Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
GSS Kankara: Ɗalibi ya gaya wa BBC Hausa yadda ya kuɓuta daga ƴan bindiga
Bayan sace ɗaruruwan ɗaliban makarantar sakadiren kwana da ke Ƙanƙara a jihar Katsina, BBC Hausa ta zanta da wani ɗalibin makarantar da ya tsira daga hannun yan bindigar da suka yi awon gaba da su a ranar Jumma'a.
Ɗalibin, wanda BBC ta nemi amincewar iyayensa kafin a yi hira da shi, ya ce ranar Juma'a da daddare bayan sun dawo daga karatu wajen karfe 9:30, sai suka ji ana ta harba bindiga a sama, daga bisani suka lura cewa har maharan sun shigo cikin makaranta.
Ya ce: "Sai kowa ya fito muka yi ta gudu muna haura katanga, bayan mun haura katanga sai suka riƙa hasko mana fitila suna cewa mu dawo".
A cewar ɗalibin, a lokacin ne suka juya suka koma, bisa tunanin cewa mutanen jami'an tsaro ne, amma daga bisani sun lura cewa ba su ba ne.
Ku nawa aka sace ?
"Bayan an shiga da mu cikin dajin, sai wani babba daga cikinsu ya bayar da umarnin a tsaya a ƙirga ko mu nawa ne kafin a ci gaba da tafiya", in ji matashin wanda muka sakaye sunansa.
Ya ce a lokacin da aka ƙirga su, sai aka ga cewa su 520 ne cif-cif.
Haka muka yi ta tafiya cikin daji muna taka ƙaya ana tura mu ana bugunsu, sai da muka kwana muna tafiya, saura miniti 30 gari ya waye aka ce mu kwanta mu huta", a cewarsa.
Yaya aka yi ka tsira ?
Ɗalibin ya shaida wa BBC Hausa cewa "bayan sun zaunar da mu sai na ɗan yi baya-baya, na samu gefen bishiya na ɗan juya musu baya, na kwanta na ɗan miƙe ƙafa ta''
"Bayan kowa ya tafi ne na taho ina rarrafe da dbube-dube har na shigo cikin gari" a cewarsa.
Ya ce ko da Allah ya taimaki mutum ya tsira daga hannun mutanen ba ka san ina za ka ba domin daji ne kawai kake iya gani, don haka Allah ne kawai ya tserar da shi daga hannunsu, kamar yadda ya ce.
Ɗalibin ya yi wannan magana ce a yayin da hukumomi suka ce jami'an tsaro na can suna farautar 'yan bindigar da zummar ceto sauran ɗaliban da aka sace.
Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya ce har yanzu akwai ɗalibai 333 da ke hannun 'yan bindigar.
Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban Najeriya ya shaida wa BBC cewa yara da dama sun gudo yana mai cewa yara 10 ne kawai suka rage hannun ƴan bindigar.
A cewarsa, yaran da suka tsere daga hannun maharan sun ce yara 10 ne ke hannun ɓarayin ƙasa da yawan ɗaliban da malaman makarantar suka bayyana.
"Wasu daga cikin yaran da suka gudu daga daji sun ce yara 10 ne ƴan bindigar suke garkuwa da su," in ji shi.
Sai dai shugaba Buhari yana shan suka daga 'yan ƙasar waɗanda ke ganin ya kamata ya je garin nan Kankara da kansa domin gann abin da ya faru maimakon aikewa da jami'an gwamnatinsa tun da dai yana jihar ta Katsina.
'Ba Buhari ne yake jagorantar Najeriya ba '
A cewar Kwamared Kabiru Dakata, wani ɗan gwagwarmaya, kana mai sharhi kan al'amuran yau da kullum a Najeriya, rashin zuwan Shugaba Buhari wurin da lamarin ya faru ya sake fitowa da ikirarin da wasu ke yi cewa ba shi ne yake tafiyar da harkokin Najeriya ba.
"Waɗanda ke cikin tawagar da ya tura su wakilce shi su ne fa mutanen nan da tun farko ya kamata su samar da tsaro, kuma su ne mutanen da yan Najeriya ke ta kukan cewa sun gaza a canja su, yau kuma an sace ɗaruruwan ɗalibai sai kuma aka sake tura su wai sune za su je su bawa iyayen ɗaliban tabbacin cewa za a dawo musu da ƴaƴansu", in ji kwamared.
A cewarsa, idan ka haɗa dukkanin waɗannan al'amura zarge-zargen da ake yi cewa shi shugaba Buhari ba shine yake gudanar da al'amuran ƙasar nan ba na sake bayyana a fili.
'Abu ne mai sauƙi ceto ɗaliban'
Sai dai Ministan Tsaron Najeriya, Bashir Salihi-Magashi, ya ba da tabbacin cewa za a ceto ɗaliban ba da jimawa ba.
Magashi ya bayar da wannan tabbacin ne a ranar Lahadi, lokacin da ya jagoranci wata tawaga ta gwamnatin tarayya zuwa ga Gwamna Aminu Masari na jihar ta Katsina.
Ya ce jami'an tsaro na aiki tuƙuru don ganin cewa an ceto su.
"Zuwa yanzu, kwamishinan ƴan sanda, da Kwmandan rundunar soji shiyyar Zamfara, da shugabannin DSS da na sojin sama da sauran jami'an tsaro sun yi mana bayani''
"Abin da muke sha'awa shi ne mu san yadda abin ya faru kwanaki biyu da suka gabata kuma mun yi imani da bayanan da suka gabatar, wannan aikin zai zama mai sauki a gare mu.
"Muna da dabaru kuma na yi imanin za mu iya yin hakan ba tare da wani lahani ga jama'ar jihar Katsina ba.
"Muna da bayanan sirri, bayanan, inda suke, motsinsu da kuma hanyoyin gudanar da ayyukansu.
"Aikin yana da sauki ga sojoji da' yan sanda.
Wanne hali iyayen ɗaliban ke ciki ?
A halin da ake ciki dai iyayen ɗaliban da aka sace na ci gaba da roƙon hukumo su yi dukkanin mai yiwuwa domin ceto musu ƴaƴansu, da har kawo yanzu basu dan halin da suke ciki ba tun bayan sace su.
Mahaifin wasu ɗalibai biyu ya shaida mana cewa tun da lamarin ya faru suke cikin damuwa "domin duk lokacin da aka ce yaronka ya ɓata dole ka shiga damuwa, don gara ma a ce mutuwa ya yi."
Ya ce mahaifiyar yaran ta shiga damuwa sosai ko da yake sun fawwala komai ga Allah.
Sai dai wani abu da ya ja hankali shine na tarwatsa iyayen yaran da suka taru a makarantar da jai'an tsaro suka yi, ta hanyar sanya musu barkonon tsohuwa, abin da wasu daga cikin yan kasar suka yi Allah wadai da shi, ciki har da jam'iyyar PDP da ta kira matakin a matsayin abin kaico. ''A dake ka, kuma a hana ka kuka", in ji PDP.
Shi dai gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari, wanda ya ziyarci makarantar ranar Asabar, ya bayar da umarnin rufe ɗaukacin makarantun sakandare na kwana da ke faɗin jihar.
Sannan ya ce a halin da ake ciki jami'an yan sanda da sojoji da ma na hukumar tsaron farin kaya sun duƙufa domin gano inda daliban suke tare da tseratar da su lami lafiya.