ba a gama farfadowa daga lamarin harin gidan yarin Kuje ba sai kwatsam ga sanarwa daga Ma'aikatar Ilimi ta Najeriya a ranar Litinin 25 ga watan Yuli, tana bayar da umarnin rufe makarantar sakandiren Kwali da ke Abuja babban birnin kasar.

Sanarwa ta ce rufe makarantar ya zama wajibi ne bayan da 'yan bindiga suka kai hare-hare a ƙauyukan Sheda, da Lambata da ke maƙwabtaka da makarantar, abin da ke zama barazana ga makarantar.

Sannan wasu bayanai sun ce an samun saƙonnin gargadi kan barazanar hari a wasu yankuna ko makarantu a Abuja.

Wannan dalili ya sanya gwamnatin Najeriyar ta umarci a gaggauta rufe makarantun birnin Tarayyar gaba ɗaya daga ranar Laraba 27 ga watan Yuli, maimakon Juma’a 29 da aka tsara makarantun za su yi hutu.

Haƙiƙa wannan abu ya sanya matuƙar fargaba da ɗar-ɗar a zuƙatan mazauna Abuja. Kuma kafin ka ce kwabo iyaye sun yi ta rububin kwaso ƴaƴansu da suke makarantun kwana.

Makarantu kuma sun yi gaggawar kammala komai tare da rufewa.

Ruɗani ya ƙaru, tsoro ya cika zuƙata, amma hukumomi sun ba da tabbacin samar da tsaro.

Hari kan jami'an rundunar dogarawan fadar shugaban ƙasa

Ana cikin wannan juyayi kuma sai ga shi a ranar Talata 26 ga watan Yuli rundunar dogarawan fadar shugaban ƙasa ta ce ta baza jami’anta a kewaye da dazukan Bwari domin fatatakar ‘yan bindigar da suka yi wa jami’anta kwanton-ɓauna a daren Lahadi.

A wata sanarwa da ta aikewa BBC, rundunar ta ce an murƙushe harin da aka kai musu na ranar Lahadi, sai dai akwai jami’anta da dama da suka jikkata.

Sannan wasu bayanan sun ce an kashe sojoji uku a harin, ciki har da wani Kyaftin ɗin rundunar.

Harin na daren Lahadi ya auku ne kan sojojin da ke bayar da tsaro a kewayen kwalejin koyar da aikin lauya da ke Bwari, mai nisan kilomita 37 daga ƙwaryar babban birnin.

Kwalejin ta aike da saƙon ankarar da jami’an tsaro kan wata wasiƙar barazanar kai musu hari da aka kai wa makarantar.

Kafin a hallaka su, sai da sojojin suka je makarantar suka tattauna da mahukunta kan matakan da ya kamata a dauka domin kare ɗalibai, malamai da ma ginin makarantar.

Sai dai kamar yadda masu magana ke cewa baya ba ta kaɗan, bayan barin kwalejin a hanyar da ta hada Bwari zuwa Kubwa, sai ‘yan bindigar suka yi musu kwanton-ɓauna, nan take kuma sojojin uku suka rasa rayukansu.

Sannan ko a baya-bayan nan an yi garkuwa da wani basaraken yankin Kucihbuyi da ke ƙaramar hukumar Bwarin.

Ƙaruwar shingayen bincike

Duk ana cikin waɗannan yanayi sai kuma mazauna birnin Abuja suka lura da ƙaruwar shingayen bincike da baza jami'an tsaro ta ko ina.

Lallai wannan abu ne da dole zai sanya tsoro da fargaba a zuƙatan mazauna birnin, musamman ganin cewa jiya na son dawowa, wato yanayin da aka samu kai shekaru kusan takwas da suka gabata.

Sannan kuma a ranar Laraba 27 ga watan Yuli, sai ga saƙon babban Sufeton Ƴan sandan ƙasar yana ba da umurnin a tura ƙarin jami'ai zuwa wasu muhimman sassan Abuja.

Ya bayar da umurnin ne a lokacin da ƙungiyar ISWAP ke barazanar kai hari a kan birnin.

A cikin sanarwar da ta fitar, rundunar ƴan sandan ta ce babban Sufeton Ƴan sanda Usman Baba Alkali, ya cewa rundunar ta ɗauki duk wani matakin da ya dace wajen tsaurara tsaro a birnin Abuja da kewaye.

Wannan ne ma, a cewar sanarwar ya sa babban Sufeton ya ba da odar a tura ƙarin ƴan sandan a dukkan muhimman wurare da ke birnin.

Kazalika ya buƙaci sashen tattara bayanan sirri na rundunar ya dage wajen tattara bayanai tare da haɗa-gwiwa da sauran hukumomin tsaro da ke ƙasar, wajen sada bayanan, duk da nufin inganta tsaro.

Haka kuma sanarwar ta buƙaci mutanen gari da su cigaba da gaba da kasancewa a ankare, sannan su ba da haɗin kai ga jami'an tsaro ta hanyar samar da bayanan da za su taimaka wajen kare su daga aika-aikar miyagu.

Duk da cewar sanarwa ba ta fayyace ko umurnin da babban Sufeton Ƴan sandan ya bayar yana da alaƙa da halin da ake ciki na zaman zulumi ko zaman tsoro a birnin na Abuja ba, amma za a iya cewa biri ya yi kama da mutum.

Yanzu dai batun tsaro ne a gaban mazauna birnin Abuja da kewaye, sakamakon barazanar kai hari da ƴan kungiyar ISWAP, wato reshen mayakan da suka ɓalle daga jikin ƙungiyar Boko Haram da wasu ƴan bindiga ke yi a kan birnin.

Wannan matsala ta tabarbarewar tsaro dai babban ƙalubale ne ga gwamnati - saboda kamar yadda masu sharhi ke cewa - babban birnin tarayya ma bai tsira ba, to ina ga sauran sassan ƙasar?