Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rashin tsaro: Manyan dazukan da ƴan ta'adda ke samun mafaka a arewacin Najeriya
- Marubuci, Halima Umar Saleh
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja
Hare-haren ƴan ta'adda da masu satar mutane na ƙara yawa a Najeriya musamman a arewacin ƙasar, kuma a yanzu kowa ya san cewa waɗannan miyagu kan samu mafaka ne a wasu manyan dazuka domin kitsa hare-hare ko kuma ɓoye mutanen da suke sacewa.
Alal misali mayaƙan ƙungiyar Boko Haram sun mamaye dajin Sambisa inda suka mayar da shi maɓoyarsu tun bayan da suka yi ƙarfi sosai.
A baya-bayan nan kuma an ga yadda masu satar mutane don kuɗin fansa da ƴan bindiga su ma suka mamaye wasu manyan dazuzzukan yankin kamar su Falgore da Rugu da dajin Birnin Gwari ko Kamuku da sauransu.
BBC ta yi nazari kan waɗannan dazuzzuka ta hanyar tattaunawa da Farfesa Khalifa Dikwa na Jami'ar Maiduguri da Stephen Zailani Haruna tsohon daraktan Hukumar kula da gandun dazuzzuka ta Najeriya da kuma Malam Abubakar wani haifaffen yankin dajin Kamuku ko Birnin Gwari.
Manyan dazuzzukan da miyagu suka fi mayar da su maboya a arewacin Najeriya su ne Dajin Sambisa a jihar Borno da Dajin Falgore a jihar Kano da Dajin Kamuku ko na Birnin Gwari a jihar Kaduna da Dajin Rugu na Katsina da Dajin Kuyambana na Zamfara da Dajin Alewa da Dajin Zugurma na jihar Neja da kuma Dajin Lame-Burra na jihar Bauchi.
Dukkan waɗannan mutane sun yi amannna cewa masu aikata miyagun laifuka kan yi amfani da waɗannan dazuzzuka ne saboda girmansu da duhuwar itatuwa da ke cikinsu da kuma yadda dukkan dazuzzukan suke da alaƙa ta haɗuwa da juna daga wasu ɓangarorin.
Haɗewar tasu kuwa ba wani abu ya jawo ba sai dama can haka Allah Ya tsara su, akwai hanyoyi da suke ɓullar da mutum daga wannan zuwa waccar saboda ayyukan noma da ake yi," in ji Farfesa Dikwa, mai sharhi kan al'amuran yau da kullum kuma wanda ya san Dajin Sambisa da kyau.
Dajin Sambisa
Dajin Sambisa a cikin jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya yake. Yana da nisan kilomita 60 daga birnin Maiduguri.
Yana daga kudu maso yammacin Gandun Dajin Tafkin Chadi. Dajin Sambisa ya yi iyaka da jihohin Yobe da Gombe da Bauchi ta wuraren Darazo, kuma masana da dama sun yi amannar ta yi iyaka har da jihar Kano.
Girman dajin ya kai murabba'in kilomita 60,000, wanda ya ninka ƙasar Isra'ila sau uku a girma. Turawan mulkin mallaka sun mayar da wajen gandun daji a zamanin mullkinsu. "Girman dajin ya ninka girman yankin kudu maso gabashin Najeriya," a cewar Farfesa Dikwa.
Dajin na ƙarƙashin ƙananan hukumomin Askira/Uba daga kudu da Damboa daga kudu maso yamma da kuma Konduga da Jere daga yammaci.
Dajin ya samo asalin sunansa ne daga wani ƙauye Sambisa da ke iyaka da Gwoza daga gabas. Dajin yana zagaye da dogwayen tsaunukan Gwoza da Mandara masu tsawon mita 1,300 waɗanda suka haɗe kan iyakar Najeriya da Kamaru, kamar yadda farfesa ya shaida wa BBC.
A shekarun baya-baya, daga tsakanin 2011 zuwa 2012 mayaƙan ƙungiyar Boko Haram suka mayar da dajin mafakarsu, "a da can baya akwai namun daji ma a cikinsa amma yanzu duk yaƙi ya kore su," in ji Farfesa Dikwa.
Rahotanni da dama sun sha cewa a dajin Sambisa wajen tsaunukan Gwoza ne aka ajiye ƴan matan makarantar Chibok da Boko Haram suka sace a 2014.
Farfesa ya ƙara da cewa: "A gaskiya yanzu Sambisa ta zama ƙarƙashin ikon Boko Haram don sun bibbine nakiyoyinsu da sauran munanan abubuwa da yake yi wa sojoji wahalar cin galaba a kansu."
