Rashin tsaro: Dalilin da ya sa ake kai hari makarantun kwana a Najeriya

Batun sace yara 'yan makaranta a Najeriya ba sabon abu ba ne, domin lamarin ya samo asali ne tun a shekarar 2014 inda 'yan ƙungiyar Boko Haram suka shiga makarantar sakandare ta 'yan mata da ke Chibok a garin Maiduguri suka sace ɗaruruwan mata.

Haka kuma a shekarar 2018 ma an sake irin hakan inda aka shiga wata makarantar sakanadare da ke Dapchi a jihar Yobe inda a nan ma aka kwashe 'yan mata sama da 100.

Duka waɗannan lamuran sun tayar da hankalin 'yan Najeriya da sauran ƙasashen waje, ganin cewa har yanzu akwai sauran wasu daga cikin daga cikin ɗaliban da ba dawo da su ba.

Hakan ya ja har yanzu wasu daga cikin masu fafutika da kare haƙƙin bil'adama ke ci gaba da neman a dawo da waɗannan yara, to a yanzu kuma, kwatsam sai a ƙarshen makon da ya gabata aka samu labarin cewa an sake kai makamantan waɗannan hare-hare da aka kai a Chibok da Dapchi garin Ƙanƙara na jihar Katsina.

Rahotanni sun ce sama da yara 'yan maza 500 aka yi awon gaba da su a lokacin da wasu da ake zargin 'yan bindiga ne suka kutsa makarantar a ranar Juma'a da dare.

Ganin cewa ba wannan ne na farko da ake kai irin wannan harin a makarantun kwana ba, BBC ta tuntuɓi Barrista Bulama Bukarti, wanda mai sharhi ne kan harkokin tsaro domin jin dalilin da ya sa ake kai hari a makarantun kwana.

Me ya sa makarantun kwana suka zama wurin kai hare-hare a Najeriya?

A cewar Barrister Bulama ya ce, "Babban burin ɗan ta'adda shi ne ya kai hari inda zai zama labari duk duniya a rinƙa cewa an kai hari wuri kaza don ya ɗau hankalin duniya, domin ta'addanci ba ya tafiya sai an haɗa shi da ɗaukar hankalin duniya an saka wa mutane tsoro".

A cewar Bukartin, abin da irin wannan hari ke nunawa shi ne Najeriya ta kasa koyon darasi a hare-haren da aka kai a baya ba, kuma gwamnati da jami'an tsaro ba su ɗauki matakai da za su tabbatar an tsare makarantu don tabbatar da cewa ba a ci gaba da kai hari irin waɗannan makarantu ba.

"Gungun masu laifi suna kai hare-hare irin waɗannan ne, domin suna neman wuri mai maiƙo ne, duk inda suka ga idan suka kai hari, za su iya kama wanda za su samu kuɗi, to lallai za su kai harin.

"A makaranta za su yi tsammanin akwai 'ya'yan masu kuɗi, ko gwamnati ta damu da ɗaliban, saboda haka idan aka kama su aka yi garkuwa da su, za a iya samun kuɗi a waɗannan wurare.

Waɗanne matakai ya kamata a ɗauka?

Domin ganin cewa ba a sake kai irin wannan hari a wata makaranta ba a Najeriya, Barrista Bukarti ya bayar da shawara da mafita ga gwamnatin kan wannan lamarin.

A cewarsa, hari a ko wane wuri abu ne mai hatsari kuma abin takaici, "lallai ne gwamnati ta kai isassun jami'an tsaro a dukkan wuraren da ake tsoron irin waɗannan hare-hare musamman makarantu da kuma ƙauyuka inda ake kai wa manoma hare-hare.

"Idan ba haka ba, za mu ci gaba da ganin irin wannan abin takaici, kuma goben al'ummarmu za ta lalace, dama yau ɗinta an rikata ta tuni."