Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lokuta 15 da aka sace ɗalibai a makarantu a Najeriya
- Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
- Aiko rahoto daga, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 9
A makon nan an samu dawowar hare-hare kan makarantu da sace ɗalibai bayan kwashe kimanin shekara guda da samun sauƙin al'amarin.
BBC ta yi duba dangane da sace-sacen ɗalibai a makarantu da suka girgiza Najeriya da ma duniya baki ɗaya.
Sakandiren St. Mary's jihar Neja
A ranar Alhamis 20 ga watan Nuwamban 2025 ne wasu ƴan bindiga suka kutsa makarantar sakandire ta St. Mary's inda suka yi awon gaba da ɗaliban da ba tabbatar da yawansu ba.
Cikin wata sanarwa da cocin St. Mary's ta fitar ta ce maharan sun ƙaddamar da harin ne tsakanin ƙarfe 1:00 zuwa 3:00 na dare a cikin makarantar.
''Ƴanbindiga sun auka makarantar furamare da sakandiren kwana ta St. Mary da ke garin Papiri, tare da sace wasu ɗalibai da malamai tare da harbe maigadin makarantar'', in ji sanarwar.
Cocin ta ce lamarin ya haifar da tashin hankali da ruɗani a cikin hotuna.
Haka kuma cocin ta ce ta yi matuƙar damuwa da harin, tare da yin Allah wadai da shi da kuma kiran al'umma su kwantar da hankali tare da bai wa jami'an tsaro haɗin kai domin tabbatar da kuɓutar da ɗaliban.
Sakandiren ƴan mata ta Maga
A ranarLitinin 17 ga watan Nuwamban 2025 ne ƴan bindiga suka sace ƴan mata ɗalibai 25 daga makarnatar kwana da ke garin Maga na ƙaramar hukumar Danko-Wasagu a jihar Kebbi.
Bayanai sun ce maharan sun far wa makarantar ɗauke da muggan makamai inda suka yi ta harbi kafin daga bisani su tafi da ɗaliban.
Ɗaya daga cikin malaman makarantar da ya zanta da BBC ya kuma buƙaci a sakaya sunansa ya ce maharan sun kashe malami guda da maigadin makarantar a lokacin harin.
Malamin ya ce maharan sun far wa makarantar a lokacin da ɗaliban tsaka da barci.
''Sun shigo makarantar ne daga yamma, riƙe da muggan makamai, inda suka yi awon gaba da ɗalibai masu yawa'', kamar yadda ya bayyana.
Sakandiren mata ta Chibok
A ranar 14 ga watan Afrilun 2014 ne mayaƙan Boko Haram suka kai wani hari makarantar sakandaren mata da ke Chibok a jihar Borno, inda suka sace ɗalibai masu yawa.
Mayaƙan ɗauke da manyan bindigoyi sun shiga garin da tsakar dare suka tashi mazauna da ƙarar harbi kafin su kutsa cikin ɗakunan kwanan ɗalibai suka loda su a motoci sannan suka yi awon gaba da ƴanmata 276.
Wannan hari shi ne irin sa na farko da mahara suka sace ɗalibai a makaranta, batun satar ɗaliban ya ja hankalin duniya.
Hakan ya sa ƙasashen duniya suka yi ta sukar gwamnatin Najeriya ta wancan lokacin bisa rashin ɗaukar mataki.
Hasalima an ƙirƙiro maudu'in #BringBackOurGirl a shafin Twitter wanda ke nufin 'A dawo da ƴaƴanmu mata', inda fitattun mutane ciki har da mai ɗakin tsohon shugaban Amurka Michelle Obama suka riƙa yayatawa domin jan hankalin hukumomi su ɗauki mataki.
Kodayake an ceto galibinsu lokacin da shugaba Muhammadu Buhari ya karɓi mulki, amma har yanzu wasu na hannun mayaƙan ƙungiyar ta Boko Haram.
Sakandiren mata ta Dapchi
A watan Fabrairun 2018 ne wasu da ake zargi mayaƙan Boko Haram ne kuma suka kai hari makarantar mata da ke garin Dapchi na jihar Yobe sannan suka sace ɗalibai 110.
Lamarin ya faru ne kusan shekara huɗu bayan sace ƴanmatan makarantar Chibok.
Bayan sace su ne gwamnatin tarayya ta tura sojojin sama da sauran jami'an tsaro domin ceto ƴan makarantar.
Gwamnan jihar Yobe na wannan lokaci Ibrahim Gaidam, ya ɗora alhakin sace matan a kan sojojin Najeriya waɗanda ya zarga da janye shingen binciken ababen hawa daga garin na Dapchi, lamarin da ya ce shi ya bai wa Boko Haram damar sace ɗaliban.
