Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Boko Haram: Mene ne gaskiyar iƙirarin da Shekau ya yi kan sace daliban Ƙankara?
Tun bayan sace ɗaliban makarantar sakandare ta Ƙanƙara da ke jihar Katsina, 'yan Najeriya da dama musamman iyayen waɗannan yara suka shiga ɗimuwa sakamakon yadda lamarin ya faru.
Gwamnatin jihar Katsina dai da kuma jami'an tsaron Najeriya sun ce suna iya bakin ƙoƙarin su wajen ganin cewa an ceto waɗannan yara duk da cewa gwamnatin ta sanar da cewa suna tattaunawa da waɗanda suka sace ɗaliban, tare da jadda cewa an gano wurin da aka ajiye su.
Sai kuma kwatsam Shugaban Ƙungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya fitar da wani saƙon murya kimanin minti huɗu inda yake iƙirarin cewa ƙungiyarsa ce ta sace yaran kuma ya jaddada cewa ƙungiyarsa ba ta fara tattaunawa da kowa ba kan sakin yaran.
Wannan sanarwar ta Shekau ta ƙara kiɗima kusan duk wani mai bibiyar wannan lamari, ganin cewa wannan ne karo na farko da aka yi garkuwa da mutane masu ɗimbin yawa a makaranta a Najeriya, bayan ɗaliban Chibok a 2014 da kuma na Dapchi a 2018.
Sai dai wannan iƙirari na Shekau ya zo wa jama'ar ƙasar da mamaki kuma ya yi musu ba zata, ganin cewa a baya an yi zaton cewa 'yan bindigan da ke cin karensu ba babbaka a arewa maso yammacin Najeriya ne suka yi awon gaba da ɗaliban.
Duk da cewa akwai bayanan sirri da aka yi ta fitowa da su a kwanakin baya da ke nuna cewa akwai wasu daga cikin 'yan ƙungiyar Boko Haram da suka gangaro zuwa arewa maso yammaci inda suke gudanar da aika-aika.
Sai dai jama'a ba wai sun gamsu ba ne, domin sun san cewa 'yan Boko Haram akasari sukan kai hari ne su kashe mutane ko su sace domin su juya su don su zama nasu, amma ba a cika samun labarin cewa suna sace mutane domin karɓar kuɗin fansa ba, an fi danganta irin wannan da ɓarayin da ke shawagi a jihohin Zamfara da Katsina da Kaduna da Neja da Nasarawa.
Wasu daga cikin masu sharhi kan harkokin tsaro na ganin cewa Shekau na wannan iƙirarin ne kawai domin yaɗa farfaganda domin ya fito ya nuna wa duniya cewa har yanzu ƙungiyarsa na da ƙarfi.
Haka kuma ana ganin ya yi haka ne domin ya nuna wa ƙungiyoyin adawarsa na ISWAP da ANSARU cewa yana da ƙarfi ko kuma tauraruwarsa na haskawa.
Amma masu sharhi irin su Barrista Bulama Bukarti na ganin cewa zai iya yiwuwa iƙirarin da Shekau ɗin yake yi na ƙarya ne domin a cewarsa, "mutumin da ya ƙirƙiri ƙarya ya jingina wa Allah da manzonsa yake cewa kashe-kashen da yake yi Allah ne da ManzonSa suka sa shi, ba abin mamaki ba ne a ce ya yi ƙarya".
Ya kuma ƙara da cewa ba abin mamaki ba ne idan wannan iƙirarin na Shekau ya kasance gaskiya saboda dalilai da dama.
Dalili na farko da Barrista Bukarti ya bayar shi ne tun daga watan Janairun 2020 suka rinƙa samun bayanai cewa 'yan Boko Haram musamman na ɓangaren Shekau sun kutsa arewa maso yammacin Najeriya.
Dalili na biyu da Bukartin ya bayar na gasgata iƙirarin Shekau ɗin shi ne akwai wani saƙon na murya da wani maƙwafin makarantar ta Ƙanƙara da ya ɗauka yayin da ake kai harin, inda ya ce ya ji ana kabbara.
Bukartin dai ya ce duk da cewa bai da tabbaci kan wannan iƙirari na Shekau, amma yana ƙarfafa zaton wannan magana za ta iya zama gaskiya.
Me gwamnatin Katsina ta ce game da iƙirarin Boko Haram?
A nata ɓangaren, gwamnatin jihar Katsina, ta ce ba ta da masaniya kan iƙirarin da Abubakar Shekau ya yi cewa su ne suka kwashe ɗaliban.
A tattaunawar da BBC ta yi da Alhaji Abdul Aziz Mai Turaka, wanda shi ne mai bai wa Gwamna Aminu Bello Masari shawara kan sha'anin wayar da kan jama'a, ya shaida cewa su ma haka suka ji wannan batu kamar yadda kowa ya rinƙa gani a kafafen sada zumunta.
A cewarsa, "ko Boko Haram tana da hannu ko ba ta da hannu, mu roƙon Allah muke yi ya kuɓutar da waɗannan yara daga wannan musiba da suka afka ciki".
A halin yanzu iƙirarin da gwamnatin jihar Katsinan ta yi na cewa tana tattaunawa da waɗanda suka sace yaran ya sa wasu cikin ɗimuwa, inda wasu ke ganin gwamnatin kamar ba ta san da su wa take tattaunawa ba.
Haka kuma mutane sun ƙara saka shakku a iƙirarin da gwamnatin ta yi na cewa ta gano inda yaran suke tun bayan wannan iƙirarin na Abubakar Shekau.
Gwamnatin tarayyar ƙasar dai ba ta ce komai ba kan wannan iƙirarin na Shekau.