Gwamnatin Katsina ta ce an ceto ɗaliban makarantar sakandiren Kankara 344

Latsa hoton sama domin sauraren hirar BBC da sakataren gwamnatin Katsina

Gwamnatin jihar Katsina da ke arewacin Najeriya ta ce an samu nasarar karɓo yaran makarantar sakandaren Kankara su 344 a ranar Alhamis da daddare.

Sakataren gwamnatin jihar Alhaji Mustapha Inuwa ne ya tabbatar wa da BBC hakan, inda ya ce a yanzu haka ana hanyar kai yaran birnin Katsina daga garin Tsafe na jihar Zamfara da ke maƙwabtaka da ita.

Ya ƙara da cewa a daren yau za a tarbe su a Katsina ƙarƙashin rakiyar jami'an tsaro, sannan a gobe Juma'a Shugaba Buhari zai gana da su a birnin Katsinan.

Nisan tafiya daga garin Tsafe na Zamfara zuwa birnin Katsina ya kai kilomita 213, tafiyar da za ta ɗauki sa'a kusan uku saboda rashin kyan hanya. YAyin da nisan daga Tsafe zuwa Kankara inda aka dauki yaran ke da nisan kilomita 83.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne wasu ƴan bindiga suka dirar wa makarantar kimiyya ta kwana ta maza da ke garin Kankara inda suka yi awon gaba da yara kusan 400.

Kwana hudu bayan haka sai shugaban ƙungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya fitar da saƙo yana ikirarin sace yaran.

Ko a ranar Alhamis da rana ma ƙungiyar Boko Haram ɗin ta fitar da wani bidiyon ɗaliban.

A cikin bidiyon, wanda jaridar intanet ta HumAngle ta fara wallafawa, ya nuna ɗaya daga cikin ɗaliban yana roƙon gwamnatin Najeriya da ta janye sojojin da ta aika domin ceto su yana mai cewa "babu abin da za su iya yi musu wallahi.

Tun da farko gwamnan Katsina Aminu Bello Masari ya shaida wa BBC cewa ba da daɗewa ba za a saki ɗaliban domin sun san inda aka ɓoye su.

Ya ce ƙoƙarin da gwamnati ke yi shi ne na a karɓo yaran ba tare da an yi amfani da bakin bindiga ba saboda kar a ji wa wsu rauni ko a kashe wasu bisa tsautsayi.