Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sojoji sun ce sun ceto ɗalibai 137 ƴan makarantar Kuriga da aka sace
Shalkwatar tsaron Najeriya ta ce ta kuɓutar da ɗalibai 137 na makarantar gwamnati ta Kuriga a ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.
Darektan da ke kula da harkokin yaɗa labarai na tsaron ƙasar, Manjo Janar Edward Buba a cikin wata sanarwa, ya ce sun ceto ɗaliban su 137 a dajin Zamfara.
A cewar sanarwar, sojojin sun ceto ɗalibai mata 76 da kuma maza su 61.
Tun a ranar 7 ga watan Maris ne aka sace ɗaliban firamare da na sakandare a makarantarsu da ke ƙauyen Kuriga a Kaduna kuma wani malamin makarantar da ya sha da ƙyar ya ce ɗalibai kusan 287 aka sace.
Malamin makarantar mai suna Sani Abdullahi ya ce an sace ɗalibai na ɓangaren sakandare 187, sai kuma bangaren firamare ɗalibai 100.
"Sojoji tare da jami'an ƙaramar hukuma da na cibiyoyin gwamnati sun haɗa hannu wajen ceto ɗaliban da aka sace a makarantarsu da ke Kuriga," in ji Edward Buba.
Sai dai mai magana da yawun shugaban Najeriya, Abdulazeez Abdulazeez ya shaidawa BBC Hausa cewa "ɗaya daga cikin malaman da aka sace tare da ɗaliban ya rasu".
Tun da farko ƴanbindigar sun buƙaci a basu naira biliyan ɗaya a matsayin kuɗin fansa kafin ranar 27 ga watan Maris domin su saki ɗaliban. Kuma babu tabbas ko an biya kuɗin fansa kafin kuɓutar da ɗaliban.
Galibin ɗaliban da aka sace ƴan shekaru biyar ne zuwa 18.
A ranar Lahadi da asuba ne gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya fitar da wata sanarwar inda ya ce "an sako duka ɗaliban kuma suna cikin ƙoshin lafiya".
Sanarwar ba tayi ƙarin bayani ba game da irin matakan da aka bi wajen sako ɗaliban.
"Ba dare babu rana ina tattaunawa da Malam Nuhu Ribadu domin lalubo hanyoyin da za a bi wajen kuɓutar da ɗaliban, kafin mu samu nasara," in ji Uba Sani.
An sace mutane da dama a Najeriya cikin watan Maris
A ranar shida ga watan Maris ne aka fara satar farko a watan nan, kuma an yi ne a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Wasu da ake kyautata zaton mayaƙan Boko Haram sun sace a kalla ƴangudun hijira 200, yawancinsu mata da ƙananan yara a lokacin da suka shiga daji yin ice.
Duk da ƙaddamar da nemansu da sojoji suka yi, amma hakan ta gagara, babu wanda aka yi nasarar kuɓutarwa.
Washegari watau ranar bakwai ga watan dai na Maris, ƴanbindiga suka tasa ƙeyar ɗalibai kusan 300 daga makarantar firamare da sakandare a jihar Kaduna.
Daga bisani gwamnatin jihar ta sanar cewa ɗalibai 28 daga cikin waɗanda 'yan bindigar suka sace sun tsere daga hannunsu.
A ranar tara ga watan Maris, ƴanbindiga sun sace ɗalibai ƴan makarantar allo 17 a wata makaranta da ke jihar Sakkwato a arewa maso yammacin Najeriya.
Amma an sako su a ranar 22 ga watan Maris.
Kwanaki biyu bayan nan, waɗansu da ake zargin ƴanbindiga ne sun kai hari ƙaramar hukumar Kajuru a jihar Kaduna tare da sace mutane 61.
Hare-hare na baya-bayan nan ma sun faru ne a Kajuru, inda ƴanbindigar suka sace akalla mutane 100, yawanci mata da ƙananan yara.