Greenfield University: An sace 'dalibai da dama a Jami'ar da ke Kaduna'

Hukumomi a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya sun tabbatar wa BBC Hausa cewa wasu 'yan bindiga sun kai hari kan Jami'ar Greenfield da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja inda suka sace dalibai da dama.

Rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar mana cewa 'yan bindigar sun kai hari a Jami'ar ne da daren Talata inda suka yi awon gaba da dalibai da yawa.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Kaduna Mohammed Jalige, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya kara da cewa "ya zuwa yanzu ba mu kai ga tantance adadin daliban da aka sace ba."

A cewarsa "yanzu muna wurin da lamarin ya faru, don haka sai mun samu rijistar makarantar sannan za mu san yawan daliban da aka sace."

Sai dai a wata hira da BBC, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida Samuel Aruwan ya tabbatar da mutuwar mutum daya wanda ma'aiakacin jami'ar ne, sannan wani daban na asibiti sakamakon raunin da aka ji masa.

Ya ce ko da sojoji suka je sun samu tuni an kwashe ɗaliban. "A yanzu mun rufe makarantar mun kwashe ɗaliban da ba a sace ba, mun miƙa su ga iyayensu.

"A yanzu haka muna ƙoƙarin tantance yawan waɗanda aka sace ɗin.,' a cewar Aruwan.

An sace daliban ne daga dakunansu kuma rahotanni sun ce daliban maza da mata ne.

Jami'ar Greenfield ta 'ya'yan masu hannu da shuni ce wadda aka bude a shekarar 2019.

A watan jiya ne 'yan bindiga suka sace ɗalibai 30 daga Kwalejin Horar da Harkokin Noma da Abubuwan da suka shafi Gandun Daji ta gwamnatin tarayyya wato Federal College of Forestry Mechanisation a unguwar Mando a cikin garin Kaduna.

Kodayake an kubutar da dama daga cikinsu, amma har yanzu wasu daliban suna hannun mutanen da suka yi garkuwa da su.

Jihar Kaduna na cikin jihohin da suke fama da hare-haren 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane domin neman fansa.

Alkaluman da hukumomi a jihar suka fitar a watan jiya sun nuna cewa mutane an kashe akalla mutum 937 sakamakon hare-haren 'yan bindiga da masu satar mutane a jihar a shekarar 2020.

Gwamnatin jihar Kaduna ta sha bayyana cewa ba za ta yi sulhu da 'yan bindiga ba domin kuwa suna kashe mutane ne babu gaira babu dalili.

A wata hira da BBC Hausa kwanakin baya, Gwamna Nasir El-Rufai ya ce ya kamata a buɗe wa 'yan bindigar wuta har sai an ci karfinsu.

"Idan Gwamnatin Tarayya ba ta ba mu sojoji na sama da na ƙasa da 'yan ƙasa ba, a shiga dazukan nan a kashe 'yan ta'addan nan a lokaci ɗaya, to za mu ci gaba da zama ciikin matsala," in ji gwamnan.