Dajin Falgore
Dajin Falgore yana jihar Kano ne a kudu maso yammacin Najeriya. Shi ma an mayar da shi gandun daji a zamanin Turawan mulkin mallaka a shekarar 1960 sanan yana da nisan kilomita 150 daga birnin Kano.
Dajin na ƙarƙashin ƙananan hukumomin Tudun Wada da Doguwa da Sumaila. Sannan ya tafi har ya haɗe da jihohin Kaduna da Bauchi.
Wannan ne ya sa masana ke ganin Falgore ya haɗe da Dajin Lamai Bura na Bauchi da Dajin Birnin Gwari na Kaduna.
Dajin na da girman murabba'in kilomita 1,000. Manyan ƙalubalen da a yanzu haka Dajin Falgore ke fama da su, su ne farautar da ake yi da take ƙarar da dabbobin ciki da kuma yadda ƴan fashi suka mayar da shi wajen cin karen su babu babbaka.
A baya-bayan nan al'ummar yankin dajin Falgoren suna kokawa kan yadda masu garkuwa da mutane suka matsa wa hanyar da ƙauyukan da ke dajin.
Ko a watan Satumban 2020 ma rundunar ƴan sanda jihar Kano ta ce ta yi nasarar ceto mutum biyar da aka yi garkuwa da su a dajin, sannan wani ganau a yayin wani hari da aka kai ya ce suna cikin wani hali na zaman fargaba sakamakon yadda a cikin mako biyu aka yi garkuwa da mutane sama da 30.
To sai dai masu sharhi kan al'amarun yau da kullum na ci gaba da dasa ayar tambaya kan yadda har yanzu ake ci gaba da samun ɓullar masu garkuwa da mutane a dajin na Falgore, duk da samar da sansanin sojoji da na 'yan sanda a cikin dajin da gwamnatin jihar Kano ke ikirarin ta yi.
Haka zalika ko a shekarun baya sai da gwamnatin Kano ta samar da hukuncin kisa ga dukkan wanda aka kama da laifin garkuwa da mutane a faɗin jihar, wanda ake kallon ya yi tasiri wajen raguwar matsalar.
Dajin Kumuku ko Dajin Birnin Gwari
Birnin Gwari Kamuku yana yammacin garin Birnin Gwari ne a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya. Yana da nisan kilomita 14 daga garin Birnin Gwari. Ana ce masa Dajin Kamuku ko Dajin Birnin Gwari.
Yana da girman murabba'in kilomita 1,120 sannan ya zagaya ya haɗe da Dajin Kuyambana na Zamfara. Dajin ya samu ne tun a shekarar 1936 lokacin Turawan mulkin mallaka inda yake ƙarƙashin ikon jiha, daga baya aka mayar da shi Gandun Daji ƙarƙashin gwamnatin tarayya a shekarar 1999.
Malam Abubakar Isyaku wani haifafen yankin Dajin Birnin Gwari ne kuma suna da gonaki a wajen, ya shaida wa BBC cewa daga cikin dalilan da suke sa ƴan bindiga da masu satar mutane ke samun mafaka a can saboda yana da girman gaske.
"Akwai itatuwa a dajin da za a iya ɓoyewa ba tare da an gano mutum cikin sauƙi ba saboda surƙuƙi. Sannan yana sada ka da sauran manyan dazuzzuka.
"Kuma akwai ƙananan raufka da ake samun ruwa a ciki ba tare da ƙalubale ba. Sai dai daga cikin abin da ya sa masu laifin ke son wajen babu wani babban kogi da tsallake shi zai musu wahala.
"Da a ce akwai babban kogi da jami'an tsaro za su yi saurin rutsa su su kama su kafin su haye kogin," in ji Malam Abubakar.
Ya yi amannar masu satar mutane a babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna da kuma hanyar Birnin Gwari a wannan dajin suke ɓoye waɗanda suka sata kafin a biya su fansa a karɓe su.
Sannan ya ƙara da cewa a ganin sa za a iya maganin waɗannan miyagu, "Ya danganta da shirin gwamnati ko hukuma". "Ana iya amfani da jirgin sama don maganinsu."
Dajin Rugu
"Kowa zai shiga Dajin Rugu sai ya ratsa ƙasar Safana. Allah Ya kai mu Dajin Rugu domin in bi ƙasar Safana." In ji Dr Mamman Shata a wata waƙarsa da ya yi wa dajin a can baya.