An saki 104 daga cikinsu a watan Maris na 2018 yayin da biyar suka mutu a ranar da aka sace su, amma har yanzu yarinya ɗaya mai suna Leah Sharibu na ci gaba da kasancewa a hannun mayakan na Boko Haram, waɗanda suka ƙi yarda su sake ta saboda 'ta ce ba za ta bar addininta na Kirista ba'.
Sakandiren Kankara
A watan Disamban 2020 ne wasu ƴan bindiga suka kai hari makarantar sakandaren kimiyya ta maza da ke garin Kankara na jihar Katsina da ke arewacin Najeriya.
Ƴan bindigar sun sace ɗalibai fiye da 300 inda suka yi doguwar tafiya da su zuwa wasu dazuka da ke jihar Zamfara wadda ita ma ke fama da matsalar rashin tsaro.
Satar ɗaliban makarantar ta janyo ruɗani bayan da shugaban wani ɓangare na ƙungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau ya ce mayaƙansa ne suka sace ɗaliban.
Sai dai daga bisani hukumomi a jihar Katsina da Zamfara sun ce masu satar mutane ne suka sace ɗaliban.
Bayan wasu kwanaki ne 'yan fashin dajin suka saki dalibai 340 daga dajin jihar Zamfara bayan gwamnan jihar na wancan lokacin Bello Matawalle ya ce ƙungiyar Fulani ta Miyetti Allah ta shiga tsakani.
Makarantar mata ta Jangebe
A cikin watan Fabrairun 2021 ma ƴan bindiga sun kai hari makarantar kwana ta mata da ke garin Jangeɓe a jihar Zamfara wato GGSS Jangebe, inda suka sace kimanin ɗalibai 317.
Wani shaida a lokacin ya tabbatar wa BBC cewa an sace 'yan mata kusan 300 ne sakamakon kirga dukkan 'yan makarantar da suka rage bayan ɓarayin sun tafi.
Shi ma dai wannan hari ya ja hankulan mutane da dama a ciki da wajen Najeriya, inda aka riƙa kiraye-kirayen samar da jami'an tsaro a harabar makarantun kwana domin bai wa ɗalibai tsaro.
Harin ya sa gwamnatin jihar ta rufe mafi yawan makarantun kwana da ke nesa da gari.
Kwalejin Kagara
Haka kuma a ranar Talata 16 ga watan Fabrairun 2021 wasu ƴan bindiga suka shiga makarantar sakandaren maza da ke garin Kagara a jihar Neja da ke tsakiyar Najeriya inda suka yi awon gaba da wasu daga cikin ɗaliban tare da wasu malamansu da kuma wasu iyalan malaman.
Shugaban makarantar ya shaida wa BBC cewa akwai dalibai kusan 600 a makarantar ta kwana lokacin da lamarin ya faru.
Sai dai daga bisani gwamnan jihar Neja na wancan lokacin, Abubakar Bello ya ce an kwashe ɗalibai 27 da ma'aikata uku haɗi da iyalansu su 12.
Kwalejin Gandun Daji ta Afaka
A cikin watan Maris ɗin 2021 ma wasu mahara ɗauke da makamai sun afka wa kwalejin Horas da harkokin Noma da harkokin Gandun Daji ta gwamnatin tarayyya wato Federal College of Forestry Mechanisation a unguwar Mando a cikin garin Kaduna, inda suka sace ɗalibai kimanin 30.
Cikin wata sanarwa, kwamishinan harkokin tsaron jihar na lokacin, ya tabbatar wa da BBC faruwar lamarin.
Ƴan bindigan sun afka wa makarantar ne da misalin ƙarfe 11:30 na dare, lokacin da ɗaliban ke shirin kwanciya barci.
Jami'ar Greenfield Kaduna
Haka kuma a cikin watan Afrilun 2021 ne kuma hukumomi a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya suka tabbatar wa BBC Hausa cewa wasu 'yan bindiga sun kai hari kan Jami'ar Greenfield da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja inda suka sace ɗalibai da dama.
Ita ma a nata ɓangare rundunar ƴan sandan jihar ta tabbatar da kai harin tare da sace ɗalibai masu yawa.
An dai sace ɗaliban ne - da suka haɗa da maza da mata - daga ɗakunansu a lokacin da suka kwanta barci.
Islamiyyar Tegina
A ranar 30 ga watan Mayun 2021 wasu ƴan bindiga a kan babura suka shiga garin Tegina a jihar Neja inda suka yi kutsa makarantar islamiyya ta Salihu Tanko Islamic School, inda suka sace ɗalibai kimanin 150.
