Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Boko Haram ta fitar da bidiyon ɗaliban sakandiren Ƙanƙara da ke hannunta
Kungiyar Boko Haram ta fitar da bidiyon ɗaliban sakandiren Ƙanƙara da ta yi iƙirarin yin awon gaba da su ranar Juma'ar da ta wuce.
Bidiyon, wanda jaridar intanet ta HumAngle ta fara wallafawa, ya nuna ɗaya daga cikin ɗaliban yana roƙon gwamnatin Najeriya da ta janye sojojin da ta aika domin ceto su yana mai cewa "babu abin da za su iya yi musu wallahi."
A cikin bidiyon mai tsawon minti shida da daƙiƙa 30, wanda ita ma BBC ta samu, ɗalibin ya nemi gwamnati ta rufe dukkan makarantu idan ban da makarantun Islamiyya sannan ta soke "duk wata ƙungiyar ƙato-da-gora."
Ɗalibin ya yi magana ne cikin harshen Turanci da Hausa.
Da alamu ɗaliban na cikin mawuyacin hali domin kuwa bidiyon ya nuna fuskokinsu cike da ƙura a cikin daji.
Ɗaliban sun ƙara da cewa an kashe wasu daga cikinsu inda suka roƙi gwamnati ta biya buƙatun ƙungiyar domin ta sake su.
A cikin bidiyon ana iya jin muryar wani mutum da karin harshe irin na Fulani yana cewa suna nuna wa gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ɗaliban ne domin ya ga cewa suna cikin ƙoshin lafiya.
Kazalika shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau, ya yi magana a ƙarshen bidiyon inda ya bayyana farin cikinsa bisa kwashe ɗaliban da suka yi.
Ya ƙara da cewa mutane da dama sun yi tsammanin ƙarya yake yi lokacin da ya yi iƙirarin cewa ƙungiyarsa ta ce kwashe ɗaliban, yama mai cewa ba zai ƙara cewa komai ba tun da yanzu mutanen da suka ƙaryata shi sun gani da idanunsu cewa su ne suka ɗauke ɗaliban.
A ranar Laraba ne Gwamna Masari ya shaida wa BBC cewa sun san inda aka ɓoye ɗaliban makarantar sakandaren kimiyya ta maza ta Ƙanƙara da aka sace ranar Juma'ar da ta gabata.
Gwamnan ya ce a yanzu haka bayanai sun nuna cewa yaran suna cikin dajin jihar Zamfara, "kuma ko ba dukkansu ba to mafi rinjayensu dai suna can wajen."
A ranar Talata, Ƙungiyar Boko Haram ta fitar da wani saƙon murya inda ta yi iƙirarin cewa ita ce ta sace ɗaliban.
A saƙon da shugaban ƙungiyar Abubakar Shekau ya fitar na tsawon minti 4:30, ya ce sun ɗauke ɗaliban ne a ci gaba da suke yi da yaƙi da karatun boko.
Kwashe ɗaliban ya jawo suka sosai ga gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari wadda 'yan ƙasar ke gani tana yin sakaci wajen wanzar da tsaro.