A wannan daji ne aka yi amannar ƴan bindiga suke ajiye mutanen da suka sacewa a jihohin Katsina da Zamfara, ciki har da ɗaliban makarantar gwamnati ta kimiyya ta Ƙanƙara a jihar Katsina.
Dajin Rugu yana ƙaramar hukumar Safana ne a jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya.
A wata maƙala da ta fitar, jaridar Daily Trust ta ce Dajin Rugu yana da nisan kilomita 220 inda har ya dangane da jamhuriyyar Nijar.
Dajin Rugu ya ratsa ƙananan hukumomi bakwai da suka haɗa da Jibia da Safana da Batsari da Danmusa da Sabuwa da Dandume da Faskari. Kuma a kowane yanki akwai sunan da ake kiransa da shi, amma dai an fi saninsa da Dajin Rugu.
Jaridar ta ci gaba da cewa dajin yana da iyakoki shida, sannan akwai ƙoramu da madatsun ruwa har 18 da aka samar tun lokacin Sardaunan Sokoto.
Kamar sauran manyan dazuka, shi ma Dajin Rugu ya haɗe da Dajin Birnin Gwari da Falgore har zuwa Sambisa a cewar wasu majiyoyin da muka tattauna da su.
Ibrahim Sheme dan jarida kuma dan asalin jihar Katsina ya ce daji ne mai girma sosai shi ya sa har masu laifi ke mayar da shi maɓoya.
"Ba shi da wani duhu sosai sai a lokacin damina amma a lokacin rani bishiyoyi duk sun bushe ana ma iya ganin duk abin da ke faruwa a cikinsa tarwal da za a yi amfani da jirgi mai saukar ungulu.
"A da can mafarauta kan shige shi sosai saboda akwai dabbobin daji sosai. Amma a yanzu kam ya zama mafakar masu satar mutane," a cewar Malam Sheme.
Dajin Lame-Bura
Dajin Lame Bura na cikin jihar Bauchi ne a arewa maso gabshin Najeriya. Kuma yana da girman murabba'in kilomita 2,500 kamar yadda Stephen Zailani Haruna, tsohon daraktan Hukumar kula da gandun dazuzzuka ta Najeriya ya shaida wa BBC.
"A ƴan shekarun baya-bayan nan ƴan bindiga da masu satar mutane sun mayar da wajen maɓoyarsu saboda girman dajin.
"Amma daga baya jami'an tsaro sun yi nasarar fatattakarsu, don haka yanzu ayyukansu a wajen ba su yi ƙarfi kamar na sauran manayan dazuzzukan ba," a cewar Mista Zailani.
Gandun Dajin Alawa da na Zugurma
Da yake jihar Neja da ke arewa ta tsakiyar Najeriya na daga cikin yankunan da ke fama da matsalar tsaro ta hare-haren ƴan bindiga da masu satar mutane, ya sa muka duba don ganin wuraren da suka mayar maɓoyarsu.
Mista Zailani ya ce Gandun Dajin Alawa da Dajin Zugurma su ne manyan wurare biyu da maharan ke cin karensu babu babbaka a yankin jihar Nejan.
Dazuzzuka ne masu girma kuma su ma suna da alaƙa da waɗancan manyan na sama da aka lissafa.
Zugurma wani ɓangare ne na Gandun Dajin Kainji National Park a ƙarƙashin ƙaramar hukumar Mariga. Ya yi iyaka da Kogin Kontagora daga arewa maso yamma da Kogin Manyara a arewa sannan yana da girman eka 138,500.
A yanzu waɗannan dazuzzuka da a baya aka mayar da su gandun daji na gwamnati duk sun zama maɓoyar ƴan bindiga tare da samun ɓulle wa daga wani yanki zuwa wani.
Mista Zailani ya ce su dazuzzukan da suke yankin jihar Neja sun fi sauran duhuwa sosai.
Rufewa
Bakin dukkan mutanen da muka tattauna da su ya zo ɗaya kan yadda gwamnati za ta shawo kan wannan lamari.
Sun ce idan har da gaske gwamnatin take yi yaƙar waɗannan ƴan ta'adda da ƴan fashi a waɗannan dazuzzuka abu ne mai yiwuwa in da aka sa kishin ƙasa da ganin damar yi.
Idan ba haka ba kuma sun bayyana fargabar cewa miyagun za su sake samun ƙarfin iko idan sun ga an bar su sakaka, tun suna mamaye dazuzzuka ya kasance sun fara mamaye garuruwa da birane.