Ƴan bindiga sun kai hari shingen binciken sojoji a kusa da Abuja

Rahotanni daga Najeriya na cewa wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne sun kai hari wani shingen bincike na sojoji da ke kusa da dutsen Zuma da ke kusa da Abuja babban birnin kasar.

Ganau sun shaida wa BBC Hausa cewa maharan sun je wurin ne bayan magariba inda suka ɓude wuta a shingen binciken.

Jama'ar da ke wurin sun ce sun ji ƙarar harbin bindiga ba ƙaƙƙautawa, lamarin da ya sa wadanda ke kusa da wurin suk gudu domin neman mafaka.

Rahotanni dai sun ce maharan sun yi musayar wuta da jami'an tsaro, sai dai babu tabbaci kan ko akwai wanda ya jikkata ko ya rasa ransa. Ko da yake wasu rahotanni daga kafafen watsa labaran kasar na cewa an kashe sojoji da dama.

Wani ganau ya bayyana wa BBC cewa suna cikin mota suna tafiya sun je daidai wurin dutsen Zuma, sai suka ji ƙarar bindiga ba ƙaƙƙautawa, lamarin da ya sa suka bar motocinsu suka arce cikin daji.

"Mun bar motocinmu a buɗe muka shiga daji a guje, muka je can kusa da Madallah u-turn, dama mun taho ne daga Abuja za mu je Suleja, can dai bayan kamar minti 15 zuwa talatin haka sai muka yi sa'a mutane suna ta juyawa mu ma muka je muka ɗauko motarmu muka juyo," in ji shi.

Ya bayyana cewa ko a lokacin da suka bar wurin, ƴan bindigar na ci gaba da buɗe wuta ba ƙaƙƙautawa.

Duk ƙoƙarin da muka yi domin ji daga bakin jami'an tsaro ya ci tura. Wannan harin dai na zuwa ne ƙasa da wata ɗaya bayan ƙungiyar Boko Haram ta kai hari gidan yarin Kuje da ke Abuja babban birnin Najeriya, inda fursunoni da dama suka tsere.

Kuma tun daga lokacin mazauna birnin suka ƙara shiga cikin zulumi da fargaba.

Ko a makon nan sai da ƴan bindiga suka kashe wasu daga cikin dogarawan fadar shugaban ƙasar a yayin wani harin ƙwanton-ɓauna, duk da cewa sojojin sun ce sun kashe talatin daga cikinsu bayan farautar ƴan bindigar da suka shiga.

Hari kan dogarawan shugaban ƙasar na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan ƴan bindigar sun yi barazanar sace shugaban ƙasar da gwamnan Kaduna a wani bidiyo da suka fitar.