Wasu ganau sun shaida wa BBC cewa 'yan bindigar sun rika harbi kan mai-uwa-da-wabi kafin daga bisani su dauke daliban.
Sai dai cikin wata sanarwa da gwamantin jihar ta fitar a wancan lokacin, ta ce an harbi mutum biyu lokacin harin kuma an tabbatar da mutuwar ɗaya daga ciki, yayin da guda ɗaya ke cikin mawuyacin hali.
A lokacin, shugaban makarantar ya shaida wa BBC cewa akwai sama da ɗalibai 200 a cikin makarantar lokacin da ƴan bindigar suka shiga cikin harabar makarantar amma "adadin ɗaliban makarantar shi ne 302."
Kwalejin Tarayya ta Yauri
Sannan a watan Yunin 2021 wasu mahara suka ƙaddamar da hari kan makarantar kwanan ɗalibai ta FGC Yauri da ke jihar Kebbi, inda suka yi garkuwa da ɗalibai masu yawa.
Wani mutum da ya ga lokacin da lamarin ya faru ya faɗa wa BBC cewa ƴan bindigar sun ci karfin ƴansandan da ke gadin makarantar sannan suka ƙwace motoci ƙirar Toyota Hilux daga wurinsu suka zuba ɗaliban a ciki sannan suka tafi da su.
Maharan sun kuma harbi ɗalibai da dama da suka yi yunƙurin tserewa, inda bayan tafiyar maharan aka kai su asibiti don yi musu maganin raunukan da suka samu.
Makarantar Kuriga
A ranar Alhamis da safe ne wasu ƴan bindiga suka yi wa makarantar firamare da ƙaramar sakandiren Kuriga - da ke yankin ƙaramar hukumar Chikun a jihar Kaduna - ƙawanya tare da awon-gaba da wasu ɗalibai kimanin 287 da malaminsu guda ɗaya, kodayake shi malamin ya samu kuɓuta.
A lokacin da gwamnan jihar Uba Sani ya kai ziyara garin, malamin da ya kuɓutar ya shaida masa cewa, maharan sun zo makarantar ne daidai lokacin da aka kammala taron ɗalibai wato (Assemly).
Malamin ya ce an ɗauki ɗaliban makarantar sakandire kimanin 187, sai kuma na Firamare 125, aka kaɗa su daji, sai dai malamin ya ce da suka fara tafiya shi da wasu ɗalibai kimanin 25 sun kuɓuta.
Gwamnan jihar ya yi kira ga mazauna garin su kwantar da hankula, yana mai cewa gwamnati za ta yi duk abin da ya dace domin kuɓutar da sauran ɗaliban.
Duk da kawo yanzu ba a iya tantance masu alhakin harin ba, satar ɗalibai a makarantu ba sabon abu ba ne a Najeriya, kuma jihar Kaduna na cikin yankunan arewacin ƙasar da ƴan bindigar ke cin karensu babu babbaka.
Kwalejin Fasaha ta Nuhu Bamalli
Wani gungun ƴan bindiga sun ɓalla ƙofar shiga kwalejin fasaha ta Nuhu Bamalli da ke birnin Zazzau a jihar Kaduna, inda suka yi awon gaba da mutum 10 da suka haɗa da malamai guda biyu da ɗalibai 8.
Sai dai duka an sake su bayan biyan kuɗin fansa ga masu garkuwar.
Firamaren Alwaza, Nassarawa
Ƴan bindiga haye a kan babura sun far wa makarantar firamare ta garin Alwaza da ke jihar Nassarawa inda suka yi awon gaba da ɗalibai guda shida da rahotanni suka ce shekarunsu ba su wuce bakwai da takwas ba.
Ƴan bindigar dai sun yi garkuwa da ɗaliban ne a kan hanyar ƴan makarantar ta zuwa makaranta da misalin ƙarfe bakwai na safe.
Ƴansanda sun ce sun ceto su bayan ƙaddamar da aikin ceto.
Makarantar Bethel Baptist Kaduna
A ranar 5 ga watan Yulin 2021 ne ƴan bindiga suka kutsa makarantar sakandire ta kwana ta Bethel Baptist da ke jihar Kaduna, inda suka yi garkuwa da ɗalibai fiye da 120.
Masu garkuwar sun saki ɗalibai a hankali, inda suka fara da sakin ɗalibai 28 a ranar Lahadi 25 ga watan Yuli, inda kuma suka saki sauran a watannin Agusta da Satumba da kuma Oktoba.